← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 108

Sashe 56

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh." Suka had'a baki sannan suka umarce ni akan na wuce muje, nabi su ina tunanin inda zasu kai ni, ciki muka fara komawa suka tisa mu a gaba ni da Yabi sai filin jirgi, karo na biyu da na sake dawowa tun bayan zuwa na garin. Bayan kamar awa d'aya jirgin mu ya d'aga.
   Tun daga farkon hanyar da zata kaika Masarautar zuwa karshen ta, mutane ne suke ta tururuwar isa Masarautar wadda alamu suka nuna gagarumin abu ne yake faruwa a Masarautar. Hannun Yabi na kama da naji itama ashe rawa duk kuwa da mu a mota muke mutanen kuwa a k'asa suke. Muna zuwa kofar Masarautar muka ganta a rufe sai dai akwai tsaro sosai dan yadda wajen ya cika mutane na ta hayaniya. Lekawa wanda ke gaban motar mu yayi, suna ganin shi suka yi saurin bud'e kofar, motar ta kutsa kai cikin Masarautar. Bamu tsaya ko ina ba sai gaban fad'ar, fad'ar Maimartaba Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji, sai muka ga ashe cikar da akayi a wajen ma kad'an ce akan ta ciki.

"Ku fito." Yace mana bayan ya daidaita motar a waje daya, na sake kankame hannun Yabi dan yadda nake jin kamar zan fadi saboda jiri muka fito, duk sai hankalin mutane suka koma kanmu, kamar sun ga wani abun mamaki. Kai tsaye cikin fad'ar aka umarce mu da shiga. Daga nesa na hango wani kamar Maimartaba a k'asa kansa a duk'e,sai wadda ko tantama banayi Gimbiya ce a gefen sa, tana kuka sosai sai dai babu wanda ke kallon ma inda take. Kaina ya sake kwancewa ganin wani daban akan gararar Sarkin, wanin da ba kowa bane sai dan uwan Sarkin da duk wanda ya kwana ya tashi yasan yadda shakuwa me karfi ke tsakanin sa da Sarkin, dan babu yadda za'a yi Sarki yayi wani abu ba tare da sanin sa ba. Gefe muka samu muka rakube, karo na farko da muka samu kanmu a irin wannan wajen da ke ciki da manyan mutanen Masarautar wanda da tsakanin mu dasu sai dai hange daga nesa.

"Masha Allah, gasu ma sun karaso." Wani da yake tsaye ta gefen Sabon sarkin yace, duk suka maida kallon su kanmu.

"Taso." Wani ya bani umarni, ban iya tashi ba sai jan kafa da nayi na isa gaban su, na dukar na kai na saboda yadda kwarjinin su ya cika wajen.

"Wannan itace yarinyar da sukayi amfani wajen cimma burin su,kuma itace ta haifi yaran nan guda biyu da suka dauko suka nuna wa kowa a matsayin yaran da gimbiya ta haifa, gata nan sai kuji daga bakin ta."

Wani da ya kasance babba a cikin yan majalisar Sarki yace

"Baiwar Allah muna son jin me ya faru."

"Karki ji tsoron komai, kiyi bayani babu wanda zai miki komai anan."

Wani ya dora akan abinda dayan yace. Ba tare da dogon tunani ba na shiga basu labarin komai, wanda sai bayan na sanar musu da komai sannan na fuskanci duk abinda yake faruwa, sannan na fuskanci gadar zare aka shirya ma Sarki da gimbiya. Bayan jin bayani na, mutane suka yi ta girgiza kai wanda ina kallon lokacin da Sarkin ya girgixa kansa yana jin kamar k'asa ta zage ya shige.
   Sai dai ashe duk abin nan ba wai ainihin abinda ya faru bane, ba wai ainihin maganar da aka fara ba kenan, kawai sunyi amfani da magana ta ne wajen sake tabbatar da abinda suke son tabbatarwa dumbin al'ummar Masarautar Saji.
   Mutane ne wanda a kalla zasu kai su goma aka bawa umarnin shigowa cikin fad'ar, dukkanin su kallo daya zakayi musu kasan suna cikin tashin hankali, na farko ne ya fara magana.

"Tsawon shekara guda kenan da kashe min dan uwana, kuma ba kowa bane sai Maimartaba Sarki Usman."

Da sauri Sarki Usman ya dago kansa, mamakin maganar mutumin da be taba gani ba ya shige shi, shi da tun da ya fara mulki be taba salwantar da ran ko da kiyashi bane, balle mutum sukutun da guda? Amma ba wannan ba ne zai baki mamaki, sai yadda dukkan mutanen nan suka kawo kwakkwarar hujjar da har yanzu ni kaina na k'asa gane yadda akayi hakan ta faru, idan dai zaka duba karfin hujjar da suka kawo ne to tabbas babu wanda ba zai bawa Maimartaba laifin ba, amma kuma anya zai aikata haka? Anya zai iya kashe mutum akan haihuwa? Ko da sun aikata min zalunci mafi muni duk akan haihuwar amma ban yarda da Maimartaba zai iya aikata hakan ba."

"Menene Hujjar da suka yi Amfani da ita akan Maimartaba?"

"Na farko an samu shaidar mutane kusan arba'in wanda daga ciki har da makusanta Maimartaba, sannan dukkanin gawarwakin mutanen an same su ne a wani dakin sirri na Maimartaba din, wanda babu wanda yake shiga wajen sai shi Sarkin shi kad'ai."

"Hmm..."  Wadda ake bawa labarin taja doguwar ajiyar zuciya

"Bayan nan me ya faru?"

"Bayan nan komai ya kare, mutanen wannan Masarautar da kansu suka yi wa Sarki da Gimbiya korar kare, korar da ba'a taba yiwa ko da bawa bane irin sa balle Sarki, sai dai babu al'ummar da zasu kama Sarkin da ya kasance shugaba a gare su da wannan laifin su kyale ba."

"Kina nufin tun ranar babu wanda ya sake jin labarin Sarkin da gimbiyar?"

"Babu wanda ya sake ji?"

"Toh amma ya akayi kika samu kanki anan? Ina jariran ya akayi dasu?"

Kuka ta saka sosai ta kasa magana, tana tuna yadda komai ya kasance bayan ta basu yardar ta, ashe Amfani Kawai sukayi da ita don cimma manufar su.

"Da kansa Sarki Usman ya dauki yaran ya damka su a hannu na, ya kuma umarce ni da na tafi, nayi nisa da kowa na fara sabuwar rayuwa. Ya kuma gargade ni da kar na kuskura na dawo komai runtsi. Nayi abinda yace na dauki yaran da Yabi da nufin barin Masarautar. A hanyar mu ta tafiya ne muka hadu da wani me suna Mahdi, ya tsaidamu sannan ya umarce mu da mu zo ya kaimu inda zamu zauna xuwa gobe saboda kar mu tafi yanzu dare yayi mana, muka yarda dashi ya kaimu wani gida. Cikin dare muna kwance naji kamar kakarin mutum, na tashi da sauri na haska yar karamar fitilar, Yabi na gani a kwance tana kakarin mutuwa, da sauri na yi kanta ina kiran sunanta, bata iya amsawa ba sai dai ta dauki hannu na ta saka wani abu a ciki, ta dan hasken na kalla sai naga zobe me me tsananin haske, muryar ta na fita da k'yar tace

"Ki dauki yaran ku gudu, zasu kashe su."

"Su waye zasu kashe su? Me mukayi musu?" Na hau tambayar ta ina kuka sosai ganin yadda cikin ta ke fidda jini.

"Karki bata lokaci Aminatu, kiyi hakuri ba zan rayu ba, amma duk yadda zakiyi ki tabbatar yaran sun rayu, ki tabbatar sun kai lokacin da ya kamata su kai."

Tashi nayi da sauri jin motsin an taba kofa, nayi kan yaran na dauke su na yi saurin neman hanyar da zan gudu, window na kalla naga tsawon ba zai yiwu na iya hawa ba, na dawo ciki ina kuka Ina tunanin yadda zanyi na tseratar da yaran ko da ni bazan rayu ba. Da sauri na shinfida mayafi na wanda ya kasance babba kuma me kauri na daure su a ciki na bar musu yar hanyar da zasu sha iska. Daga chan gefe na hangi wata igiya, ba tare da dogon nazari ba na jawo igiyar na daura ta a jikin mayafin nawa,sannan nayi wajen window na leka naga iya zurfin wajen, nayi addu'a sannan na zura su ta window Ina jan igiyar hankali na a tashe duk yadda ake buga kofar wadda sai a sannan na gane Yabi rufe kofar tayi. Kamar an rik'e igiyar haka naji, na kama tagar na leka,sai naga inuwar mutum a tsaye a wajen, ban iya tantance mace ko namiji ba a lokacin sai da ta juya don barin wajen da mugun sauri, ina kallo ta kwance igiyar daka jiki ta rungume su tsam a jikinta, sannan cikin dakikun da basu wuce uku ba ta bace wa gani na, a daidai lokacin suka balla kofar suka shigo, a kuma lokacin ne zoben dake hannu na ya subuce ya fad'i, naji karar faduwar sa nayi saurin durkushewa a wajen na hau lalubawa, 'bari daya hannu na ya samu nasarar dauka, na dunkule shi ina mamakin yadda akayi zoben ya rabe."

"Tun daga ranar, na cinci kaina a cikin wannan wajen da ban taba saka ran fita ba, na rasa kakata a ranar, na rasa yarana."

"Lallai kin fuskanci abubuwa masu yawan gaske, sai dai Ina miki albishir da kwanakin da suka rage miki anan kad'an ne."

"Ta yaya zan fita daga gidan nan?"

"Allah ne zai yi ikon sa akan Azzalumai."

Rano
[4/12, 11:04 PM] Maman Maryam: Hafsat Rano

Page 27

***Kasancewar Gate din a bud'e yake ya basu damar ganin duk shige da fitan dake faruwa tsakanin gidajen biyu, Afrah ce ta matsa mata akan lallai sai sun fito compound din sunyi hoto, suna tsaye suna hotunan ta hangi fitowar sa daga gidan nasu, hankalin ta, ta tattara gaba daya tana kallon sanda yayi wajen motar sa. Tana tsaye jikin kofar da zai shiga motar, ta zubo da attachment din dake kanta yazo fiye da rabin bayan ta, sai kuma ta daura dan siririn dankwali a saman gashin, riga da skirt ne a jikin ta sai dai zaka rantse da Allah fitted gown ce yadda suka bi suka tafi da tsarin jikinta, kamar dama chan tare da jikin nata a ka yi su.

"Who's she?" Ta zunguri Afrah tana nuna mata Umaimah dake tsaye suna magana da Sultan din ta, duk da bata ji me suke cewa ba amma sai taji ranta ya sosu, ko dan ganin yanayin yarinyar, duk kuwa da zaman ta a k'asar turai amma zata iya banbance tsakanin me tarbiyya da mara shi.

"Wace ita?" Ta sake tambayar Afrah
Chapter 56 · 0% Book details