← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 108

Sashe 90

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Bayan sultan ya ajiye su a gida ya tafi, suka shiga tare wajen su Maman Yara suka gaishe su, suka amsa cikin girmamawa, Maman Yara ta tambayi wace Amaryar, karaf Afrah tace itace,Amrah tayi kasa da kanta tana murmushi. Ganin haka yasa Maman Yara gane Amrah ce, sukayi ta tsokanar Afrah tana dariya, sai kuma hira ta barke tsakanin Maman Yara da Afrah inda farat daya taji matar tayi mata ita ma kuma taji Afrah ta burgeta babu girman kai ga faran faran da kirki. Amrah ba gwanar magana bace shiyasa idan aka yi abu sai kawai tayi murmushi karshe sai tayi musu sallama ta nufi dakin ta. Kan gado ta fad'a, tayi ruf da ciki tana tunanin me ya kamata tayi, tana kwance Afrah ta shiga ta hawo gadon ta shiga jan hannun ta.

"Tashi zakiyi malaama ki gyara jikin ki."

"Wai Afrah me yasa kin raina ni ne haka dan Allah?"

"Allah ba raini bane, kece kin fiya sanyin jiki, kika zauna kina wannan nuku-nuku din naki sai dai kiga anayi wallahi."

"Naji, toh me zanyi?"

"Tashi zakiyi muje na wanke miki kan nan naki kafin na wuce gida, kiyi wanka ki shirya fes."

"Bani fa da lafiya!" Ta marairace

"Sai kiyi, Allah tashi zakiyi kin ga." Ta hau nade hannu, tashi Amrah tayi dan dama itama tunanin da take kenan, taimaka mata Afrah tayi ta wanke kanta tas ta busar mata dashi da hand dryer sannan ta gyara mata shi yayi kyau sosai. Kitchen Afran ta sauka ta dora simple dish ta bar Amrah ta shiga wanka.
Shiryawa tayi sosai ta gyara jikin ta, tabi ko wanne lungu musamman bayan guiwar kafarta, da wuyanta da hannayen ta da turarurruka masu sanyin kamshi. Simple kaya ta saka wanda suka dace da yanayin lokacin ta iske Afrah a kitchen din suka karasa aikin tare, suka jera komai a saman dinning.

"Bari na wuce gida."

Rik'e ta Amrah tayi

"Dan Allah karki tafi, ki bari gobe dan Allah."

"Mesa? Baki ji me umma tace ba?"

"Ai na kira Abba nayi masa maganar yace Allah ya kaimu goben, yau fa aka sallamoni sai kuma a barni ni kad'ai?"

"Auw wai har Abba kika kira? Tabdin."

"Please please please..."

"Shikenan, Allah ya kaimu goben."

"Yeee thanks swthrt." Tayi hugging dinta suka saka dariya.

Zama sukayi, suka kunna kallo kafin a kira sallah, shiru Amrah tayi tana tunanin maganar da sukayi da Sultan jiya, wunin yau gaba daya tunanin maganar take, matsawa tayi kusa da Afrah ta kira sunan ta

"Abokin kuka shi ake fadawa mutuwa ance." Tayi maganar tana dora kanta akan saman kafar Afrah

"Lallai kinji hausa, aina kika ji wannan karin maganar?"

Dariya Amrah ta saka

"Ya Sultan ne jiya ya fad'a min."

"Yawwa ko da naji."

"Afrah magana zamuyi, amma tsakanin mu,mu biyu dan Allah karki fad'a ma ko umma ce, sai lokaci yayi, yanzu ma abinda yasa zan fad'a miki saboda na rasa wanda zai fadawa gashi maganar na ci na, kinsan dai irin yadda abun yake."

"Nayi alkawari ba zan fad'a ma kowa ba."

"Ya Sultan ya gano family sa!" Tayi maganar cike da farin ciki.

"What!" Afrah ta zame kanta daga kafarta ta dafe chest din ta

"Allah da gaske."

"Ohh My God! Masha Allah, Alhamdulillah, kai amma naji dad'i kuma nayi masa murna, ya akayi haka? Dama irin haka na faruwa bayan lokaci me tsawo?"

"Al'amarin Allah Afrah, babu yadda baya kasancewa, na tuna umma ta taba cemin tana ji a ranta Sultan zai hadu da yan uwansa sooner or later, har ta bani labarin wata da ta bata a hatsarin mota, aka dauka mamanta ta mutu a hatsarin ashe da ranta, aka kaita wani gari far from inda akayi hatsarin wata mata ta dauke ta, ta kula da ita har ta girma, tayi aure ta haifi yaya da yawa, kwatsam wata mata me tallan mai da kuli-kuli dake kawo talla gidan tace mata akwai wata mata a gari kaza, suna bala'in kama, haka dai a karshe sanadiyar me tallan man nan aka gano ashe uwa da 'ya ne shiyasa take ganin kamar su sosai."

"Ikon Allah!"

"Yafi gaban komai, kuma kinga shi case din ya Sultan daban..."

Sai ta bata labarin a takaice amma banda maganar karshe ta Daddy tunda bata san yadda sukayi ba, ita dai Afrah tsabar mamaki ta gaza cewa komai, mamakin ta be karu ba sai da taji cewa ashe Sultan din d'an sarki ne, anan tayi tsalle ta dire akan Amrah tana ihun murna

"Wallahi ba karamin kyau zakuyi ba a fad'a wai wai, akwai ruguntsumi wallahi, zan so naga idon Shegiyar Umaiman nan lokacin kinyi mata nisa."

"Ni kuma expression din Hajiya kawai nake so na gani wallahi."

"Kinsan ta kuma da son abin duniya, balle ace Sarauta kai, ai dole kowa ya kiyaya har Mah-Mah wallahi Allah."

"Hmm."

"Ranki ya dade kina bukatar wani abu ne?" Afrah data zame k'asa tayi maganar cike da girmamawa, tuntsurewa Amrah tayi da dariya, haka sukayi ta hira cike da farin cikin abinda yake tunkaro su wanda har Afrah ta fi ma Amrah nuna zakewarta, hango kanta kawai take a Masarautar irin Masarautar Saji. Kira salla ne ya tashe su daga zaman da sukayi, sukayi alwala sukayi sallah bayan sun idar sukayi waya da Umma ta sake duba jikin Amrah sannan tace lallai lallai Afrah ta dawo gobe.

***Kamar yadda yake kaidar sa ko yaushe, baya shigowa gida tun dama chan idan yaga magriba ta gabato, sai ya jira anyi sallar sannan ya wuto gidan wani lokacin ma sai ya jira anyi isha'i sannan yake dawowa. Yau ma haka ce ta kasance, ya tsaya a wani masallacin hanya yayi sallah ya dad'e yana addu'ar Allah ya saukaka komai sannan ya fito, kiran layin Muhamad ya sake yi a karo na biyu, yayi sa'a tana shiga ya daga, suka gaisa ya ce yazo gobe ya same shi ya bashi address din inda zaizo ya kuma ce masa idan zai yiwu su tawo shi da kanwar sa. Ya amsa masa sannan sukayi sallama. A aljihu ya jefa wayar, ya ja iska zuwa hunhun sa ya fezar ya ji hucin ta taba saman kuncin sa.

"Alhamdulillah ya Allah."

Ya furta dan yasan babu abin yarda da godiya sai Allah, yadda ya warware masa kusan komai a cikin sauki fiye da yadda shi yayi tunani. Ya kuma juya abubuwan suka zama a yadda shi zai fi kowa farin ciki da hakan, idan ba Allah ba yasan babu wanda zai masa wannan shiyasa baya gajiyawa wajen nuna godiyar sa cikin kankan da kai.
Mota ya koma ya shiga, har ya dau hanyar gida sai ya tuna be siya komai ba, ya juya ya samu wani supermarket ya shiga ya sai abinda yasan zasu bukata sannan ya nufi gida.
Suna zaune suka ji ana bud'e gate din, da sauri Afrah ta mik'e tsaye

"Ango is back, bari kiga na gudu wajen su Maman Yara tun kafin ya tarar dani anan."

"Pls ki tsaya, Afrah!."

"Sai kiyi kuma, tashi zakiyi kije ki tarbe shi."

"Kai ni da ban da lafiya?"

"Goodnight." Ta daga mata hannayenta alamar bye-bye ta yi ficewar ta.

Kamar wadda kwai ya fashewa a jiki haka ta ja kafafuwan ta, ta bud'e kofar falon ta tsaya ta kasa karasa fita, tana jin sanda ya rufe kofar motar ta ji takun tafiyar sa zuwa inda take tsaye, motsawa tayi da nufin komawa ya karaso hannun sa dauke da ledoji.

"Sannu da zuwa..." Tayi maganar tana mika hannu zata karbi kayan hannun sa, kin bata yi, ya had'e su a hannu daya, yasa dayan hannun ya riko ta

"Ke da baki da lafiya, ai sun miki nauyi."

"Basu min ba." Tace tana sake mika hannu

"Noo barshi."

Ciki suka shiga ya ajiye kayan da sauri ya saka dayan hannun ya had'e ta da jikin sa

"Irin wannan tarbar nake so."

"Ok sir."

"Kamar gaske, ya jikin naki? Akwai abinda ke damun ki?"

"Babu komai, kawai weakness."

"Zai tafi a hankali, I promise." Ya d'age mata gira yana murmushi.

Kallon dining tayi, ya kalli wajen yaga warmers a jere, ya mike ya nufi wajen yana kallon ta

"Don't tell me girki kikayi?"

"Afrah ce ta yi ni kad'an na tayata."

"Da baku wahalar da kanku ba, yaushe kuka dawo ma har kuka huta balle azo maganar girki."

Jan kujerar yayi ya zauna ya ja mata ta kusa dashi ita ma ta zauna sannan yace

"Thank you so much, kunyi kokari Allah yayi muku Albarka."

"Amin." Ta amsa tana daukar plate domin zuba masa, karba yayi ya zuba musu a tare

"Bismillah." Tare suka ci abincin suka gama, ya tayata suka kwashe kayan sannan yace ta karashi wajen su Maman Yara, suka kwashi ledojin abinda ya siyo musu suka kai musu,suka tarar da Afrah ana ta shan hira ana dariya, Aminatu na bata labarin gidan sarauta da yadda bayi suke a gidaje irin wadannan. Sosai hirar tayi mata dadi ta samu chance ta dinga shigar da tambayoyin ta kad'an kad'an.
Shigowar su Amrah ya katse labarin, Sultan da Maman Yara suka fito harabar wajen sukayi magana ya fad'a mata komai da komai, da kuma niyyar sa ta tafiya, tayi masa addu'a da fatan alkhairi sannan ya fad'a mata Muhammad zasu zo gidan nan su zauna tare da kanwar sa, kar su yi saurin sanar dashi komai har sai gasu ga Safiya da Madaki da su Maimartaba da kowa da kowa dai. Tayi alkawarin kiyaye wa sannan sukayi sallama.

***Kayan jikin sa ya rage bayan sun dawo ya shiga wanka, ita kuma Amrah ta nufi dakin ta, ta dauki magungunan ta tasha ta kwanta a gefen gado ta ciro wayarta tana dannawa. Bayan kamar mintuna talatin ta tashi ta kashe wayar ta saka a charge ta shiga tayi wankan ta fito ta saka kaya kenan ya turo kofar ya shigo, laptop ce a hannun sa da charger ta, ya jona ya jawo ta zuwa saman gadon, ya hau ya zauna ya mike kafar sa ya dora ta a saman kafar tasa sannan ya bud'e

"Kinsha maganin ki?" Yayi maganar yana kallon ta

"Eh nasha." Tace

"Good zo ki tayani aiki."
Chapter 90 · 0% Book details