← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 108

Sashe 76

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥© Hafsat Rano
Page 36

Zafafa biyar na kud'i ne!!!

***
Shi yake driving din yana duba address din, tafiyar da nisa sosai shiyasa suka dan dauki lokaci kafin su isa, ya sauka daga kan kwaltar ya shiga gangarawa ta wata hanya da bata da kyau sosai.
    Yanayin yadda suke binsan be sa ya gane suna bin nasa ba, ganin hanyar ta kare daga inda suke ya saka su fitowa suka kashe motar, Safwan ya karbi key din shi kuma ya saka waya a kunne yana dialing number da aka kira shi da itan, tana ta ringing ba'a daga ba, har ta katse yayi saurin sake dialing looking very stressed out. Still wayar tana ringing amma no answer, kansa ya dora a saman motar yana jin kamar yayi failing, dafa shi Safwan yayi, yana kokarin calming nasa, ya karbi wayar yana sake gwada kiran shima, yana kira aka daga sai dai muryar sa tayi chan ciki

"Muna ta bayan wata bishiyar mangoro, akwai wanda suke neman mu ne and suna kusa sosai, please kuyi sauri, amma kuzo da yan sanda dan akwai bindiga a hannun su."

"Kana ji, karku fita daga wajen,muna kusa daku muma sannan..."

Daukewa wayar tayi, ya kalla da sauri sai ya ga kiran yayi disconnecting

"Me yace?"

"Neman su suke amma sun buya, kana ganin ya kamata muzo nan mu kad'ai? Akwai bindiga a hannun su, kar muyi risking life din Amrah."

"Ya zamuyi Safwan? Babu wani tunani a kai na, komai ya zama blank I'm not thinking straight,me ya kamata muyi yanzu?"

"Mun riga munzo, dole ba zamu fita daga wajen ba, ina ji a raina we are surrounded."

"Then ka tura wa Adnan da location din da muke, ka fad'a masa briefly yadda zai gane."

"Good idea." Yace da sauri yayi abinda Sultan din yace tare da bayanin yadda Adnan din zai gane sannan ya kirashi, yana dagawa yace ya duba whatsp dinsa yayi saurin kashe kiran.
    Duddubawa suka shiga yi har suka hango bishiyar mangoron,babu tazara a tsakanin su saboda haka kai tsaye suka nufi wajen. Wani iri Sultan ya shiga ji a jikin sa kamar bashi da lafiya, wani irin weakness ne yake sauko masa, ya kalli zoben hannun sa da yayi duhu sosai, sannan suka cigaba da tafiya a hankali har suka isa daf da bishiyar, kafin su karasa suka hangi wasu mutane su biyu suna shawagi a wajen, alamar sune ke neman su Amrah. Makalewa su Sultan sukayi yadda ba zasu gansu ba, aamma su suna kallon su daga inda suke, sun dan jima a tsaye a wajen sai kuma suka juyo suka bar wajen, da sauri Sultan fa Safwan suka karasa bayan bishiyar, Amrah na durkushe a k'asa idonta na zubda hawaye babu ko takalmi a kafarta, da wani irin sauri Sultan ya durkusa a gabanta, ya saka hannu ya jawo ta jikin sa gaba d'aya yana jin kamar kirjin nasa ya bud'e ya saka ta ciki.

"Ya Sultan..."

"Shissh...I'm here." Yace yana sake rik'e ta sosai, yana shafa bayanta a hankali

"Sultan, yakamata mu fita daga wajen nan."

Mikewa Sultan yayi tare da ita, ya kalli Muhammad dake tsaye shima yana kallon sa, yaji wani abu ya fizgeshi da karfi, da sauri duk suka kalle shi har Amrah ganin wani haske fari sosai na fita daga jikin zoben hannun sa. Ba karamin mamaki Sultan yayi ba ganin yadda zoben yayi haske sosai hasken da tun da ya saka shi be taba ganin yayi shi ba, sai kuma yaji wani sakayau kamar an cire wani abu me nauyi a jikin zoben.

   A daidai lokacin Sarki Bello ya farka da ihu, ihun da ya jawo hankalin mutanen da yawa dake kusa da wajen,da sauri Yarima Bilal ya kutsa kai dakin da Sarkin yake tun ranar, waige waige ya tarar dashi yanayi bayan ya jawo akwatin ya duba babu komai yana ganin Yarima Bilal din yayi wajen sa da sauri

"Yarima, ya shigo gidan nan, ya dau zoben nan, wallahi ya dauka, shikenan komai ya kare, komai yazo karshe."

"Wanne zoben?" Yarima yace dan shi har ga Allah ya manta da wani batun zobe.

"Amm baka sani ba ko? Na tuna baka san amfani shi ba, me ya faru dani? Ya akayi na ganni a haka."

Sai kuma ya kurawa Yariman ido sosai, ya kalli kayan jikin sa da rawanin dake kansa, sai kuma ya tuna abinda ya faru ranar, bayan sun jima suna hira shi da Yariman, dan tare suka ci abinci ma, daga nan kuma be iya tuna abinda ya faru ba.

"Yarima?" Yace yana nuna shi da hannu bayan ya tabbatar da abinda yake tunani. Kicin-kicin yayi da fuska yana kallon Sarki Bellon

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, shikenan ka gama dani, ka kashe ni, dama chan sarautar kake wa, shine ka taimaka masa ya shigo har nan ya dauki abinda kai kanka baka Isa kayi mulkin nan ba idan yana tare dashi, wanne irin mahaukaci ne kai, wanne irin d'a ne kai, Idan kayi hakuri dukkan fafutukar da nake akan wa nake yi? Nace akan wa nake yi idan ba kai ba."

"Menene wai amfani shi wannan zoben da kake magana."

"Zoben nan, shine garkuwata, garkuwar ka, kai dama duk wanda yake da alaka damu, gaba ki daya tsatson mu, barin zoben nan shine dalilin zama ta akan kujerar da har ta baka sha'awar da ka iya yaudarar ni mahaifin ta akanka,ko kasan kasantuwar zoben a hannun sa, wanda na gani yanzu a mafarki, komai ya lalace, ina kyautata zaton ya had'a daya barin domin karfin sa ya kai duk inda ake so ya kai.."

Shiru Yarima Bilal yayi yana jin gefe daya na zuciyar sa na dana sanin abinda ya aikata, me yasa ma be yi kakkwaran bincike akan zoben ba shima. Wani bafade ne ya tsaya dgaa kofa, yace

"Allah ya baka yawan rai, buzu da jama'ar sa na son ganin ka."

Kallon juna Yariman sukayi da sarki Bello, wanda gaba daya yanayin sa ya chanja wani abu me kamar tsoro ya bayyana a fuskar sa, yasan dalilin zuwan su, ya kuma san ba abu bane me sauki dawo da zoben nan.

"Muje." Yace mishi suka fito zuwa fadar, babu kowa kamar dai yadda yake duk sanda suka zo ganin Sarkin, dukkanin su sun bayyana tashin hankalin su karara, duk a tsaye suke sai buzu ne da ya ajiye wannan mudubin a k'asa be riga ya mike ba, kan Yarima tsaye ya wuce zuwa karagar mulkin ya haye, suka kalle shi dukka amma sai sarki ya basar ya matsa yana kallon mudubin, sai dai abinda ya gani wanda be yi zato ba shine ya sakashi ja baya da sauri

"Ya akayi haka? Ta yaya suka hadu da juna

"Kasantuwar zoben a hannun su ya saka hakan Allah ya baka yawan rai."

Sake matsawa yayi ya durkusa yana kallon danjojin, shiru yayi yana nazarin abinda yake faruwa. Mikewa yayi daga durkusan ya koma ya zauna sannan yace

"A kawo baiwar nan."

Duk sunyi shiru aka shigo da ita, aka gurfanar da ita a gaban su. Kowa ya zuba ido yana kallon abinda Sarkin zai yi, da kansa ya taso ya tsaya sannan yace

"Ina yaran da kika tafi dasu? Suna raye dukkan su ko daya ne yake raye ko duk sun mutu? Idan kika yi min karya..." Sai ya saka hannu ya zare takobin dake makale a jikin Buzu yace

"Sai na sare kanki a yanzu yanzu."

"Kayi min rai, tabbas yaran suna raye tunda ni da hannu na na raini daya, sai dai dayan ne bansan inda yake ba, tun bayan da na bar nan dasu, Madaki yà karbar min daya ya rik'e, tun daga ranar bansan ina ya kaishi ba, nasan dai tabbas yana raye, tunda ko da muka hadu be cemin ya mutu ba."

"Ina wanda kika raina din?"

"Yana nan, kafin a tawo dani nan na barsu a gida."

"Ku maida ita ku rufe ta!" Yace yana jefar da takobin,

Fita sukayi da ita,

***Yana zaune ya mike kafar sa da take masa masifaffen ciwo, Al'qur'ani me girma ne a hannun sa yana tilawa sai yaji wani abu kamar cirar k'aya ya fita tun daga tsakar kansa ya sauka zuwa tafin kafar sa, a hankali ya nemi ciwon kafar ya rasa, ya mike da sauri domin son tabbatarwa, da gaske babu ciwon babu alamar sa, sai wani irin sakayau da ya ji jikin sa yayi har yaji kamar zai fadi, dafa wa yayi ya zauna ya dauki landline ya kira dakin ta, tasowa tayi ta sameshi a zaune ya kalmashe kafar tasa wadda rabon da yayi irin zaman ya manta, zama tayi a gefen sa tana karantar sa.

"Ina ciwon kafar?"

"Babu." Yace yana jujjuya kafar

"Ikon Allah."

"Aifa sai ikon Allah, amma sai nake jin kamar zanyi zazzabi, kinga kuma na kinga ma kiran da nayi miki na manta abinda zan ce miki, kaina yayi wani dum babu dad'i."

"Toh, sannu Allah ya sa ba zazzabin bane, dan zazzabi baya maka da sauki."

"Ga girma ba."

"Allah ya sauwake, bari na samo maka magani."

"Yawwa Gimbiya, taimaka min da black tea dan Allah."

"Da me kuma?"

"Sai karamar wayata zan kira Sultan."

Shigewa tayi shi kuma ya zauna yana kisissima abinda ke shirin faruwa dashi yanzu kuma.
Chapter 76 · 0% Book details