Sashe 105
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Masu Nad'in Masarautar ne suka matso kusa, aka umarci Yarima Bilal da ya sauka, aka ce wargi ma wuri yake samu, yadda yaga Sultan, Safwan da Muhammad, da kuma yadda yake jin ihun mutanen ciki da wajen Masarautar yasan bashi da damar musu domin idan yace zai ja komai zai iya faruwa, ya lura da yadda jikin su Sarki Bello ma yayi tubus balle shi karamin kwaro, ko babu komai ai ya d'ana, shiyasa ma ana cewa ya saukan ya sauko babu musu, Sultan ya dare kujerar aka shiga nada masa rawani sannan aka bashi abubuwan da suka zama cikin dokoki da sharudan zaman mutum Sarki a Masarautar ta saji, cikin kankanin lokaci akayi komai aka gama, aka tabbatar da Sultan a matsayin sabon sarki, labarin da ya shiga kowanne lungu da sako na k'asar ma baki daya, hakan ya kara saka mutanen gari a cikin farin ciki, baka jin komai sai murna da sambarka. Kafin kace kwabo wajen Masarautar ta dinke tsaf da mutane ta kowanne lungu tuttulowa suke domin nuna farin cikin su bisa nadin sabon sarkin da ya kasance da ga adalin Sarki, Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji wanda mutane suke kauna.
Dole aka raka su Ummi cikin Masarautar saboda maza manya da masu kudi da yan siyasa dake ta shigowa kowa yaji dawowar Sarkin sai ya taho. Daya bayan daya Sarki Bello da mukarraban sa suka dinga ficewa har suka gama ficewa tas ya zama babu sauran kowa sai Sabon Sarki SULTAN da yan uwansa a gefen sa da Maimartaba da jama'ar sa.
****Bayan abubuwan sun fara lafawa ne Sarki Muhammadu Sultan ya saka aka kirawo tsohon Sarki Bello da jama'ar sa, suka dawo cikin fad'ar, daga nan ya saka aka je kurkuku aka fito da kowa ya saka aka taho da Safiyya nan, aka kuma kirawo su Maman Yara duk suka hallara, kan Sarki Bello a k'asa yana tunanin abinda Sultan din zai ce. Maimartaba ne yayi gyaran murya bayan kowa da ake bukata ya iso, ya soma jawabi a nutse
"Ina yiwa kowa fatan alkhairi ina kuma fatan na samu kowa lafiya bayan dogon lokacin da na dauka bana nan ni da mai daki ne,wanda da yawan ku anan kunsan makasudin da hakan ta faru, wanda zan iya cewa rami ne ka hak'a mun Bello ka tura ni ciki duk kuwa da yardar da nayi da kai, sai dai duk da haka babu abinda zan maka ko nace maka, sai dai fa ka sani dole ne zaka girbi abinda ka shuka tun a duniya..."
"Kai ne ka bani shawarar yiwa baiwar Allah Aminatu dashe, ashe ba da zuwa daya ka bani shawarar ba, sai dan na fad'a ramin da ka hak'a min me matukar zurfi."
"Sannan kuma da kai ne aka had'a baki wajen rama ni da d'a na, duk kuwa da lokacin ban san har da kai ba sai daga baya, nayi mamaki k'warai da na same ka kai da Buzu a cikin irin wannan abun,bayan kaf Duniya babu wanda nafi yarda dashi kamar kai, haka babu wanda gimbiya ta yarda dashi kamar dan uwanta buzu, sai kuma ya zama na ashe ku din da muka aminta daku kuñe kuka lalata mana farin ciki... Ku da kuka fi kowa kusanci damu..."
"Kiyi hakuri Gimbiya da abinda zaki jii..." Ya kalli bangaren da Ummi take yayi maganar sannan ya cigaba
"Mahaifin ki da dan uwanki Buzu su suka taimaka wajen shigar ki kunci da bakin ciki tsawon wannan lokacin, da taimakon su Bello ya zama duk abinda ya zama haka da taimakon su aka raba ki da gudan jinin ki, bani da gamsasshiyar hujja a lokacin shiyasa ban iya yi miki bayani ba. A lokacin da abun ya faru, nayi amfani da damar wajen sanya Aziza ta fita da jaririin daga Masarautar ,a tunanin su baya numfashi, wanda nasan idan suka san haka zasu halaka shi ne ko ta halin kaka, shiyasa na nuna miki bansan abinda ma kike magana akai ba, nayi kamar bansan kullin da akayi ba duk kuwa da bansan su waye kai tsaye ba amma nasan abinda suka shirya. Abinda yasa tsawon wannan lokacin ban sanar miki da abinda ya faru ba, saboda bani da masaniyar inda Aziza take, bansan inda zan neme ta balle naji halin da jaririn yake ciki, a tunani na ma ko bashi da rai ko kuma sun kama su sun yi musu wani abun. Dalilin haka yasa na kamu da ciwon hawan jini me karfi...Page 57
RanoNet
www.ranonet.com.ng
Register for your amazing data at a very cheap price.
Mtn 1gb @300 naira only
Mahaifin ki da dan uwanki Buzu su suka taimaka wajen shigar ki kunci da bakin ciki tsawon wannan lokacin, da taimakon su Bello ya zama duk abinda ya zama haka da taimakon su aka raba ki da gudan jinin ki, bani da gamsasshiyar hujja a lokacin shiyasa ban iya yi miki bayani ba. A lokacin da abun ya faru, nayi amfani da damar wajen sanya Aziza ta fita da jaririin daga Masarautar ,a tunanin su baya numfashi, wanda nasan idan suka san haka zasu halaka shi ne ko ta halin kaka, shiyasa na nuna miki bansan abinda ma kike magana akai ba, nayi kamar bansan kullin da akayi ba duk kuwa da bansan su waye kai tsaye ba amma nasan abinda suka shirya. Abinda yasa tsawon wannan lokacin ban sanar miki da abinda ya faru ba, saboda bani da masaniyar inda Aziza take, bansan inda zan neme ta balle naji halin da jaririn yake ciki, a tunani na ma ko bashi da rai ko kuma sun kama su sun yi musu wani abun. Dalilin haka yasa na kamu da ciwon hawan jini me karfi wanda nasan zai bini har karshen rayuwa ta. Tabbas shi zalunci dan aike ne, koman daren dadewa zai dawo wa me shi, sai gashi a lokacin da bakayi zato ba, na dawo tare da kuma abin mamaki da al'ajabi, albarkar yara uku riris masu daraja da cikakkiyar tarbiyya, kaga ko anan ya kamata ka gane duk abinda Allah ya kaddara zai faru toh babu makawa sai ya kasance."
"Haka yake Sarkin sarakuna."
"Saboda haka zan bar komai a hannun Sarki Muhammad Sultan, duk hukuncin da ya dace daku zai muku shi tunda yanzu ni ba hurumi na bane."
"Kasan dalilin da ya saka nayi maka haka? Sau daya ka taba zama kayi tunanin halin da nake ciki bayan mahaifin mu ya fifitaka akai na? Komai nasa kaine, magana daya biyu sunan ka zai kira, be taba tunawa dani ba ko kuma yayi magana ta ba, kai ne kawai a gaban sa, duk abinda ya faru shine ya jawo, shine ya assasa tsanar ka a zuciya ta, ya saka naji babu abinda ba zan iya ba akan ka."
"Wannan ba hujja bace, wannan ba uzuri bane Bello, saboda son faran tawa kanka sai ka cutar dani cuta mafi muni da girma? Akan me? Me nayi maka tsawon rayuwar mu da na chanchanci wannan toxarcin daga gareka? Ban taba zartar da abu ba tun da na hau mulkin nan sai da yardar ka, na yarda da kai saboda kai din dan uwa na ne, jini na, amma me kayi? Kayi amfani da hakan ka cutar dani da iyali na da basu ji ba basu gani ba, Bello shi mulki da kake gani na Allah ne, wanda yaso yake bawa, ba wai zabin mutum bane, saboda haka hujjarka bata isa hujjar da zaka aikata min wannan danyen aikin ba, bayan korar da kuka saka akayi min irin korar kare, kuka samin ciwo me nauyi Wanda zan ji bana sha'awar komai da ya shafi k'asar ma baki d'aya."
Dukkan gurin kowa yayi tsit ana sauraron Maimartaba, yayi magana me tsawo da ma'ana. Shigowar da akayi da Madaki ne ya katse maganar Maimartaba, aka kuma juya maganar zuwa abubuwan da suka faru da yadda suka faru suka kasance din, Maman Yara ta basu labarin yadda tayi bayan ta tafi da Sultan da irin wahalar da ta sha sosai kafin Allah yasa ta samu aikin nan a gidan marayun, kowa sai da ya jinjina mata yadda ta sadaukar da rayuwar ta domin cika alkawarin da ta dauka wa maimartaba a lokacin da zata bar Masarautar.
Safiya ma da tun shigowar da akayi da ita Aysha ta koma jikin ta, ta makale ta bada labarin yadda sukayi da yan biyu, da yadda sukayi rayuwa bayan ta rabu da Madaki, da yadda ta raini Muhammad din da yar da ta haifa Aysha ita da Madaki. Ta karkare da
"Ban san inda ya kai jariri dayan ba, babu kuma tambayar da banyi masa ba akan hakan, amma be sanar dani ba, sai ma chanja min da yayi cikin lokaci kad'an yayi kud'i ya gina gida yayi aure ni kuma ya rufe babi ba, duk da haka nasan inda yake ina bibiyar koman sa har zuwa lokacin da na same shi, sai kuma dauke ni da aka zo har gida akayi, aka kawo ni nan aka shiga azabtar dani duk dan na sanar musu da inda yan biyun suke dan sun gani a tsafin su yaran suna raye dukkan su, sannan sun ga cewa biyu suna tare da da juna daya kuma daban amma kuma sun kasa ganin komai bayan wannan, bazan iya fad'a musu ba, dan yadda nake son Aysha haka nake son Muhammad, shiyasa na gwammace su kashe ni akan na fad'a musu wani abu."