← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 108

Sashe 38

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_*

_*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_*

_*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*

_*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*

_*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*

_*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*

_*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_

www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

_*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

***Akan idon sa suka soma fitowa, itace a gaba sai Adnan, Afrah sai Sultan, karshe Umma da Abba, da sauri ya isa karesu tun kafin su gama fitowa gaba daya daga wajen, ya rungume Sultan da dukkan karfin sa, fuskar sa na bayyana tsantsar farin cikin ganinsu.

"Welcome back bro." Yace yana sakin sa

"Thanks d'an-uwa, kai kad'ai?" Yace yana dubawa

"Nida Mubarak ne fa, baka ganshi ba."

"Ina zai ganni, ai ba zai ganni ba." Ya amsa yana hararar Sultan

"Allah ban ganka ba sai da kayi magana, kasan mutum ya jima be ga dan uwansa ba."

"Kwaji dashi, da an kwana biyu zamu fara jin kanku."

"In your dreams." Yace yana dariya

Matsawa Safwan yayi kusa da Adnan ya taba shi

"Kaga yadda kayi kiba kuwa? Anya kana ma karatun nan da gaske?"

"Sai daka gama ganin shi sannan ka ganni kenan."

"Na ganka mana

Ta gefe ya saci kallon ta, ta wuce wajen yan uwan Umma da suma suka zo tarar su, hannun sa sarke cikin na sultan din suka karasa inda su Umma suke yayi musu sannu da zuwa sannan suka dunguma  suka tafi gida, Sultan da Afrah suka shiga motar Safwan, Amrah ta shiga ta Mubarak ita da Adnan ba tare da ta kalli ko bangaren dasu sultan din suke ba duk da ta kama shi yana satar kallon ta, haushin yadda Safwan keta rawar kai taji, shiyasa ma da aka zo tafiya tayi saurin shiga motar Mubarak din Umma kuma suka bi motar yan uwanta ita da Abba.

Ana zuwa kofar gida tayi saurin fita ta riga kowa shiga gida, yan'uwan Abba da Umma ne cike da gidan ganin su ya mantar da ita abinda take ciki, aka shiga nan nan dasu, ga abinci masu rai da lafiya gefe kuma ga na gargajiya nan, sai ta manta da bakin cikin da take ciki aka shiga hirar yaushe gamo.

Da murna Ammi ta tare shi, aka shiga gabatar masa da abinci, sannan ta aika Umaimah da mai aikinta suka kai gidan su Amrah, tace suyi musu sannu da zuwa kafin ta shigo. Wanka ya fara yi, kafin ya fito Safwan ya ajiye masa kaya komai sabo, iri daya da na jikin sa, ya shirya sannan yaci abincin yabi lafiyar gado dan sosai yake bukatar hutu. Daga shi sai dogon wando da singlet ya ware fanka a kansa ya rufe idonsa bacci me karfin gaske ya dauke shi.

   Fita Safwan yayi ya barshi a dakin bayan ya jawo masa kofa, a hanyar shiga cikin gidan suka hadu da Umaimah zata bangaren nasu, dakatar da ita yayi yace mata bacci yake, kamar ba zata koma ba sai kuma ta juya tana jin haushin Safwan din, kwalliya tayi sosai da zata zo gashi yanzu dole komai ya baci. Amma bata karaya ba zata dawo anjima.

   Rabon da yayi irin wannan baccin ya manta, dan sosai yasha bacci sai da Safwan ya matsa masa ya tashi da k'yar ya yi Sallah ya sake cin abincin da aka aiko masa daga gidan Umma, sannan ya fito suka nufi harabar gidan inda abokansu suke a zazzaune akan fararen kujerun roba, aka dasa hira me dadi har wajen magriba sannan suka watse.

Da daddare Daddy ya dawo, suka sameshi a falon sa,da fara'ar sa ya hau cewa

"Shiyasa naji gidan ya kara haske ashe likita na ne ya dawo, welcome home son, sannu da hanya."

"Yawwa Daddy,mun sameku lafiya?"

"Lafiya lou wallahi, ya aka kammala karatun? Ina fatan dai an samu abinda ake so."

"Sosai kuwa." Safwan yace

"Ai shine ma best student dinsu na shekarar."

"Ah Masha Allah, Allah ya sanya wa karatun albarka."

"Amin." Suka fad'a a tare.

"Toh alhamdulillah, tunda an samu abinda ake so sai kaima ka kawo wadda kake so, idan yaso sai aje a samu iyayenta a yi magana ko."

Dariya Safwan yasa, yayi caraf yace

"Dama maganar da muka fara kenan daxu Daddy, soon zai turo ni da maganar."

"Da yake kaine suda ko? Sarkin labari toh ban saka ba."

Dariya Sultan ya saka yana kallon Safwan da yayi kicin kicin da fuska,  duk da yadda yaji da Daddy ya ambato maganar,amma sosai Safwan din ya bashi dariya har sai da sautin dariyar tasa ta fito.

"Zan rama ne." Yace yana barin falon.

Tattaunawa suka cigaba da yi da Daddy akan karatun da kuma yanayin banbance banbance da suke tsakanin kasar mu Nigeria da ma sauran kashashen da suka cigaba, da haka suka shafe lokaci me tsawo suna tattaunawa sai wajen goma sannan yayi ma Daddyn sallama.

Yana shiga ya tarar da Safwan na kaiwa da komowa hankalin sa a tashe, nazarin sa yayi na d'an sakanni sannan ya jawo hannun sa ya zaunar dashi ya zauna a gefen sa.

"Menene?" Yace yana balle links din hannun sa

"Anya ban yi garaje ba Sultan?"

"Na me fa?"

"Na kai magana ta da Amrah gaban iyaye tun kafin mu sasanta kanmu, da gaske Sultan Amrah bata sona ko k'ad'an, wani daban ne a zuciyar ta..."

"Kamar ya?" Sultan ya fad'a hankali a tashe

"Ya kai kasan akwai wani a zuciyar ta dan kawai bata sauraron ka."

"Ita ta fad'a min da kanta, tace bata sona dan Allah na barta ta auri wanda take so yake son ta."

"Ta fad'a maka waye suke soyayyar?" Ya fad'a kirjinsa na bugawa, girgixa masa kai yayi alamar a ah sannan yace

"Tace idan na bata dama zata sanar dani ko waye, amma bana jin ina da karfin zuciyar da zan iya tsayawa na saurareta,Ina cikin matsala Sultan."

Ajiyar zuciya Sultan ya sauke da karfin gaske, wanda har yasa Safwan din kallon sa,yayi saurin waskewa tare da dora hannun sa a saman kafadar Safwan din

"Mubi komai a sannu, karka takurawa kanka da tunani kasan abinda hakan zai haifar, Ina so dai kawai ka sa a ranka babu wanda ke auran matar wani, idan kaga baka aure ta ba toh ba matar ka bace, mu cigaba da addu'a."

Sai ya mike ya cire kayan jikin sa a fad'a saman gadon sa yana fatan kar Safwan ya gane komai.

***Sati biyu da dawowar su, babu abu daya daya sauya na daga yadda Amrah take ma Safwan, tun bayan da taje ta samu Hajiya da maganar tayi kokarin ganin ta wayar mata da kai amma fafur taki fahimta sai ma hado ta da tayi da wasu turaren hayaki da tulin magungunan sha, hakan ya kara bata mata rai ta watsar da komai ta kuma kuduri aniyar sai ta san yadda tayi aka fasa auren wanda take ji a bakin su Umma saura sati biyu banda uban shirye shiryen da ake, komai baya mata dad'i, kowa haushin sa take ji shiyasa ma ta kara janye kanta daga harkar kowa ta sake zama introvert din gaske, a haka Anty Fatima yayar umma ta kawo wata mai gyaran jiki,ba karamin baci ranta yayi ba, tayi ta mita tana kunkuni babu wanda ya kulata.

Hadari ne sosai ga garin sai dai a lokacin be taso ba, tana kwance a daki tana lissafin yadda ranakun suke guda wanda har gashi ana maganar saura sati daya bikin wanda bata ga alamun fasa shi ba, duk yadda tayi babu wanda ya saurare ta, gaba daya Hajiya tayi brainwashing din duk wanda zata samu da maganar duk kallon wadda bata cikin hayyacin ta suke mata, tashi tayi jin wani tunani ya d'arsu a ranta, ta sauya kayan jikin ta zuwa doguwar riga, ta saka d'an karamin hijabi akai, ta fito, babu kowa a falon gidan sai tv dake ta faman yi ita kad'ai, kai tsaye ta fita daga gidan nasu ta nufi gidan dake kallon shi wanda ya kasance na su Safwan, tura gate din tayi, taga motar sa a fake a gefe alamun yana gida kenan, kai tsaye ta shiga takawa sai dai tun kafin ta karasa main entrance din suka yi kicibis dashi yana sauri zai fita, wani irin birki yaja dan saura kadan su gwaru da juna, kusancin da suka samu ya saka kowanne su a cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, kasa janye idon sa akanta daga kanta, rabon da ya ganta tun watarana da ya shiga gaida umma, tun ranar be yarda sun sake haduwa ba musamman yanzu da abubuwan bikin suka kara matsowa ya zama busy sosai, Yanzu ma fita zasuyi da Mubarak yayi wata mantawa shine ya dawo ya dauka dan ko motar sa achan ya barta ya hawo napep,ja da baya yayi kad'an yana bata hanya sai dai maimakon ta wuce sai ta tsaya ba tare da ta motsa ba, bakin ta na rawa tace

"Ya sultan."

"I'm so sorry." Yace yana girgiza mata kai

Sai ta fashe masa da kuka, da sauri ya ciro handy ya mika mata

"Karki yi kuka Amare basa kuka fa."
Chapter 38 · 0% Book details