← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 108

Sashe 108

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Matso dashi yayi, ta rada masa magana a kunne, yayi dariya yana rik'e ta ganin zata gudu, dariyar take itama, da k'yar ya kyaleta ta tashi ta taimaka masa yayi wanka, sannan suka fita main falon wajen da zai zauna yaci abinci. Suna fitowa duk masu kula daga wajen suka watse sai kukun da yayi girkin kawai, da hannu Amrah ta nuna masa ya matso, ya matso da sauri tunda dama yasan me kiran ke nufi, abincin duk yabi ya dandana bayan wasu mintuna sannan ta sallame shi, ta shiga zuba musu a plate, shi kuma yana danna waya kansa a k'asa. Sai da ta gama zuba abincin sannan tayi masa magana ya ajiye
    Bayan sun gama ne suka zauna duba inda ya kamata suje suyi ko two weeks ne, tare suke dubawa duk inda yayi musu sai a cire a ajiye, a haka har suka gama tara wuraren, sannan suka fi su daya bayan daya suna son tantancewa. Daga karshe suka karkare akan Maldives. Wayar sa ya jawo ya kira Safwan, yace yayi musu booking komai da komai daga Umrah da za'a su zasu wuce wani wajen.
  Haka kuwa akayi, suka dunguma har su Maman Yara suka tafi, aka bar Safwan da Muhammad akan sha'anin mulkin. Kamar an zare ma Sultan wani nauyi haka yaji shi sakayau, sukayi Umrah suka gama lafiya sannan sukayi musu sallama suka nufi Maldives.

***Tafiya ce me matukar muhimmanci da tsayawa a zuciya, sun yi komai cikin farin ciki irin wanda basu taba samun kansu a ciki ba, ana gobe zasu tawo Amrah ta fara zazzabi me zafi, duk da haka ta daure suka fita karasa siyayyar da zasuyi, kasancewar hotel din da suka sauka a wajen ruwa yake, sai ya zama na sun tsaya a wajen kafin su koma ciki, suna tsaye hannun sa a cikin nata suna kallon yadda ruwan ke hawa da sauka gwanin sha'awa, kamar wasa sai taji tana jin jiri, ta jingina da jikin sa sosai yadda zata fi jin dadi amma sai taji kamar na mintsine ta a mara, cikin kankanin lokaci sai ciwon mara, ta shiiga ya tsine fuska hankalin Sultan din na kan ruwa yana kallon wasu tsuntsaye masu kyau sai yaji ta damke hannun sa da ta rike da karfi, ya waiwayo ya kalle ta sai yaga hawaye na sauka a idon ta

"Lafiya?" Ya taro ta da sauri ganin zata fad'i, kuka ta shiga yi tana rik'e marar ta, da sauri ya sunkuce ta sukayi cikin hotel din. Akwai karamin clinic a ciki yana zuwa suka karbe ta lokacin har ta fara bleeding so badly, duk Sultan ya rikice ya riga ya gane miscarriage zatayi, amma ya akayi be gane tana da ciki ba a matsayin sa na likita? Haushin kansa yaji kwalla na taruwa a idon sa, yana son yara sosai sosai, da yasan tana dauke da cikin nan da babu abinda zai saka suzo nan.
A ranar tayi barin cikin, tasha wahala sosai kamar ba zatayi rai ba, dole suka fasa tafiya a washegarin amma suka baro resort din da suke. Sai da ta warke sosai sannan suka dawo.
Tun daga lokacin ya zama yana observing komai sai dai shiru kake ji wai malam yaci shirwa.

Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Allah, Matar Adnan ta haihu, haka ma Afrah, Safwan ya samu wata yarinya itama sun daidaita har ma an saka musu rana, lokacin bikin ne Amrah ta sake samun ciki Sultan ya hanata yin komai, amma shima cikin be zauna ba ya fice,sosai suka damu suka kuma shiga binciken abinda yasa cikin ke zubewa, wata babbar likitan mata Sultan din ya saka aka nemo ta zama ita ke kula da Amrah, ta duba ta sosai tace babu abinda yake damun ta kawai lokaci ne be yi ba. Dole suka hakura suka barwa Allah zuwa lokacin da Allah zai kawo.
Shakuwa tsakanin Sultan, Muhammad da Safwan ba'a magana, komai daya zai sai da sanin daya, kansu a had'e yake babu wanda yake jin cikin su. Safwan kamar yadda yayi na Mah-Mah alkawari, zaman sa da rayuwar sa tafi yawa a wajen Masarautar, baya kwana biyu be je ya ganta ba, gidan sa a nan kusa da su Maman ya zauna duk son ya faranta mata, har kuma gobe ita din yake ji a matsayin mahaifiyar sa, shiyasa ma Muhammad da Sultan suka fishi shakuwa da Ummi da Maimartaba, hakan kuma baya rasa nasaba da dama su chan suna lacking iyayen shi sultan dukka shi kuma Muhammad mahaifi, shiyasa zasu fi sabawa dasu ba kamar shi ba.

***Mah-Mah ce ta kira Amrah a waya tace mata umaimai tana so tazo Masarautar. Tace mata sai tazo, da tazo Amrah tasa aka shigo da ita, ta bata hakuri ta kuma bata katin bikin ta da wani bayerabe da suka hadu da wani bikin kawarta a Lagos din, sosai Amrah tayi mata murna, ta kuma taimaka mata taga Sultan din shima ta bashi hakuri, sannan ta taf tana musu fatan alkhairi dan tasan sun mata nisa sai dai kallo

***Alhamdulillah ya Allah, anan na kawo karshen littafin nan nawa me suna Abinda Ke Cikin Zuciya, ina godia sosai da hakurin da kukayi wajen bibiyar littafin nan, ina kuma baku hakuri akan rashin jina yadda ya kamata.
Ina ma kowa fatan alkhairi ina kuma rokon Allah ya yafe mana kurakuren da mukayi.
Ina rokon Allah ya bawa duk wata mace da take neman haihuwa yaya masu albarka, masu jin kai.
Na sadaukar da littafin nan nawa zuwa ga duk wata TTC MOTHER (trying to conceive) Allah ya azurta kowa da yaya masu albarka.
Zafafa biyar na godia da kaunar da kuke nuna musu, Allah ya bar zumunci har zuwa aljanna.

Zaku iya zuwa website dinmu me suna Ranonet.com.ng domin yin register,ku siya data Mtn a farashi me sauki. Sannan yar uwa zaki iya zama reseller inda zaki dinga siyar da datar kema ki samu naki, yafi zaman banza kina kwance a gida. Domin karin bayani sai ku yi min magana pc. Nagode

#Son so😘😘😘😘

Rano
Chapter 108 · 0% Book details