Sashe 66
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Karku damu da komai, ban fito ba sai da na shirya, ba kuma zan yi wasa da damar da na samu ba, zamuyi amfani da abinda muka san zai yi saurin mika wuya, saboda haka yanzu aikin ya rage naku, komai yana cikin bayanan da na tura muku kwanan baya, har da address da komai, kamar yadda yake bincike da zakulo komai akammu, haka muma zamuyi nasa, duk da munsan kusan komai a kansa sai dan abinda ba za'a rasa ba."
"Ya za'a yi da yaron nan Muhammad? Tunda har yanxu babu labarin mahaifiyar su."
"Zuwa yanzu banyi tunani akan sa ba, Amma shima zai mana amfani sosai wajen kama Sultan a hannu,saboda haka yanzu mu bar komai a yadda yake, ku fara aikin da yake gabanmu yanzu."
"Shikenan, angama."
"Ku tabbata ba'a samu wata matsala ba."
"Ba za'a samu ba."
"Shikenan duk yadda akayi, sai muyi waya."
***Suna kwance wajen karfe daya na dare, Amrah ta dad'e da bacci ita kuma Afrah na kwance tana danna wayar ta, shiru babu sound din komai sai ta fara jin kamar motsi kad'an kad'an, daina abinda take tayi ta sake kasa kunnen ta, da gaske motsin ne amma ta wajen bayan d'akin, matsawa tayi kad'an ta makale jikin Amrah tsoro na cikata, an dade tana jin motsin kafin ta daina ji, da k'yar ta samu ranar tayi bacci saboda tsoro.
Da safe suka tashi normal, bata cewa Amrah komai ba, sukayi breakfast suka zauna zaman kallon wani series film wanda ya dauke hankalin su sosai.
Suna zaune Ya Adnan yazo, ya kira Afrah ta bud'e masa kofar, zuwan sa ya sa suka sake shagala da hira, suka dafa abinci suka ci tare har wajen tara na dare yana gidan sannan yayi musu sallama ya tafi. Yana tafiya tunanin motsin da Afrah taji jiya ya dawo mata, sai a lokacin taji haushin mantawar da tayi bata gaya ma Ya Adnan din ba. Har sukayi shirin kwanciya hankalin Afrah ba a kwance yake ba. Hira Amrah take mata amma taki sakewa suyi hirar sosai musamman da aka dauke wuta wajen goma da rabi duk sai garin yayi tsit, ganin haka yasa Amrah ta kyale ta, ta kwanta bayan sunyi addu'ar kwanciya bacci sun kuma rufe ko ina. Kamar yadda Afrah tayi tunanin zata sake jin motsin ranar ma sai bata ji ba, har bacci barawo ya kwashe ta wanda bata sake farkawa ba sai da aka fara kiraye kirayen sallar asubah.
***Yana zaune har garin yayi haske sosai, yana jin yadda hayaniya ke tashi alamun mutanen Masarautar sun firfito kowa zai yi uzurin sa, sake kishingid'a yayi yana jin yadda komai yake wakana. Sosai lokaci yaja suna nan zaune, Musa ya sake komawa bacci ya tashi, ya shiga ya gyara bandaki ya fito.
"Ko zaka watsa ruwa?" Ya tsaya a gaban sultan yana rik'e da sabon soso
"Ok." Ya mike ya shiga ya yi wankan a gurguje ya fito babu Musa a dakin ya chanja kaya zuwa kanana marasa nauyi ya zauna, yana zama Musa ya dawo ciki ya samu waje ya zauna shima.
***Tawaga guda ce ta sarki da mukarraban sa suka nufi kofar Masarautar, kowa yayi mamakin fitowar sarki a lokacin, da kuma zuwan sa kofar, sai dai babu wanda yasan dalilin sai makusantan Sarkin. Sun dade a wajen suna lura da duk wani shige da fice na Masarautar ba tare da sun san cewa abinda suke kokarin hanawa shigowa ciki shi tuni ya tsufa a cikin Masarautar.
Har magriba babu wani bako da ya zo da nufin shigowa Masarautar, haka suka tattara suka koma da tunanin yadda akayi bayanin da suka samu akan cewa yau za'a shigo Masarautar tasu.
Suna komawa duk suka zube a gaban Sarkin bayan yasa an kira masa manyan yan duban Masarautar tasa.
"Ya akayi haka?"
"Ina matsalar take?"
Babu wanda ya motsa a cikin su, duk kansu na k'asa, dalilin babu wanda xai iya kushe ko kalubalantan abinda Babban su ya duba, tabbas duk sunyi nasu binciken a bayan nasa kuma sunga akasin abinda shi din ya dubo amma basu da ikon cewa ba haka bane, ko sun fad'a din ma Sarki ba yarda zai ba, saboda yafi yarda da gamsuwa da abinda Babba ya fad'a masa.
Ganin ba zasu ce komai ba yasa Sarki bello komawa ya zauna sannan ya umarce su da su fito da kayan aikinsu, suka dukufa, tsawon lokaci babu wani haske da suke gani a aikin nasu sai ma duhu da ya mamaye babu wani alamun akwai nasara, duk sun tsorata da abinda suka gani, sai dai babu wanda yake da k'warin guiwar sanar da Maimartaba abinda suka gani din. Hakan ya saka jan lokaci me tsawo kowa yana jiran wani ya fara magana, shirun nasu ya kara tunzura Sarki Bello Moddibo Saji ya daka musu tsawa me karfi yana nuna su.
"Zan saka a sauke min kawunan ku dukka Idan har zakuyi min wasa."
Da sauri Babba ya yaye nad'in kansa, ya kuma duka sosai cikin k'asa da murya yace
"Allah ya huci zuciyar ka shugaban sarakuna, gaba salaman baya salaman, tuba muke bamu da nufin bata wa sarki rai, sai dai abinda muka gani ne ya saka mu a cikin dimuwar da har muka gaza cewa komai."
Yana daya daga cikin abinda yasa Sarki Bello Moddibo Saji ke ji dashi kenan, yasan yadda zai bullo masa idan ma ransa ya baci, a hankali yaji ransa na sauka kad'an kad'an, idanun sa da suka soma chanjawa suka dan washe ya muskuta kad'an.
"Ina matsalar take?"
"Abinda muka gani Allah ya baka yawan rai shine, tabbas akwai masu yi wa aikin mu zagon k'asa, kuma suna aiki ne bayan sun samu labarin abinda muke kokarin yi, tabbas wanda muke zaman jira yazo har kusa da Masarautar nan, sai dai tun daga nan komai yayi baki bama iya ganin komai akai, mun duba babu wani kuskure,abu daya da muka tabbatar dashi shine ya dauko hanyar zuwa, amma bamu tabbatar da yadda ta kasance ba bayan zuwan nasa."
Zufa me yawan gaske Sarki ya share, ya had'e hannun sa waje daya yana ayyana abinda ya kamata yayi, ga dukkan alamu komai na neman kwabe masa, a tunanin sa tunda yana da wannan bataliyar na gaban sa babu wanda zai iya aikata komai ba tare da sanin sa ba, sai gashi duk da yasan da komai amma ya kasa aiwatar da wani abu akai. Duk da haka ba zai k'asa a guiwa ba,ba kuma zai bawa abokan gaba damar da zasu samu galaba akan sa ba, zai iyakar kokarin sa. A take ya tattara su, yasa aka bud'e musu wani babban daki anan cikin fad'ar tasa, suka dukufa aiki. Ciki ya koma ya fiddo da akwatin karfen nan, ya sake tabbatar da abinda yake ciki yana nan a inda yake, sannan ya mayar ya ajiye.
***Saida yaji kafa ta dauke gaba daya, ya tashi ya shirya, yayi nad'in kamar yadda ya tsara, ya fita bayan ya rufo wa Musa dakin wanda yayi nisa a baccin sa. Tafiya ya shiga yi a hankali yana kallon ko'ina, yadda ya samu zanen Masarautar haka komai yake, ya haddace kowanne lungu da sako na Masarautar shiyasa kansa tsaye yake tafiya yana kaucewa duk wani waje da yasan zai tarar da masu tsaron wajen. Tazarar da ke tsakanin inda aka ajiye su zuwa kurkukun yasa yayi doguwar tafiya kafin ya isa. Sanda ya isa, ya samu wani corridor ya tsaya saboda yadda wajen ya cika da tsaro. Yana nan tsaye wani daga ciki yayo wajen yana juya wata zabgegiyar dorina a hannun sa. Nannade hannun rigar sa Sultan yayi yana zuwa daidai wajen da yake ya sa hannu daya ya toshe masa baki, kokarin kwacewa yake ya daga masa kudade masu yawan gaske, zaro ido yayi ganin kud'i sai ya daina kokarin kwacewa ya saki jikinsa, sai da Sultan ya tabbatar da gane abinda yake nufi sai ya sake shi, suka sake matsawa chan inda babu kowa.
"Me kake so?" Ya tambaye shi yana dube duben hanya alamar a tsorace yake.
"Ka nutsu, inason ganin mutanen dake cikin kurkuku me lamba 108 ne, idan har ka taimaka na samu ganin su, zan baka ninkin wadannan kudaden nayi alkawari."
"Amma Sarki ya hana kowa ganin su, ya saka tsaro sosai akai, ina jin tsoro."
"Babu abinda zai faru, idan ma wani abu ya faru, ba zan taba ambatar ka a matsayin wanda ya taimaka min ba, zan dauki laifin dukka nayi wannan alkawarin."
"Ka tabbata zaka bani ninkin wadannan kudaden?"
"Zan baka, ka rike wadannan yanzu, zan kara maka kafin na bar nan."
"Shikenan ka tsaya anan." Yace sannan ya karbi kudin ya juya da sauri. Tsawon lokaci ya dauka dan har sultan ya fara tunanin ko yaudarar sa yayi sai gashi ya dawo.
"Tawo." Kawai yace masa da sauri yana juya, da saurin shima Sultan din ya bishi yana fatan ya samu abinda yake nema kafin yakai ga daukar wa Madaki abinda yake so. Babu kowa a wajen kamar dazu, kai tsaye kurkukun suka nufa ya daga kansa ya na kallon inda aka rubuta number, babu kowanne daki a kusa da nasu shi kad'ai ne a wajen daga chan karshe. Matsa masa yayi ya bashii hanya.
"Kayi sauri dan Allah, kar na shiga matsala."
Kafad'ar sa Sultan ya dafa
"Karka damu."