← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 108

Sashe 22

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda ya saba, haka yayi ta gifta mutane yana ratsawa ta tsakiyar masarautar har zuwa babbar fadar sarkin da ke kan mulki, Sarki Muhammad Bello Moddibo Saji, babu wanda yayi yunkurin tsaidashi, har ya dangana da tsakiyar fadar, ganin sa yasa sarki sallamar kowa dake fadar, aka barsu su biyu, bayan an rufe kowacce kofa da zata iya daukar magana ko mai kankantar ta, ta fitar da ita.
Nadin kan nasa ya cire, kansa da babu ko gashi ziri daya ya bayyana yana ta kyalli kamar wata a daren sha biyar, kamar sa ta sha banban da ta mutanen da yayi irin shigar su, baki ne kakkaura, kuma gajere, be zauna ba, dan bashi da sukunin zaman, a hanya yake dole ce ta sashi ratsowa, ya fiddo wani abu kamar mudubi, ya ajiye a k'asa sannan ya haske shi daidai saitin Sarki, yan kananan danjoji ne guda biyu jajaye masu matukar haske suka bayyana, sai wata daga chan gefe guda d'aya da ta rabe gida biyu, hasken ta yayi matukar dishashewa sai ka kalla sosai zaka gane shi. Sai kuma wata itama daga gefe da babu ko haske a tattare da ita.

"Ranka ya dade, matsala tana sake gabatomu, ya kamata ayi wani abu."

Yace yana kallon sarkin daya zurawa mudubin Ido, babu ko kiftawa, kansa ya jinjina a hankali sannan cikin muryar sa me amo da sauti mara karfi yace

"Idan har kun k'asa gane inda suke ku nemo su lallai akwai tangard'a a aikinku, idan har wannan karamin aikin zai hana mu sukuni toh lallai kun gaza, gazawa irin ta faduwar bakar tasa, babu sauran abinda zan ce muku, ina bukatar a tabbatar min da in da take, da kuma inda yaran suke, daga yau zuwa karshen sati, idan har hakan bata samu ba, zan chanja ku,da wanda zasu maye gurbinku suyi aiki na kwarai."

Da sauri ya zube a k'asa, cikin kasa da girmawa yace

"Ranka ya dade, gazawar mu ba tana nufin kasawa ta har abadah ba,ba tana nufin shikenan komai ya baci ba, aikin ne yake cike da sarkakiya da bamu san menene Allah ya lullube ba, su waye taurari biyun nan da suke haskawa ako da yaushe, kullum hasken su kara karfi yake kusancin su da masarautar nan na sake matsowa, me suka taka? Me suka sani game da wani abu daya shude, aka kuma rufe babin sa tun shekaru masu yawan gaske."

"Ko su waye su, ko me suke takama dashi, muna nan muna jiran su."

"Akwai karfi a tattare dasu ya mai girma, karfin da mutum ko aljanna basu isa su gane komene zasu zo dashi ba."

"Aiki ya rage naku, a kwanakin da muka baku, idan kun so kunyi abinda ya dace, idan kuma kunki kun cigaba da wasa da damar ku..."

"Hakan ba zata faru ba ranka ya dade."

"Madallah da kai, zaka iya tafiya."

Nannade komai yayi, ya maida nadin nasa ya saka sannan ya bi ta kofar baya ya fice gaba daya daga gidan.

***Ya riga yasan inda zai sameta, tun da ya duba bata nan a inda ya zame mata office din ta, sai ya nufi chan din yana sake tattaro courage din sa, kafin ya karasa ya riga ya gama tsara yadda xai mata magana, yana kuma fatan ta fahimta yadda ya zauna ya dau tsawon lokaci yana tsara abinda zai ce mata. Jiñ an bud'e kofar yasa ta dago da idonta dake saman fence din wajen ta sakala hannayen ta ta makalo shi jikin hannun nata,guiwar hannun na saman fence din, kayan dake jikinta sunyi matukar amsar ta, ta yi rufe kan ta turban. Sanyayyen kamshin turaren ta na Jadore da Prada ya bigi hancin sa, ya rufe su da wani irin yanayi sannan ya bud'e su a hankali, suka sauka acikin nata, da ta d'anyi k'asa dasu har kana iya ganin yadda gashin idon ya kwanta a saman fuskar ta. Ita ta fara janye idon ta, ta maida su wajen balcony din tana bin wasu couples da kallo.

A daf da ita ta tsinkayi muryar shi, ya dora hannayen sa a saman fence din kamar yadda tayi,

"Naga alama kina son yanayi irin wannan, me kika fi tunawa a duk sanda kika kebe kanki ke kad'ai dan bana raba daya biyu tunani ne ke tsare ki har a manta da inda kike mafiya yawan lokuta."

"Lokuta da yawa nafi son na ji ni ni kad'ai."

"Umm, da gaske?"

Daga masa kai tayi alamar eh,

"Me yasa ka chanja kwana biyun nan? Bana jin dadin yadda kake acting."

Tace a hankali, gefe ya kalla, ta ina xai fara ce mata su hakura da juna bayan yasan su din suna kaunar junan su da gasken gaske, ta yaya zai ce mata ta bawa dan uwan sa dama, suyi soyayya bayan yana duniyar ba mutuwa yayi ba, anya zata fahimci yadda abin yake kuwa? Ba zata zarge shi da rashin adalci ba? Daga chan bayan kansa yaji wata murya na tunasar dashi waye Safwan, halin da yake ciki a yanzu da ma wanda zai iya shiga idan har be samu abinda zuciyar sa ke muradi ba, kenan shine yake da dama da Ikon da Safwan zai zauna lafiya, idan kuma ya samu matsala shine mutum na farko da zai fara zargin kansa da rashin sadaukarwa.
Kansa yayi fadi, fadin da yake jin kamar an saka abu an kwashe komai da ya ke cikin kan, babu abinda yayi saura sai fanko. Samun kansa yayi da sauka akan kafafuwan sa, ya had'e hannun sa waje daya, kana kallo zaka ga yadda Adam Apple dinsa ke kaikawo a tsakanin wuyan sa, sai kuma fuskar sa da tayi fayau kamar farar takarda, yawun bakin sa ne yaji ya kafe, ya kasa hado kalma daya da zai fad'a mata, bin sa tayi itama ta durkusa a kusa dashi, kwalla na taruwa a idon ta, ko menene zai gaya mata tasan ba me dadin ji bane. A hankali kamar wanda ya shekara guda ba tare da ya furta kalma daya daga bakin sa ba maganar ta fito, yanayin yadda ta Fito din zaka gane kwacewa tayi ta bayyana kanta

"Ple..eseee ki ba...wa S..a..f..w..an dama."

"Na'am?" Ta dago da sauri

Sai ya daga kansa cikin tabbatarwa yace

"Kinsan condition dinsa, yana kwance yanzu haka a gadon asibiti saboda abinda kika fad'a masa, yana shan wahala sosai, Safwan mutumin kirki ne, he deserve the best, shi ya chanchanta da ya same ki, nayi masa alkawarin zan yi kokari na wajen ganin na daidaita komai."

Girgiza masa kai take har ya gama maganar, ya kuma karashe kamar zai fashe da kuka, sai dai dakiya irin tasa da jarumta sun shanye komai.

"Dan Allah karka yi min haka ya Sultan, karka barni dan ALLAH."

"Amrahhhhhh..." Ya kirata ganin yadda take kuka sosai,

"Karka yi breaking heart dina, kayi min alkawarin zaka zauna always by my side, yanzu kuma kake cemin na bawa Safwan dama, ni ba toy bace da zaka gama playing da ita ka turawa Safwan shima ya buga, nima mutum ce da zuciya a kirjina."

"Na sani, nafi kowa sani, kuma ki sani this the hardest thing da zan taba yi a rayuwa ta, I love you so much kin sani, but Safwan deserve you fiye dani, kun dace da juna, kuna da wani abu mai muhimmanci a neman aure da ni na rasa shi, saboda haka ban cika ba, ina da wani gibi a rayuwa ta da babu abinda zai cike shi."

Sai ta mike tace

"Bazan taba son Ya Safwan ba, na tsane shi na tsane shi. I hate him!!!"

Ta shige da sauri tana kuka sosai, kukan da wanda aka taba balla wa zuciya ne kawai zai iya fuskanta.

Idon sa ya kada yayi jajur, ya kalli wayar ta sake yashe a wajen, ya sa hannu ya dauka, zuciyar ta ta shiga raya masa abinda ya kamata yayi, ya kuma yi na'am da hakan, babu bata lokaci ya dauki matakin farko na ruguje dukkan farin cikin su.

RanoWannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan*

*0903 234 5899*
Or
*09033181070*

Page 13 

*ANNUR PERFUMES* 
MASARAUTAR KAMSHI KENAN, MUNA BADA TURAREN MU AKAN FARASHIN SARI DA KUMA SAYI ‘DAI-DAI, SHIN NA LISSAFO MUKU ABUBUWAN DA MUKE SIYARWA KUWA?_

_TURAREN WUTA (NA KAYA/ GIDA/ JIKI/ DA TSUGUNNO. KHUMRAH, KULACCAM,_
_MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)_
_DECORATIONS (NA GIDA/OFIS/ KAMFANI DA SAURAN SU/ MUNADA INGANTATTUN KAYAN INFECTION (HERBAL WANDA BA ZAI SAKI WANI SIDE EFFECT BA, MUNADA DANA MATSI (STEAMING)_

_ANNUR PERFUMES NA GARIN *KANO* ADIRESHIN MU: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!. LAMBOBIN TARHON MU: 07086341096//07069037534. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NIJERIYA. SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA SAI ANNUR PERFUMES_

_WANNA SCENT EXOTIC??HEY.. WHICHEVER WAY YOU WANT IT WE’VE GOT YOU COVERED AT *ANNUR PERFUMES(CASTLE OF SCENTS)* FOR YOUR MIND/ YOUR SOUL.. AND YOUR HOME.. BE THE CENTER OF ATTRACTION WITH ANNUR PERFUMES.. WE ARE YOUR SCENT PLUG..TANTALIZE YOUR SENSE OF SMELL AS YOU SINK INTO BLISS. SAY NO!! TO DAMP SMELL LOVELIES. OUR DUKKANS LAST’S LONGER AND LINGER. VERY AFFORDABLE... DELIVERY IS NATIONWIDE

*******

*Sosai yaji karfin jikin sa tun bayan maganar da sukayi da Sultan, sallamar sa akayi daga asibitin suka wuce gida, kamar zai fadi haka yake jin sa ya samu da k'yar ya isa daki, ya kwanta, yana kwance Mah-Mah ta shigo, ta zauna daf dashi sannan tace

"Inaso muyi magana ne."

Tashi yayi da k'yar yana fuskantar ta

"Ka fad'a min gaskiyar abinda yake damun ka,ni mahaifiyar kace don haka Ina bukatar sanin halin da tilon d'ana yake ciki."
Chapter 22 · 0% Book details