Sashe 23
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tausayi ta bashi, tun bayan da yaxo duniya take dawainiya dashi, dawainiya irin ta duk d'an da aka haife shi da wata tawaya, yadda iyaye suke fadi tashi akan da, suna burin ace shima ya zama kamar sauran yara masu lafiya. Bata chanchanci boye mata abinda yake ciki ba, watakila zata iya masa wani taimako Akai, duk da yana ji a ransa ba zai taba so ayi wa Amrah dole ba, yana dai fatan kawai za'a iya shawo kanta har ta amince dashi, maganar da sukayi da Sultan da alkawarin da yayi masa ya kara bashi kwarin guiwa , yasan Sultan zai yi iya kokarin sa.
"Mah-Mah..." Ya matso yana dora kansa a saman kafadarta, hannu tasa ta shafa kan nasa sannan ya cigaba, ya bata labarin komai tana sauraron sa, bata kuma katse shi ba har ya gama, sai daya kai karshe. Murmushi tayi masa ta mike sannan tace
"Ka kwantar da hankalin ka kamar ka sameta ka gama ne."
Kallon ta yayi a hankali yace
"Kar ayi mata dole dan Allah Mah-Mah."
"Karka damu." Tace
"Ka sanar da Sultan ko?"
Daga kansa yayi alamar eh sai tace
"Shikenan...Bari na samo maka abinda zaka ci."
Fita tayi ya maida kansa baya ya runtse idon sa a hankali ya furta
"Ya Allah!
Tana fita ta isa wajen da ta ajiye wayar ta, ta dauka sannan ta kira Umma, gaisawa sukayi sannan ta sake tambayar lafiyar Safwan din, tace mata an sallame su ma sun dawo gida, shiru suka d'an yi kafin Mah-Mah tace
"Ai ashe wai rashin lafiyar ta Amrah ce."
"Ta Amrah kuma?" Ta tambaya da mamaki
"Wallahi, kinsan yaran yanzu da saka soyayya a rai,wai ce mishi tayi bata sonshi shine shi kuma ya hau ciwo."
"Toh subhanallah." Umman tace tana jin ya kamata tayi mata maganar
"Wallahi, sai dana matsa masa sannan ya sanar dani."
Sai kuma tayi k'asa da muryar ta
"Dan Allah Umman yara alfarma nake nema, kasancewar Safwan shine kad'ai d'an da muka mallaka a duniyar nan, ga kuma lalurar da yake dauke da ita tun yana tsumma, shine nake neman alfarma wajenki, dan Allah ki bawa Amrah hakuri ta taimaka masa ta bashi dama, na tabbata ba zatayi dana sani ba, dan Allah."
Sosai umma ta lula tunani farkon maganar Mah-Mah, shine kadai d'an da suka mallaka, idan haka ne kenan? Toh ko sun san da maganar Sultan amma suka zabi ta Safwan din suka kyale tashi?
"Kina kan layi kuwa?" Mah-Mah ta tambaya jin tayi shiru
"Ya hakuri ina kai, na tafi wani tunani ne,naji kince Safwan ne kad'ai d'an da kuka mallaka, kenan Sultan..."
"Kiyi hakuri dole ce tasa ni fad'ar haka, amma dai wannan maganar ta wata ranar ce daban ba yau ba. Ki taimaka dan Allah,ke UWA ce kinsan yadda iyaye suke ji a duk lokacin da d'an su ya shiga wani hali."
"Shikenan ki kwantar da hankalin ki, ki kwantar wa Safwan din ma nasa, matar mutum kabarin sa, ko munso mu bawa Safwan idan Allah beyi Matar sa ce ba bamu Isa ba, saboda haka mu cigaba da addu'a Allah ya zaba mana mafi alkhairi."
"Haka ne, shikenan Allah ya taimaka mana."
"Amin ya Allah." Tace sannan sukayi sallama.
Ajiye wayar Umma tayi cikin tsananin mamaki, bata taba ganin ko da alamar da zai nuna cewa basu ne suka haifi Sultan ba, tayi niyyar yi wa Mah-Mahn maganar Sultan din amma jin abinda tace yasa ta fasa dan hakan na iya jawo masa wata matsalar, bata san me yasa ba take jin shi sosai a ranta take kuma yi wa Amrah sha'awar auren sa fiye da Safwan din ba duk da shima Safwan din bashi da wani nakasu. Tun da aka fara maganganun nan shikenan ta rasa sukuninta, sai a lokacin ta gane yadda iyaye keji idan aka fara maganar auren yaransu, zaka ga sun shiga damuwa sosai ashe ire-iren wadannan matsalolin ne ke tasowa, bata da wani zabi dan bata masan ya zatayi ba, kawai sai ta dukufa rokon Allah ya kawo musu koma menene cikin sauki.
***Tun bayan abinda ya faru tsakanin Sultan da Amrah wani abu me kuma faruwa ba, basu sake haduwa sunyi magana da juna ba, wayar ta dake hañnun sa ma Adnan ya bawa ya bata ya kuma sake dedicating kansa gaba daya a school baya dawowa gidan sai dare. Kallo daya zaka yi masa ka ga tsantsar rama da rashin kwanciyar hankali, duk sanda Abba yayi masa magana sai yace makaranta ce, a haka suka cigaba da tafiya babu abinda ya sauya dan Amrah na nan a kan bakanta ba kuma ta sake daga wayar mayen nata ba duk yadda yake kiran ta wanda tasan sarai Sultan ne ya cire shi daga block list data sashi, sashe daya na zuciyar ta na tausaya masa idan taga yana jera mata kira babu kakkautawa, takan tausaya masa tayi masa message da words biyu zuwa uku ta tura masa. Hakan da take shine yake kara masa hope har yake ganin watarana komai zai iya chanjawa.
Kamar ko yaushe idan ya dawo zai tarar da abinci me rai da lafiya a daki an ajiye masa wanda yasan aikin Amrah ne, duk sanda ya gani sai yaji wani iri, yana jin kamar ya dau waya ya kira Safwan yace masa yayi hakuri ba zai iya cika masa alkawari ba, kamar ya dauke loudspeaker ya fad'a yadda kowa zaiji wala'alah hakan zai sa abinda ya danne masa zuciya yayi sauki , sai dai ya riga ya gama making mind dinsa, ya kuma yi alkawarin duk runtsi bazai taba chanjawa ba, not now not ever.
Kadan yaci abinci ba wai dan bayajin yunwa ba, ba kuma don abincin babu dad'i ba, sai dan baya cikin abubuwa masu muhimmanci yanzu a rayuwar sa, yana ci ne kawai dan ya faranta mata rai, sannan ya saka wani abu ko yaya ne a cikin nasa ko dan lafiyar sa.
Kudade sosai yake samu a duk watan duniya, dama scholarship din tasa 100% ce tayi covering komai,sannan suna biyan sa wasu kudade na karatun da yakeyi, ganin babu abinda zai yi da kudin yasa ya tuntubi Mubarak akan ya nema musu fili shi da Safwan, bayan an samu an siya ya kuma dora masa alhakin kula da komai ba tare da ya sanar da Safwan ba dan so yake kawai yayi masa bazata.
Karatun nasa ma ya matse shi sosai baya ko hutawa saboda so yake yayi yayi ya tattara ya bar kasar dan zama waje daya da Amrah kara masa nauyi yake a zuciyar sa.
Wani yammaci ya dawo da wuri ranar, yayi wanka ya chanja kayan sa yana so ya kai musu ziyara, kusan kullum sai mutumin ya kirashi akan yaushe zaizo, shiyasa da yaga ya gama da wuri yau sai kawai ya shirya ya fito. Suna zaune ita da Afrah suna solving wani puzzle, ya shigo falon, bata dago ba har ya iso daidai kujerar da take kai, ya tsaya yana kallon abinda sukeyi, duk da babu yadda rana zatazo ta fadi be saka ta a idon sa ba ko da daga nesa ne, amma sai yaga yau ta chanja masa baki daya, kamar an sake sabunta ta ta ko yace an musanyata da wata daban, muryar Afrah ta katse shi
"Ya Sultan fita zakayi ne?"
"Eh kina da sako ne?" Yace
"No Amrah ce dai tun dazu take jiran ya Adnan wai zai rakata ta ina kika ce ma?" Ta kalle ta
"Bansani ba." Tace tana bata rai, harde hannayen sa yayi yana kallon ta, ta dago suka hada ido kawai ta harare shi ta cigaba da abinda take dan har ga Allah haushin sa take ji sosai.
"I'm Sorry." Yace a hankali, taji shi sarai sai tayi kamar bata ji ba, gaba ya d'an yi kamar zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo
"Dan Allah minti biyu." Ya langabe kai tare da hade hannun sa waje daya alamar roko, tashi tayi kamar zata sai kawai ta wuce shi tayi shigewar ta ciki. Be ji dad'i ba, ya kuma san tana da right din reacting fiye da yadda tayi, toh amma ya zai yi? Da tasan yadda yake ji da bata kara masa akan abinda yake ji din ba. Guiwa a matukar sake ya fita ya nufi gidan.
Afrah na duba messages din ta na whatsapp taga Mah-Mah tayi mata magana tun jiya ama ashe, shiga tayi sai ta ganta online ma, da alamar recording take, jira tayi ya shigo ta kunna tana sauraro. Bayan ta gama shi ta danna itama ta shiga recording, recording din daya yi sanadiyyar chanja alakar mutane da yawa!
***Yau kai tsaye ya shiga gidan ya kuma wuce kai tsaye ya danna door bell, ya rungume hannayensa a bayan sa yana jiran a bud'e. Yarinyar ranar ce yau ma ta bud'e, ganin shine yasa tayi gaba bayan ta ce ya biyo ta, suka wuce falon farkon da suka zauna ranar suka shiga chan cikin gidan, waje ta nuna masa ya zauna sannan ta shiga ciki, jim kadan ta fito ta wuce shi. Kansa a k'asa yana tunanin abinda ya faru kafin ya tawo ta fito, yau ma kamar wanchan ranar fuskarta babu walwala, sai dai tana ganin shi tayi kokarin daidaita yanayin ta, ta maye damuwar dake shinfid'e saman fuskarta zuwa murmushi me fadi,me dauke da ma'anoni masu yawa. Zamowa yayi ya gaishe ta, ta amsa a sake sosai fiye da duk ganin da yayi mata, sannan da kanta yaga tabi wata kofa sai gata ta dawo da dan karamin plate da cup da Lemo alai ta ajiye masa sannan ta zauna, godiya yayi mata sannan ya ce
"Yau Baba baya gida?"
"Baya nan, ya dan fita amma nasan zaka iya ganin shi ya shigo yanzu ma."
"Allah sarki." Yace yana kisissima abinda ke masa yawo a zuciyar sa, yana jin idan be ji wani abu daga garesu ba kamar ba zai iya cigaba da komai ba, yana son sanin damuwar wadannan bayin ALLAH da yake jin su sosai a ransa, dan gyara zaman sa yayi kad'an yace