← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 108

Sashe 104

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu wanda ya tanka sai lumshe Ido kawai da Sultan yayi masa kad'an ya bud'e su, da gudu ya koma wajen kofar ya saka aka wangale kofofin suka tura motocin su ciki, masu tsaron kofar suka bi bayan motocin da akayi wa lamba da SMMS 1 har zuwa 4 da kallo suna tunanin wadanne Masarautar ne suka zo haka, daga gani Babbar Masarautar ce.
   Kai tsaye gaban Babbar Fadar suka nufa, dama Sultan yasan wajen, da ido kawai Maimartaba yake bin komai zuciyar sa babu dadi, yana tuna abinda ya faru a shekarun baya, har suka samu waje sukayi parking idanun mutane basu bar kansu ba, gaban fad'ar a cike take taf, babu abinda kake ji sai kid'ekid'e da bushe bushe.
   Daga ciki manyan Masarautar ne suna cike da farin ciki, Sarki Bello Moddibo Saji be fito ba, suna ciki suna magana da Bilal wanda ya tubure lallai ba zai bada Sarauta ba, wanda suke so a yau ayi komai ya maida wa mahaifin nasa sarauta, tun suna lallaba shi har suka fara yi masa wuta wuta amma be sa ya saduda ba, sai ma maganganu da yake fad'a har yana ikirarin zai saka a rufe duk wanda yace zai kawo masa cikas ciki kuwa har da mahaifin nasa, abun yayi matukar basu mamaki basu kuma yi tunanin iskancin nasa ya kai haka ba, gashi dole dai suna bukatar abubuwan da suka zama jigon Sarautar daga wajen sa kafin su gudanar da komai.
  Karar jiniya ce ta cika Masarautar wadda ya saka su maida hankalin su gaba daya, suka fito da sauri da mamakin zuwan Maigirma gwamna wanda daga jin jiniyar kasan shine, babu sanarwa zuwan ba zata hakan ya nuna lallai akwai wani babban al'amari, a gefen da su Sultan sukayi parking motocin su a gefen nan ne motocin mai girma gwamna suka tsaya suma. Ganin haka ya saka Maimartaba Sarki Usman Muhammad Moddibo ya balle murfin motar ya fito, Sultan, Safwan da Muhammad suma suka fito a kusan lokaci daya, suka tsaya daga bayan sa Sultan a tsakiyar su kowannen su sanye yake da shigar Sarauta, idanun Sultan makale da glass dan siriri fari wanda ya sake fito dashi sosai, zoben hannun sa ya shafa kad'an lokacin da suka karasa wajen Maigirma gwamna da ya taho suka hadu.
  A daidai lokacin Sarki Bello da mukarraban sa suka fito da sauri. Wata irin zabura sukayi dan ganin wanda basu taba tunani ko hasashen gani ba, hasali ma makasudin wannan taron nasu akan nasarar da suka samu akansa ne, a firgice suka bi yara matasan dake bayan sa, idon Sarkin ya sauka akan hannun Sultan da yake murza zoben yana kallon cikin idon sa wanda kana gani kasan da biyu yayi hakan, daga nan inda suke aka rasa wanda zai karaso ya tarbi Maigirma gwamna. Kallon Maimartaba Gwamna yayi sukayi murmushi sannan suka haura zuwa inda suke tsaye zufa na karyo musu. Take musu baya su Sultan sukayi kowannensu fuskar sa dauke da farin ciki mara misaltuwa.
  Fuskar Sarki Bello kad'ai zaka kalla ka tabbatar da irin tashin hankalin da ya shiga, ya kasa furta kalma daya har suka cimmasa, sai a lokacin yayi ta maza ya shiga yiwa Maigirma gwamna sannu da zuwa, amma kuma idon sa yana kan Sarki Usman da yake masa murmushi me cike da ma'anoni ta cikin nadin sa. Kamar wanda aka bige wa kafa haka ya jasu zuwa cikin fad'ar inda a lokacin kowa ya tsure, duk suna tsattsaye kamar wadanda aka dasa, kansu duk a k'asa musamman wadanda suka zama masu fuska biyu a wajen Sarki Usman din.
   Kai tsaye kujerar da aka tanada domin gwamna nan ya zauna, Yarima Bilal ya yi saurin danewa kujerar Sarkin, kunya ta kama Sarki Bello amma ya kanne ya samu gefe ya zauna, daf da shi Sarki Usman ya zauna shima yayi saurin kallon sa, gefe Maimartaba ya kalla kamar be san me kallon nasa yake nufi ba.

Daga wajen fad'ar tuni wajen ya kaure da ife-ife da sowa, babu abinda kake ji sai murnar mutane kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa, manyan da suka san waye Sarki Usman suka shiga bawa yaran da suka taso bayan tafiyar sa labarin irin halayen sa, wanda dama sun jijji wasu a wajen iyayen su, abin ka da matasa masu jini a jiki, tuni suka dauki hayaniyar suka shiga buga abubuwa suna kiran sunan Sarki Usman, hakan ya sake saka Sarki Bello da mukarraban sa a matukar tashin hankali, gashi har lokaci Maigirma gwamna be ce komai ba akan zuwa bazatan da yayi, sai amsa gaisuwa kawai yake yana murmushi.
   Kokarin daidaita wajen akeyi dan tuni wajen ya dinke taf da mutane, wane gaya wa wane har mata ma dake cikin Masarautar duk sun fito, wasu na kuka, kukan farin ciki wasu na dariya.
   Ummi da hawayen ta ya cigaba da sauka ta dinga binsu daya bayan daya daga cikin motar kukan ta na karuwa, tana jin wani abu yana zagaye kowanne lungu da sako na jikin ta, niyyar bud'e kofar tayi Amrah ta riko hannun ta da sauri.

"Ummi karsu yi miki wani abu, kiyi hakuri wajen ya lafa."

Komawa tayi ta zauna tana girgiza kanta, sai kuma tasa tafin hannun ta, ta toshe bakin ta gudun kar kukan ya fito sosai.
  Duk yadda jami'an tsaro da fadawa sukayi kokari tsaida mutanen nan amma abin ya fassaka, ihu kawai suke suna Kiran sunan Sarki Usman. Duk abin nan da ake a kunnen Sarki Bello da jama'ar sa, gashi kunya duk ta kamashi abinda Yarima Bilal yayi masa balle yayi wani abu akai, yana nan zaune kamar kowa Gwamna ya tashi ya soma magana,

"Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh..." Yayi sallama

"Wa alaikumussalam warahmatullah wabarkatuh."

Jawabi ya shiiga yi akan makasudin zuwan sa Masarautar, da labarin da ya samu na saukar Sarki Bello ya dora dansa akai, yaron da duniya ta tabbatar da rashin chanchantar sa da zama shugaban al'umma, dan haka ne gwamnati ta shigo ciki, ta kuma bada umarni bisa ga sharadin da yake a shashi na 104 na dokar k'asa, ta sauke Sarki Bilal daga kujerar mulki ta nad'a Yarima Muhammad Sultan Usman Moddibo Saji a matsayin sabon sarkin Masarautar Saji, bisa ga dalilai masu karfi da duk wanda yake cikin nan wajen yasan su, ya kuma san zabin da gwamnati tayi ba zabi ne irin na tumun dare ba, zabi tayi bisa chanchanta da dacewa, ta kuma yi amfani da koke da korafin al'umma domin ita gwamnati dama ta mutane ce."

K'asa k'asa maganganu suka dinga tashi a cikin fad'ar, wani daga cikin dan majalisar sarki ya mik'e yace

"Bama goyon bayan wannan sabon tsarin, bamu yarda da shigo mana da bare cikin mu ba, bamu da masaniya akan waye Muhammad Sultan da har za'a bashi damar mulkarmu,saboda haka muna so gwamnati tayi mana bayani yadda zamu gane."

Murmushi kawai Maimartaba yayi, ya sake gyara zama yana kallon yadda wasan yake tafiya, Sultan da yaji kamar an dora masa wani abu a take, yaji baya shakka ko tunanin wani a wajen ya tashi, ya daga hannun sa duk suka zuba masa na mujiya,

"Sultan Usman Moddibo Saji, babban d'a ga Sarki Usmwn Moddibo Saji, wanda aka raba shi da mahaifiyar sa tun yana ciki, aka so salwantar da rayuwarsa, cikin jahilci da rashin sanin cewa duk wanda Allah ya kaddara masa rayuwa babu wanda ya isa ya hana shi, shine yau a gaban ku, dauke da abinda kuka rasa, wanda ya zama kamar wata shaida ce ta zama cikakken Sarki me iko, ina fatan wannan..." Ya nuna zoben hannun sa

"Ya ishe ku hujja... Saboda haka idan akwai me yin magana sai yayi."

Tashi gwamna yayi,

"Za'a aiko wakili da rubutacciyar takarda akan sabuwar dokar da gwamnati ta saka, sannan gwamnati ta shirya yin nadin sabon sarki nan da kwana uku idan Allah ya kaimu, saboda haka kuna da nan da kwana ukun ku karkare komai."

Da haka ya juya, masu tsaron lafiyar sa da mukarraban sa na gwamnati suka take masa baya, babu wanda ya iya tashi ya rakashi, yana fita wani tsoho cikin bacin rai yace

"Gimbiya bata da d'a, bata taba haihuwa ba, ta ya akayi aka haife ka, kuma ta yaya ka mallaki zoben hannun ka?"

"Ni da kai da kowa anan da duk wanda yake da hannu yasan cewa Gimbiya na da 'yaya ba d'a ba, ya kuma san yadda akayi gimbiya ta rasa d'anta na farko."

"Karya kake yi yaro, karka zo mana da sabon abu nan kaji."

"Ka iya bakin ka, ka kuma rik'e girma da tsufan ka, kafin kayi nadama."

Shiru yayi ganin yadda Sultan din yayi magana fuskarsa a had'e, sosai ya fito a jinin sarautar sa, tamkar mahaifin sa lokacin da yake kamar sa, komawa yayi lakwas be sake magana ba, ran Sultan da ya baci ya kalli fadawan da suke kofa a zafafe yace

"Akwai baki a mota a shigo dasu."

Rige rigen fita suka yi, aka je aka shigo dasu Amrah, babu wanda be yi shock ba ganin Gimbiya, Maman Yara da Aminatu a tare.
   Sarki Bello ya tashi da sauri yana nuna Maman Yara da hannu

"Atika! Atika!"

"Allah ya taimake ka,Nice nan maafarki kake ba."

"Ina kika shiga, tsawon wannan lokacin."

"Ina nan ina ruwa kamar yadda Allah ya hukunta sai nayi."

"Inaaaa... Inaaa jinjirin da... daa.. kike tafi tashi." Ya karashe kamar an fizgo maganar.

"Gashi nan a gaban ka, Allah yayi hukuncin Sa akan shi, ya raya shi rayuwa me inganci."

"Daa..maaa...ha'iin..ta ta ki.. kayi??"

"Idan hakan na nufin ha'inci ba? Toh hakan ne."

"Ke! Ki kula da wanda kike magana dashi."
Wani bafade yayi maganar yana daka mata tsawa. Wani kallo Sultan yayi masa, ya dauke kansa yana cije bakin sa.

Tasowa wasu dattijai su biyu masu farin gemu sukayi, suka matso suka kama hannun Sultan, yayi musu murmushi kad'an ba tare da ya saki fuskarsa ba, cikashi sukayi suka isa gaban Sarki Usman suka zube kowannen su kansa a k'asa

"Barka da zuwa Sarkin sarakuna, hakika mun yi matukar farin ciki da dawowar ku, Allah ya tsare ku ya kare ku a duk inda kuke, Alhamdulillah."

"Barka dai Wambai, barka dai Waziri." Ya amsa musu a ciki fuskar sa dauke da fara'a.
Chapter 104 · 0% Book details