← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 108

Sashe 16

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**Abin duniya yayi wa Safwan yawa, har ya fara jin chanji sosai a tattare dashi, wanda yake tunanin zai iya shafar lafiyar sa, sam Amrah ta daina daga kiran sa ko ya kira, text messages din kuwa bashi da TABBACIN tana gani ko bata gani tun da ba reply take masa ba, Mah-Mah ta lura da yanayin sa,ranar ta zaunar dashi tana tanbayar sa me yake damun sa, ganin ta damu sosai yasa ya fad'a mata gaskiya ya kasa samun yadda zai shawo kan Amrah ne, lallaba shi tayi, tace zasuyi magana da Daddyn su, shima idan yaso ya tuntubi Sultan da maganar ko zai bashi wasu shawarwarin. Basu fiya magana yanzu da Sultan din ba sbaoda dukkan su sun zama busy, shi da karatu shi kuma aikin da ya fara a Federal High Court ya kara sashi ya zama so busy, gashi yana under wajen kamfanoni uku a matsayin private lawyer dinsu. Bari yayi gari ya waye daidai lokacin da yasan zai same shi a waya sai ya kira.
Gari na waye wa ya kira Sultan, he badly need him dan idan be fallasa asirin zuciyar sa ba, zata iya farfashewa a zo a tarar da ita ta zama pieces a k'asa, babu dogon zance kamar yadda suka saba yana dagawa yace

"Akwai matsala."

"Subhanallah, are you sick?" Ya tambaya yana mikewa daga zaman da yake yana bitar karatun aa

"I'm about to be, so soon kuma dan wallahi ina jin zuciya ta na zafi, idan ban fad'a mata ba komai zai iya faruwa,please help me ina cikin damuwa."

"Me kake cewa? Me yasa ka kasa fad'a mata? Who is she? Ni ka bani number ta, na kirata na fad'a mata yadda dan uwana ya damu da ita, nasan dole ta karbi soyayyar ka."

"Bansan me yasa ba, bani da confidence sam, kuma har nayi ma su Daddy magana har an gama magana da su Abba."

Abban da ya ambata yasa gaban sultan ya dan buga, sai kuma ya share da ya tuna ai kowanne Baba ma zai iya zama Abba..

"Amma me yasa ka saka su Daddy a maganar ba tare da kun daidai ta ba, kuma tun yaushe akayi haka amma baka fad'a min ba."

"Ka gane, ina jin tsoron kamar zan rasata, shiyasa nayi saurin fada musu, nasan idan suka shiga maganar na same ta na gama, saboda babu yadda za'a yi Abba yaki, toh kuma kaga abinda ya faru, wallahi tama ki bani dama balle na yi mata bayanin kaina."

"Baka kyauta ba, kasan mata basason irn haka, shiyasa ma kila taki sauraron ka, tana ganin kamar zaka sa ayi mata dole ne."

"Toh ya zanyi yanzu? Wallahi idan ban sameta ba rayuwa ta na cikin matsala."

"Safwan!!! Get hold of your self,kasan condition dinka, kasan komai amma kana so ka jefa kanka a cikin matsala muma ka jefa mu, ya kake so su Daddy suyi idan wani abu ya sameka, kana tunanin Mah-Mah kuwa? Kasan irin tashin hankalin da take shiga duk lokacin da wani abu ya faru da kai? Kayi tunani first kafin ka shiga ramin da mu kanmu ba zamu iya ciro ka ba dan Allah."

"Sultan! Ya zanyi!? Kasan abinda nake ji kuwa? Kasan soyayya da yadda take da zafi kuwa? Ka sani? Ba yin kaina bane, kuma bansan yadda zanyi na rage ba wallahi."

"Ok ok, I understand, dan Allah ka kwantar da hankalin ka, ka nutsu zan yi kokarin ganin komai ya zo da sauki. Yanzu idan mun gama magana ka tura min number ta, zan kira ta, zan yi kokari wajen convincing dinta in sha Allah."

"Zaka iya? Ka tabbata zaka mata magana? Zaka iya mata magana face to face amma idan kafi son number zan tura maka, please kayi iya kokarin ka dan Allah, ka fini kusa da ita yanzu idan ma face to face din ne zaka fi saurin convincing dinta."

Sultan be gane kan abinda Safwan ke nufi ba, shi da ke wata uwa duniyar amma yake ma maganar face to face, sai ya share kawai dan kar ya kuma sashi dogon tunani yace

"Zan iya yin komai for you, I promise you ko bata so ka ba at the beginning zata so ka a karshe, i promise you this."

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin kamar matsalar sa ta kau, yana jin kamar bashi da sauran matsala ko damuwa, yasan Sultan zai yi komai domin ganin ya bashi dukkan abinda yake so. Ta ina zai fara gode masa? Kaf rayuwar sa a tsaye yake akan sa, koman sa shine, bashi da wani buri sai na ganin shi ya samu abinda yake so ko da shi zai rasa, ta ina zai fara saka masa? Anya yayi daidai daya dora masa alhakin kula da komai nasa ciki harda abinda ya kamata ace shi yayi wa kansa? Toh amma be san yadda zai yi ba, he's too weak akan komai, shi tashi kaddarar kenan, tun da yazo duniya yake struggling da komai ciki harda iskar numfashin da yake shak'a. Sultan is a blessing to him, Allah kadai yasan dalilin da yasa shi turo shi cikin rayuwar sa. Be tura masa number a lokacin ba, ya bari a matsayin zai bi komai a sannu yaga abinda Allah zaiyi.

*** Ranar da su Afrah suka dawo murna wajen Umma da Amrah ba'a cewa komai, text tayi wa Sultan yana school ta fad'a masa dawowar tasu, ya kirata sukayi magana sannan ta kashe.
A makare yake dawowa ranar, saboda haka sai da ya fara tsayawa wani shopping mall ya siyo musu chocolate da yawa sannan ya nufo gidan, a falo ya tarar dasu dukkan su suna hira da Abba, takalman sa ya cire ya karaso ya zauna a gefen Adnan ya gaida Abba cike da girmamawa yayi masa sannu da zuwa sannan ya gaida Umma, Amrah da Afrah suka gaishe shi, ya d'an tsokani Afrah ya tashi ya shiga ciki, yana zama Adnan ya shigo ya kirashi inji Abba, rigar saman kawai ya cire ya same shi falo, cups ne guda uku a jiye da coffee me zafi, abba ya dau daya ya basu suka dauka shida Adnan sannan suka shiga hirar karatu yana musu tambayoyi, sai wajen sha d'aya sannan yayi musu sai da safe ya wuce dakin sa.
Umma na zaune ya shigo, ya zauna a gefen gadon sannan yace

"Menene labarin da kika ce zaki bani da zarar na dawo, dan nima tafe nake da labarin da nasan zaki so sosai."

"Nima kam nasan zaka so so labarin."

"Toh ina jinki." Yace yana gyara zama.

"Dama maganar Amrah ce..."

"Nima maganar tace din, amma inaga nawa zaifi naki saboda haka ni zan fara." Yace yana dariya

"Shikenan, ina sauraron ka."

"Nayi wa Mamana miji." Kamar saukar aradu haka Umma taji maganar, zaro ido tayi da sauri tace

"Miji kuma Prof? Waye shi?"

"Kwantar da hankalin ki, Danki ne ma ai."

"D'ana? Wanne kenan?"

"Safwan!"

Da sauri ta mike ta kuma dora hannun ta akan chest dinta

"Safwan ko Sultan?"

"Sultan Kuma? A ah Safwan ne dai mukayi magana da Alhaji Sulaiman kuma har ma nayi musu alkawarin basu sanin da nayi babu wanda yaran nan suke kulawa "

Jagab umma ta koma ta zauna kamar wadda aka tura,

"An samu matsala Prof, Sultan da Amrah suna son junan su, chan gefe kuma Safwan har ya kai maganar wajen iyaye, na tabbata iyayen nasu basu san da maganar Sultan ba, yanzu ya kenan?"

"Kina nufin shi Sultan din ne yake son mamana?"

"Kwarai kuwa, itama kuma tana sonshi, bansan ya akayi haka ba."

"Toh gaskiya ni iyayensu Safwan suka ce min, kuma bama haka ba tun kafin suyi min magana Hajiya tayi min maganar dan yaje ya sameta da zancen, kinga kenan babu kuskure a maganar kenan."

"Toh, akwai matsala."

"Kinga Ina zuwa." Abba yace yana mikewa, dakin ya wuce yayi musu knocking, Sultan ne ya bude, ganin Abba yasa shi dan ja baya, tsayawa yayi yana kallon sa sai kuma ya fasa magana yace yazo falo ya same shi ya juya zuwa dakin su Amrah, nan ma knocking yayi, Afrah ta bud'e masa, yace Amrah ta same shi a falo ya wuce yana kokarin had'a maganganun waje daya.

Rano

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________

_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )

💙

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
Chapter 16 · 0% Book details