Sashe 54
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sun shirya fad'ar abinda muke so muji?"
"Basu shirya ba ranka ya dad'e, ko dazu mun yi musu abinda muke tunanin zasu karaya su mika wuya, sai dai duk yadda suka jigatan be sa sun karaya ba, daya daga ciki ma tana cikin ciwo, Kamar ba zata kai ba."
"A basu magani, a dakatar da duk abinda ake musu, a basu abinci me kyau, nafi son rayuwar su fiye da komai, dole ne su rayu, domin rayuwar tasu da kasancewar su a hannun mu zai zama wata tawaya ga abokan gaba!"
"An gama ranka ya dad'e."
Juyawa yayi ya bar wajen zuciyar sa cike da kudurin abinda zai aiwatar. Yana kuma jiran ranar da ko ma waye zai saka kafa a cikin Masarautar. A ranar ne zai tabbatar da abinda ya dade yana zargi!
****
***Zamewa tayi ta zauna a tsakar dakin kunya na sake kamata, maza sai dai a barsu, sam basu da ta ido wallahi, tana jin shi yana tsokanar ta, tayi masa banza. Kira taji yana yi da wayar sa, kafin chan a daga.
"Wai kana ina dan Allah?"
"Ina dakin ka ina jinyar matata."
"Wait what? Wai kana cikin gidan? Toh ai nazo dakin a rufe ko? Kai tsaya ai kuwa kamar naga takalmi a wajen amma hankali na yayi gaba ban lura ba. Wai da gaske kana ciki?"
"Muna ciki wallahi." Ya fad'a yana kashe mata ido daya, dauke kanta tayi da sauri tana murmushi
"Eh wallahi Afrah ce ta rufe mu, ah tana sane ta rufe, kuma dole na bata tukwuici ba."
"Toh shikenan ina jiran ka."
Yace sannan ya ajiye wayar, yazo ya zauna a gefen ta ya tankwashe kafarsa kamar yadda tayi har kafar tasa na gogar tata. Babu wanda yayi magana kowa da abinda yake tunani a ransa, har zuwa sanda aka bud'e kofar, Afrah a gaba tana raba idanu Adnan na bayan ta suka shigo. Hararar ta Amrah tayi bayan tayi saurin jan jikin ta ta matsa gefe sannan ta kad'a hannun ta alamun zaki sani.
"Me tayi miki?" Yayi maganar yana tashi tsaye
"Babu komai."
"Kike hararar ta kuma?"
"Yawwa dai Ya Sultan, ai idan ba'a gode min ba ai ba za'a zageni ba ko?"
"Saboda kinyi abin arziki ko?" Adnan riga amsawa yana hararar ta
"Kinyi abinda ya dace kanwata,kuma nagode sosai."
"Toh kindai ji." Tace tana wa dariya
"Muje dan Allah, ba kai ba Safwan babu dad'i ai kuma kasan dole mutane zasu neme ku."
Kiran sunan Safwan da Adnan yayi yasa Sultan saurin tashi, ya akayi ya shagala haka har ya manta da halin da ya barshi, duk da alkawarin da yayi na komawa ya duba shi, hanyar fita yayi Adnan din ya bishi suka tafi yana mishi bayanin yadda abubuwan suke.
"How far?" Afrah tace tana dariyar shakiyanci
"Afrah wallahi ki kiyaye ni!"
"Me nayi? Daga taimako? Ki rantse da Allah ban taimaka miki ba, bari naji." Ta kai hannu saman kanta
"Ehen, ina fever din?"
Hannu Amrah ta saka ta taba kan nata itama, da gaske babu zazzabi, bata ma san sanda akayi ya tafi ba, murmushi kawai tayi bata amsawa Afrah ba, dan bata masan me zata ce mata ba, dan wani karatun duk yadda aka karanta maka shi ba zaka taba gane shi ba sai yazo kanka.
Ciki gidan suka koma, Amrah ta sake wanka ta chanja kaya, mutanen dake ta tambayar ina Amarya ta dinga bi daya bayan daya tana gaishe su, su kuma suna mata fatan alkhairi a sabuwar rayuwar da zata shiga. Sosai take jin dadin addu'ar, a k'asan mokoshin ta, take amsa musu da Amin,ita kuma Afrah sai ta amsa a fili.
***Ran Hajiya ya baci sosai, fad'a take ta inda take shiga bata nan take fita ba, shi dai Abba be ce komai ba har ta yi ta gama,dan ya riga yasan Allah ne yayi Sultan din ne mijin shisa ma hakan ta faru,amma bashi da bakin da zai yi convincing hajiyar shiyasa ya bita da ban hakuri kawai ya ja bakin sa yayi shiru. Fad'an ta akan abu biyu ne, akan me za'a dauki Amrah a bawa wanda bashi da asalin, kuma ma a boye komai sai bayan an daura sannan kowa zai sani, idan wani abu ya faru fa? Idan labari ya chanja daga abinda suka sani fa?
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri, ina ganin kamar Sultan ba shine ya zaba ma kansa hakan ba, jarrabawa ce da zata iya samun kowa, kuma kinga Sultan duk a gaban idonmu ya tashi, tare ma da namu yayan,tarbiyyar su daya ce da Adnan da Safwan din, dan Allah Hajiya ki manta da komai kiyi musu Addua."
"Bance ai ba hakan bane ba, kawai dai kasan za'a iya samun wani hali daban da mu bamu san dashi ba, kuma ko ma ba haka ba, kuka san ta hanyar da akayi aka same shi? Wacce uwa ce zata bar danta idan har ba wani abun kunyar tayi ba?"
"Hajiya!?"
"Nayi karya ne? Yawancin yara irin haka abinda ya faru kenan, kalilan dinsu ne ba hakan ba."
"Toh dan Allah Hajiya mu kyautata ma Sultan zato,ko ba dan komai ba, ko dan Kasancewar sa yanzu a matsayin mijin yarmu."
"Toh me zance? Bayan sai da ka gaba yin abinda ka ga dama sannan ka sanar dani, Allah ya basu zaman lafiya."
"Amin ya Allah, kiyi hakuri Dan Allah."
"Nayi!" Tace a gajarce
Sake bata hakurin yayi, ganin da gaske ba zata taba yarda da dalilin nasa ba yasa ya bita a haka kawai. Saboda haka ne ma ya fasa fad'a mata akan tariyar Amrah wani sati me zuwa,yasan yadda zata kara hawa akan maganar, sai kawai ya sake bata hakuri yayi sallama ya tafi yana fatan Amrah ta samu rayuwa me inganci da Sultan, yana ji a ransa Sultan ba zai bashi kunya ba kamar yadda mutane da yawa suke tunani. Tun da maganar iyayen sultan ta fito wadda Abban ya rasa ta ina maganar ta fara shikenan mutane da yawa suka chanja yadda suke ganin Sultan din a dah, akwai wadanda ma suka fita harkar sa kamar dai yayi wani abu ne mara kyau ko kuwa shi ya zabi rayuwar sa ta zama a hakan. Har yaje gida yana tunane tunanen abinda ya sa mutanen duniya suke irin haka.
***Yana kwance kansa na masifar sara masa, idon sa daya ya kanne shi ta side din da yake masa ciwon ya dora hannu a saman kan ya dafe, tun bayan fitar SULTAN din be iya aikata komai ba, sai faman tunane tunane. Ya riga ya san abinda yayi shine daidai amma kuma ya kasa karbar hakan, zuciyar sa ta gaza daukar komai har yake jin tayi matukar yin weak din da bai taba jin irin sa ba. Iska ya fezar me zafi ya sake maida idon sa ya kulle jin an budo kofar. Mah-Mah ce dauke da tray ta shigo ta tura kofar sannan ta ajiye tray din ganin kamar bacci yake ta juya bayan ta kalle shi ta fita.
Kara bude kofar akayi, Sultan ne da Adnan suka shigo, yayi sauri isa wajen sa.
"Safwan, are you alright!?" Yace yana taba fuskar sa, dan bud'e idon sa yayi ya kalli Sultan din sai kuma ya mayar ya rufe.
"Abinda nake tsoro kenan,you ruined everything Safwan, da bakayi abinda kayi ba yanzu kalli yadda kake ji, why? Me yasa ka zabi haka? Is this what you call sacrifice? Um?." Yayi maganar da sauri da sauri yana firfiro da kayan cikin first aid kit dinsa
"Sultan please..."
"Shishh, karka ce komai, maganar zata iya lalata abubuwa da yawa, just stay still." Ya matso kusa dashi yana dora masa dan karamin pillow a saman kansa yadda zai samu support.
"Kana jina?"
"Eh..."
"Yawwa." Yace yana kafa masa inhaler a baki
A hankali ya shiga jan numfashin nasa da yake jin yana kokawar dauke masa. sauka a hankali ya daidaita.
"Alhamdulillah." Sultan da duk ya jike da zufa yace yana kama hannun sa daidai wajen pulse din sa
"Kana tunani da yawa ne, ka daina tuna komai ka cire komai a zuciyar ka, zan maka allurar bacci for you to be safe, idan ka tashi, komai zai wuce, komai zai zama kamar ba'a yi ba."
"Sannu Safwan." Adnan da duk tausayin su ya kama shi yace daga chan gefen inda yake tsaye,be iya amsa masa ba saboda yadda allurar taa fara daukar sa. Drip Sultan ya ciro ya daura masa ganin kwanukan da aka ajiye na abinci be taba komai ba, ya kuma san dama ba ci din zai ba saboda halin da yake ciki. Fita Adnan yayi ya barshi a ciki ya zauna yana kallon sa lokaci zuwa lokaci.
Ganin zaman ba na yanzu bane yasa ya shiga tunanin abinda zai fara. Da farko dai ya na son duk information akan Masarautar Saji, yana son ya san yadda suke gudanar da koman su, tun daga safiya zuwa dare, yaña so yasan iya adadin mutanen dake cikin Masarautar da kuma wadanda suke da kusanci da Sarkin na sosai. Ta Ina zai fara? Me yasa a duk sanda ya tuna abinda ke gaban sa sai yaji kamar idan ya tafi tafiyar kenan,amma kuma ya rasa dalilin da yasa yake jin ba zai taba iya fasa zuwan ba duk kuwa da abinda yake ji din.
Yayi nisa a tunanin sa har be ji sanda Mah-Mah ta shigo ba, tsayawa tayi ta na duban sa, sai kuma ta kalli Safwan dinta dake kwance yana karbar drip, a haka rayuwar sa zata kare Kenan shi? A haka zai ta fama da lalurar ne wai? Ji tayi zuciyar ta, ta tsinke sosai, tausayin danta take ji, irin tausayin da uwa zata ji akan d'anta, abinda take guje masa kenan, abinda take ji masa tsoro kenan, shi tasa zuciyar bata da karfin da zata yi irin wannan sadaukarwar.
Tasowa yayi ya tsuguna a gaban ta,
"Tabbas duk wata uwa da d'an ta yake a irin halin da Safwan yake ciki dole ne ta shiga damuwa, amma wallahi tallahi Mah-Mah, ban yi abinda nasan zai cutar da Safwan ba, bansan ya akayi yasan komai ba, bansan wanda ya fad'a masa ba, kuma wallahi da nasan abinda zai faru kenan da na hana faruwar sa."