← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 108

Sashe 81

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    A kofar dakin ya tsaya yana jin hayaniya na tashi, fasa shiga yayi ya koma dakin sa ya bari idan suka ragu sai ya je ya ganta, duk da ta matsu ya ganta din amma haka zai hakura xuwa anjima din.
   Rufe idon sa yayi kamar me bacci a zahiri sai dai a bad'ini tunanin abinda ya kamata yayi kenan, dole zai koma Canada, kuma dole zai tawo dasu domin dawowar su shine zai kawo kusan karshen komai, amma dole sai ya jira Safwan ya samu sauki, Maman Yara da wannan Matar sun dawo daidai, Amrah ma ta samu sauki tunda da ita zai yi tafiyar ba zai sake barin ta ba ko nan da chan zaije. Sai yaji chan kasan zuciyar sa, zuciyar sa dake son sauya halin da take ciki na bacin rai ta maye gurbin sa da farin ciki ta rada masa wata magana, maganar da ta saka shi yin murmushi duk da ba har chan ciki murmushin yake ba.
   Mike kafarsa ya sake yi yana son kore tunanin zuciyar tasa musamman a wannan halin da yake ciki na ganin lafiyar Safwan.
   Sai kuma saurayin nan ya fado masa, saurayin da ya taimaka ma Amrah, menene hadin sa da Madaki, me ya kai shi wajen me kuma yake nema? Be sake ganin sa ba tun bayan sun dawo,be ma kuma tuna dashi ba sai yanzu. Tashi yayi da sauri ya zauna yana tuna sanda ya ganshi a gidan Madaki sun shigo a lokacin shi kuma zai fita, idan har yana da alaka da Madakin me zai saka ya taimaka wa Amrah? Ba shi da amsar,sai dai yana jin son sake haduwa dashi, akwai tambayoyi masu yawa da zai masa, yana jin sa sosai kamar ba ranar ya fara sanin sa ba, kamar sun dade da haduwa a wani waje daban wanda ba zai tuna ba.
  Haka ya cinye lokacin wajen tunanin abubuwan da ya kamata yayi, shigowa Adnan yasa ya tashi suka je sukayi Sallah, maimakon ya dawo sai yayi zaman sa a masallacin har akayi isha'i, yayi shafa'i da wutri ya dan zauna kafin ya fito. Kai tsaye dakin da Amrah take ya nufa, ya tsaya a kofar ya kwankwasa, Umma ce sai Hajiya da wata kanwar Abba kawai sauran sun tafi, plate ne a hannun Hajiyan tana ta sababin kin cin da Amrah tayi tana mitar inda za'a samu lafiya idan ba'a ci abinci ba ya kwankwasa. Umma ce tace a shigo amma sai ya tsaya ya kasa shigo.

"Ya Sultan ya ka tsaya anan?" Afrah da dawowar ta daga gida kenan ta dauko wa Amrah wasu kayan da brush da toothpaste ta fad'a daga bayan sa.

"Afrah..."

"Bari nayi musu magana." Tace tana shigewa ciki

Komawa yayi daga gefe ya tsaya, yana tsaye suka fito, ya durkusa kansa a k'asa ya gaida su, Hajiya da tayi gaba kawai bata tsaya ba ya dan kalla sai kuma ya kalli Afrah dake masa maganar ya shigo ciki.

Kamshin turaren sa ne ya fara yi mata maraba, ta bud'e idon ta, ta rufe a hankali ta sake budewa tana jin wata nutsuwa na shigar ta

"Gata nan ya Sultan, taki cin abincin kuma Dr tace taci abinci sannan ayi mata allurar ta, sai fama ake da ita kila idan kasa baki taci."

Sai kuma tace

"Auw ya jikin? Ashe wai kaima baka ji dad'i ba, dazu naji ana fad'a."

"Da sauki."

"Allah ya kara sauki."

"Amin ya Allah, Nagode!"

"Bari naje wajen su Umma." Tayi gaba ta rufe kofar. Ledar da Afrah ta ajiye ya dauka ya fito da kayan ciki, bra ce da pant sai doguwar riga da toothpaste, da sauri Amrah ta rufe idon ta ganin ya daga bra din yana kallo, sai kuma ya ajiye su a gefe ya matso.

"Ya jikin naki?"

Kin bud'e idon ta tayi, tayi shiru dan sosai taji kunyar ganin kayan da yayi, har da dagawa yayi ya kalla sosai tana kallon sa ta gefen ido. Kafin ya shigo ta riga ta gama tsara yadda zata yi masa idan ya shigo, zata tambaye shi ya jikin sa, ta kalle shi sosai saboda she's missing him, amma daga shigowar sa sai taji gaba daya tayi losing confidence, ta kasa daga ido ta kalle shi musamman ganin yana kallon underwears dinta, a take abinda ya faru ana gobe ranar da zai tafi ya faru, hakan ya kara saka ta cikin matsananciyar kunyar sa taki bud'e idon ta. Tana jin idon sa akanta yana bin kowanne lungu da sako na jikin nata da kallo, idon sa yayi mata karfin da ta shiga jin sanyi sosai kamar wadda zazzabi zai rafke.

"Zaki chanja kaya ko?" Yayi maganar yana dago kayan. Tashi yayi ya shiga toilet din dakin, ya tara mata ruwa sannan ya fito, yazo ya kama hannun ta

"Tashi ki watsa ruwan sai kici abincin."

"Na'am..."

"Lemme help you." Ya rik'e ta, ya taimaka mata ta sakko, ta tsaya a gaban sa so close har tana jin hucin numfashin sa da yake da zafi.

"Ya jikin?" Ta tambaye shi

"Alhamdulillah."

Juyawa tayi zata tafi taji ya rike mata riga ta baya

"Bari na taimaka maki, naga kamar har yanzu akwai weakness."

Zip din ya kama ya shiga zuge mata, sai da yazo tsakiyar bayan sannan ya saka hannu ya balle mata bra din, da sauri ta juyo tana kallon sa, hankalin ta a tashe.

"Comman, taimaka miki zan,idan kika shiga sai kawai ki cire gaba daya."

"O... Ok." Tace tayi saurin juyawa tayi hanyar toilet din,

"Amrah..." Ya kira sunan ta, tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya tako ya tsaya a bayan nata, yasa hannu ya juyo da ita, yayi kokarin shigar da idon shi cikin nata amma ta ki, matso da ita yayi sosai har jikin ta na taba nasa, yasa hannu ya taba bandage din dake saman kan nata ya girgixa kansa

"I'm sorry, so sorry."

Bata bud'e idon ta ba, ya shafa fuskar ta da cikin hannun sa, a hankali ya kai bakin sa saman nata ya bata light kiss, wanda ya saka ta jin wata irin juya, tayi saurin dafa bangon wajen.

Cikin tashin hankali ta saki kofar, zuwan su kenan ta tambayi Sultan, taje dakin da yake baya nan shine ta biyo shi nan, hankalin ta ya tashi da aka ce mata baya jin dadi Shima, shine duk ta rikice ta biyo shi nan din, sai dai abinda ta gani ya saka ta kusan shid'ewa, mutumin da aka ce shima sai da aka bashi taimakon gaggawa shine a tsaye yana kissing mace. Yadda ta saki kofar ne ya saka Sultan juyowa, Amrah tayi saurin shigewa toilet shi kuma ya koma wajen kayan abincin ya shiga zuba musu.

**Ayi mun afuwa rashin jina, yara suka lalata min charging point n wayar©®Hafsat Rano

Page 41

Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na al’adance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da:
Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa
Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma
Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama
Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da:
Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi DA
Gashe gashe da soye soye kamar su
Kaza
Kifi
Nama
Doya
Dankalin turawa/hausa
Awara
Danwake
Gurasa
Kwado da dai sauransu....
Ba Mu tsaya anan ba——
The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe da suka hada da
Hoppers wato Fara
Milky candies wato alawar madara da kuma
Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke buqata...
Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka
IG: @the_flavorland
Whatsapp:08104673847
Sending Some treats your way.... l

Let us satisfy your cravings:
We Deliver anywhere and everywhere.

***Gama zuba abincin yayi, sannan ya ciro magungunan ya ajiye a gefe ya zauna yana cigaba da duba file din, shiru bata fito ba, ganin ta dade yasa ya tuna kayan da zata saka na ajiye a gefe, ya san kuma ba zata maida na jikin ta ba, dauka yayi ya tsaya a kofar ya kwankwasa

"Ga kayan ki saka."

Zuro hannu tayi xata karba ya rik'e,ta ja ya sake rikewa yana kokarin bud'e kofar, da sauri ta danno kofar, yayi dariya kad'an, dama tsokanar ta yake yi, bata yayi ya koma wajen da ya taso, sai gata ta fito tana taba saman kanta tana yatsine ido. Da sauri ya tashi ya riko ta, sannan ya taimaka mata ta zauna sosai.

"Zanyi sallah."

"Ok." Yace ya ciro hijab a kayan ya saka mata, ya taiamaka mata ta zauna tayi sallolin a zaune, tana gamawa ya dauko abincin ya ajiye ya matso da ruwa da magungunan,

"Oya." Ya debo abincin ya nufi bakin ta, a kunyace ta bud'e bakin ya saka mata, ta marairace fuska kamar zata yi kuka, babu taste a bakin ta ko k'ad'an,

"Ba zan iya ci ba." Ta juyar da bakin ta gefe ganin ya sake debowa, ajiye yayi ya had'a mata tea, sai ta karba tasha sosai, sannan ya bata fruit taci kad'an tasha magani da k'yar saboda yadda ta tsane shi. Sannu yake ta faman jera mata cike da kulawa da tausayawa.

"Zan kwanta." Tace masa jin kan nata na mata ciwo. Sake taimaka mata yayi ta kwanta sannan ya karasa cin abincin da taki ci duk da shima dan wanda yacin kad'an ne, saboda rashin appetite da rashin karfin jiki. Yana gamawa suka shigo tare da Nurse Falmata da zata yi mata allurar, yan sanda ne su biyu,hannu ya basu suka gaisa sannan suka bukaci magana da Amrah suna son daukar statement din ta, shi ya sake taimaka mata ta tashi zaune, ta amsa musu duk tambayoyin su, sannan suka bukaci sultan ma ya bada nasa bayanin. Fita sukayi ya juya zai bi bayan su Nurse Falmata ta tsaidashi

"Dr sai fa ka taimaka, dan dazu ma da k'yar aka yi mata."

Kallon Amrah yayi da idanun ta suka fito sosai alamar tsoro, yayi murmushi ya matso.
Chapter 81 · 0% Book details