← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 108

Sashe 26

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lumshe ido kawai tayi saboda yadda take jin kanta ya yi mata wani irin kato tamkar an dora mata duniya haka take jinsa, saboda raunin da yake a goshin ta shine ya yi sanadiyyar hakan. Ta sunkuyar da kanta kasa ba tare da ta kuma cewa komai ba sai zuciyar ta da ta addabeta akan ganin rashin imani da rashin mutunci a gurin bafaden da ya ce mata yar talakawa. Bata taba zato ku tsammanin cewa haka suke ba, ashe ba su da kirki kansu kawai suka sani. Amman ban da haka ba ta ga dalilin da zai sanya su dinga yiwa mutane abin da suke yi ba. Mas'oud ya dinga kallanta yana son su sake had'a ido ko zai ji sassauci akan zugi da rada din da yake zuciyar shi, yana son ta nuna masa wata alama da zata tabbatar mishi da cewa a kowane yanayi take ciki zata iya gane shi da kuma matsayin da yake a gurin ta.

Ganin tsawon lokaci taki dagowa ya sanya shi juyawa zai fita daga dakin, kamar an ce ya kuma kallon ta sai yaga ta dago ta kalleshi tana rausayar da kai alamar damuwa. Ya koma tare da cewa.

“Sannu kinji?”

Ta kifta idanuwa alamun ta amsa gashi yaga taki kawar da ido daga kansa yace.

“A kawo tea ko?”

Tayi shiru ba ta ce komai ba dan magana da kyar take iyawa. Nurse d'in tace ya bari a had'a mata suma zasu so ganin ta d'an ci wani abun ko ya ya ne. Alhaji Isma'il da kanshi ya dinga bata a hankali kasan cewar da kyar take iya daga lebeanta har a samu tea ɗin. Kadan tashi ba ne yawa ba sannan aka kuma kwantar da ita.

Haka taci gaba da kwanciya a asibiti tana samun kulawar likitoci. Yan dubiya kuwa ba'a magana, ta ko'ina zuwa ake ana duba ta, har ta fara samun lafiya fuskarta tasabe kumburin ya baje sai gurin ciwon kawai. Mas'oud kam kullum yana asibitin tun safe har dare, hakan ya kuma tabbatarwa da Dije cewar Mas'oud shine farin ciki da walwalarta a rayuwa. Soyayyarsa ta kuma ninkewa a duk wasu sassan jikinta masu motsi da kai sakonnin gamsuwa ga abin da aka hakikance akan shi. Su Hameedah da Shukrah ma kullum sai sunje, a wannan zuwan ne kuma Shukrah ta fara nanikewa Mas'oud, ko be kulata ba sai ta kula shi saboda Mas'oud ba baya ba wajan tsarin halitta.

Duk da cewa Dije ba ta da lafiya hakan be hanata jin kishi ba, yadda Shukrah take nanikewa abin alfaharinta abin yana mata ciwo dan yafi raunin goshinta zafi da radadi. Yau kwanaki biyar kenan wajan karfe hudu suna zazzune ana ta hira, duk da cewa shi baya kula su amman wata maganar idan an sako shi yana magana, yanzu ma hakan ce ta faru, Shukrah tace.

“Abokin aiki gaskiya kana da kirki.” Ba tare da ya kalleta ba yace.

“Da nayi mene?” Shukrah ta saki murmushi tare da cewa.

“Gani muka yi tunda wannan abin ya faru da Dije kullum kana nan har ka fimu zama a gurin ta.”

Mas'oud ya juya ya kalli Dije wacce itama shi take kallo, hakan kuma ya tayarwa da Shukrah hankali tayi saurin katse su ta hanyar cewa.

“Kaga wasu jakunkuna da nayi order jiya.”

Sai ya waiga ta miko masa wayarta yana kallon jakunkuna, ba karya sunyi kyau, kuma zasu yiwa Oum Waleedah kyau.

“Sunyi kyau sosai kamar na siyawa madam, tana warkewa sai ta rataya a barta ko.?” Ya fada yana kallanta da murmushi.

Turo baki tayi tare da mai da idanuwa ta rufe ba tare da ta ce komai ba, abin da yake sake jan ra'ayinsa akan ta kenan wato yanga.

“Kana nufin Dije zaka siyawa?” Shukrah ta tambayesa cikin mamaki.

“Eh mana na murnar ta tashi lafiya ba.”

“Cab, ai duk an riga an siye su. Jira kawai masu su suke su dauki abubuwan su, sai dai next time.”

Shi ma daman ba wai da gaske yake zai sai mata ba, koda zai siya mata abu baya jin zai sai mata a gurin wanda ta sani bare kuma yar uwarta. Duk iya surutun da Shukrah take yi masa besa shi ya fuskance ta ba, sai rubuce-rubuce da yake ta faman yi tamkar besan abin da take cewa ba. Haka suka yini har Mas'oud d'in ya fito zai tafi tayi saurin biyo bayan shi. Dije na kallon ta fita gabanta ya dinga bugawa, gani take tamkar wani makircin zata ta yi masa, gaba daya bata yadda da Shukrah ba sam. Cikin ranta ta dinga addu'a dan tasan babu mai tsare mata Mas'oud sai Allah, shine ya had'a zukatan su a lokacin da basu sani ba, haka suna fatan ganin Waleed da Waleeda a tsakanin su.

°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°°
*MASARAUTAR BASANNABAS*

Tun a ranar da wannan tsautsayin ya affku ya ke cikin jimami, ko da suka shiga mota yaso ya daure ya tsaya dan yaga abinda zai faru da yarinyar da bafadansa ya rafkawa sanda. Amman ya kasa saboda shi baya san hayaniya, wannan dalilin ne yasa ko kallon gurin be sake yi ba bare asaka ran zai yi wani abu akai. Har suka je gida bai dena ganin jarumta irin ta wannan zakwakurar yar jaridar ba, da take son taji wani abu daga gare shi. Sashensa na musamman ya nufa kowa ya tsaya daga bakin kofa dan wannan ka'ida ne da indai ya shiga cikin wannan dakin to babu wanda yake shiga sai matarsa ko mahaifiyarsa.

Cikin isa da kasaita ta nufo sashen nashi, Bayan jakadiya ta mata iso. dan a kan kunnanta motocinsa suka shigo masarautar, bayin ta suna biye da ita sun sha kaya iri d'aya. Tana zuwa wajan kofar bayin nata suma suka tsaya yayin da ita kuma ta karasa ciki kamar yadda ta taho cikin tinkaho mai nuni da cewar ita d'in matar sarki ce. A zaune ta tarar dashi kansa a kasa ko glasses d'in dake manne a fuskar shi be cire ba. Daman idan da sabo ta saba da duk wasu dabi'unsa, musamman na shariya da kin kallon mutane tamkar wani makaho. Banda wani fitinannan kamshe babu abinda take yi, ta zauna can nesa da shi idanunta a kanshi tace masa.

“Sannu da dawowa, shin me yake faruwa ne naji ko'ina ya dauki zance nama kasa gane abinda yake faruwa. Shin me ya faru da kai?”

Ya yi shiru tamkar tana magana da gunki da aka sassaka da dutse. Taja tsaki a can kasan ranta dan tasan ko mahaifiyarshi ce a nan gurin take tambayarsa ba amsa mata zai yi ba bare ita da taga wajan baccin shi.

“Anyway! Nasan daman ba magana zaka yi. Amman ko da kane ina son ka yi min alama yadda zan fita daga cikin shakkun da nake ciki. Shin kun bige wani ko wata ne a wannan fitar da kuka yi?”

Ashe yaji duk abinda take ta fada, sai gashi ya daga mata kai ba tare da bata lokaci ba. Ta jujjuya idanuwa tare da tabe baki.

“Ance ai ta mutu ma, Allah ya taimaka ba kai zaka sha azumi sittin ba driver ne da ya yi sanadiyyar mutuwar ta. Sai dai kuma kai ne zaka ba da diyya, tunda kasan dai kai za'a sanyawa ido kaji ko?”

Kamar wata uwarsa haka ya kuma daga mata kai alamar 'eh' yaji. Tayi shiru dan tasan ta gama magana dashi ba kuma daga kan zai yi ba. Kusa dashi ta d'an matsa tasa hannu zata zare masa dark shade d'in da ya yi mata shamaki da ganin fuskarshi, ya yi saurin sanya hannu ya rike nata da take shirin cirowa alamar ba ya so. Sai ta kai bakin ta kan hannun nasa tare da sumbatar shi tana cewa.

“Yau ma ba zanga fuskar ka ba ko? Shikenan.”

Mikewa tayi tabar parlorn dan dama zuwa tayi taji tabbas daga bakin shi kuma taji. Abin da kawai za ta yi shine tasan yadda kudin diyyar da za'a kai sun biyo ta hannunta. Shi kuma abin ne ya yi matukar bashi mamaki jin cewar yar jaridar ta mutu. Ya dinga yin hasbunallahu a cikin zuciyar shi, a ranshi yana jin ashe daman mutuwa za ta yi shi yasa Allah ya ba shi iko da damar daga ido ya kalleta? Rabon da ya yi irin kallon nan ya manta, dan ko mahaifiyar sa ba zai iya tuna rabon da ya kalli kwayar idanunta bare ya gane a wane hali take ciki. Abinda ya sani kawai shine muryar ta da kuma yadda take tafiya. Ranar da kyar ya rintsa saboda abin da yaji na cewar badanshi ya kashe wata yar jarida daga yin tambaya. Duk kafafan watsa labarin da ya kunna da daddare labarin ake yi, sai dai su sunyi sabanin abinda yake jiyo wa a bakunan mutane wato.

Yarinyar tana karkashin kulawar likitoci, mutane kuma suna cewa ta mutu rufe maganar ake yi dan kar ace mutanan sarki ne. Sai da safe bayan ya fito fada su waziri suke sanar dashi cewar yarinyar ta farfado kar a damu nan ba da jimawa ba zata koma bakin aikin ta. Be ce komai ba sai da yaji duk wannan firgicin da yake ji duk ya ware baya ji yanzu.

••••
A ranar da Dije ta cika kwanaki biyar a asibiti ne yasa sarki Salman ya kirawo wani amintaccen bafadanshi yace yaje ya binciko asibitin da aka kwantar da wacce aka buga, baya son kowa ya san cewar zai yi wannan binciken saboda idan suka ji hanawa zasu yi, sunfi son su ji ana zagin shi a duniya ana cewa bashi da mutunci. Haka aka yi yaje da daddare har asibitin, wanda ya gano shi ne dalilin binciken da yayi na gidan rediyon da take aiki, yaje can suka sanar dashi, shi yasa besha wahala ba wajan ganowa. Lokacin da yaje ya tarar Mas'oud ya fito Shukrah na biye dashi, bafade ya tambayi nurses d'in dake reciption dakin da aka kwantar da ita.
Chapter 26 · 0% Book details