← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 108

Sashe 13

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Durkushe take a gabanta, kanta a duke a k'asa, kirjinta cike yake da tsoron abinda zata ce mata. A tunanin ta laifi tayi, shiyasa ma da kiran ya riske ta, ta dora hannu aka tayi ta zunduma ihu har sai da Yabi ta tsawatar mata, fadawan dake tsaron bangaren gimbiya maryama ne, su aka aiko kiran ta, suka kuma tusa k'eyar ta har katafaren bangaren na gimbiyar sai da basu bi duk wata hanya da zata hadasu da mutane ba har suka isa, suka kuma isar da sakon zuwan ta, izini akayi mata ta shiga, shine ta samu gefe ta rabe tana rarraba idanuwa, duk da sanyin A.C dake busa ta, ta ciki jike take da zufa tana lissafin hukuncin da za'a yanke mata idan har wani laifin tayi. Wajen mintuna nawa gimbiya bata ce komai ba, tana ta kare mata kallo sama da k'asa, kallon sauran bayin dake durkushe a gefe tayi sannan tace su basu guri, duk suka fita har amintacciyar baiwar ta, kafin ta kalli yarinyar gaban nata, wadda ba zata wuce shekara goma sha bakwai ba tace;

"Zaki yi min rakiya zuwa wani waje, wanda nake so ya zama sirri tsakani na dake, ya zama babu wanda zai sani, Idan har kika kasa rike min sirri zan dauki mummunan mataki akanki da dukkan ahalinki."

"In Sha Allah ranki ya dade zaki same ni me bin umarnin ki."

"Shikenan. Ke kad'ai nake son gani, haka ma bana so ki fad'a wa kowa abinda mukayi magana akai."

"Tashi kije, ki zama cikin shiri zan aiko miki da kayan da nake so ki saka,bayan magriba zamu fita."

Tashi tayi, tayi godiya ta fita, zuciyarta na ta sakawa da warwarewa a dalilin kiran da gimbiya ta yi mata, ta kuma dauko maganar rakiyar ta dawo dashi gaban tunanin ta, duk cikar fadar babu wadda gimbiyar ta nema sai ita, me yasa? Me yasa haka? Sukuku ta shiga bangaren nasu, ta samu Yabi a zaune ta yi Tagumi, ganin ta yasa ya tashi da sauri ta riko ta

"Me kika aikata yanzu?"

"Babu abinda nayi fa Yabi, wai anjima da magriba zan koma wajen gimbiyar akwai aikin da zata sani."

"Ita gimbiyar? Bata da wanda zai mata aikin sai ke? Ki fad'a min gaskiya idan akwai wani abu."

"Babu komai fa Allah." Ta wuce ciki, shiru Yabi tayi tana auna abin a ma'aunin hankali, me zai sa gimbiya ta nemi jikar ta ta duk mutanen dake zagaye da masarautar, hankalin ta be kwanta ba sam, tabbas akwai babban dalili.
     Da magriba kuwa sai ga Aiken gimbiya nannade a cikin wata leda, daki ta shiga ta shiga ta saka ta fito, tayi wa Yabi sallama tabi bayan baiwar da aka turo.
     Chan wani waje a bayan masarautar in da motocin mai martaba ne cike a wajen babu wanda ake bawa Izinin shiga sai wanda ya zama amintaccen masarautar, nan taga sunyi da baiwar, daga d'an nesa baiwar ta tsaya sannan tace

"Gimbiya na ciki tana jiranki."

Bin kofar wajen tayi da kallo sannan ta sa kai ta shiga, wani bafade dake tsaye yayi saurin bude mata wata mota yace ta shiga, tsoro ne fal zuciyar ta amma haka ta daure ta shiga, ya maida kofar ya rufe ya cigaba da tsayawa a wajen.

    Yabi na zaune ta tafka tagumi jakadiya ta shigo, dan tashi tayi tana gaida ta, kasancewar tun farkon zaman su a masarautar bata taba ganin jakadiyar haka ba, sai gashi ta tako har cikin gidan su, har dakin ta inda ta bata bayanin sakon gimbiya, ta kuma fito ta barta yayin da tayi mutuwar zaune.
    Kuka ta saka sosai tana jin kirjin ta yana zafi, Aminatu ita kad'ai ce take gani zuciyar ta, tayi sanyi. Me yasa zasu zabi tauye mata rayuwa? Saboda su masu mulki ne? Sbaoda su sune mutane su kuma ba komai ba?wannan wacce iri yar rayuwa ce muke ciki? Me kudi shine kawai mutum talaka ba bakin komai bane. Bata da yadda zatayi, ba zata iya hana su abinda sukayi niyya ba, sai dai zata kai karar su wajen Allah, shine kadai abinda tasan zata iya kuma tasan zai bi mata hakkin ta

Jin tashin motoci tayi daga chan nesa, kafin daga bisani taji wadda take ciki ta tashi itama, tafiya sukayi me dan nisa a cikin masarautar kafin su fita daga ciki su hau titi sosai. Tsayawar da motar da take ciki tayi shi ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, ta kalli kofar dake budewa a hankali har ta gama budewa kafin yayi mata Izinin fitowa.
    Fitowa tayi ta tsaya, tana kallon wajen da yafi yi mata kama da tashar jirgin sama, wurga idanuwan ta, tayi tayi awajen tana son gane in da take, bafaden dake tsaye kusa da ita ta dan matsa daf dashi sannan tace

"Dan Allah Ina ne nan?"

"Filin jirgi." Ya amsa a takaice

Kanta ne ya daure ta sake yinkurin tanbayar sa, amma sai ya dakatar da ita ta hanyar yin gaba yace ta biyo shi.
Bin sa ta shiga yi har suka dangana da wata kofa, daga nan kuma sai gasu a harabar tashi da saukar jiragen, jikinta ne ya fara rawa, kanta ya fara juyawa taji tana neman zubewa amma sai wata baiwa da bata san da ita a tafiyar tasu ba, ta tareta, ta kuma riketa har zuwa sanda suka haura saman matattakalar da zata kaisu cikin jirgin, sannan kuma ta cigaba da rik'e ta har zuwa sanda jirgin ya daidai ta a sararin samaniya, ta kuma taimaka mata sanda suka isa inda zasun. Suna fitowa mota na jiransu, ta dauke su zuwa wani babban waje da sai data nutsu sosai ta gane asibiti ne. Jikin ta ya kara yin sanyi sosai, sanda suka fara haurawa zuwa wani shashe dake chan gefen cikin asibitin tsoro ya kara kamata, ita dai tun farkon tasowar su zuwa yanzu da suke nufar wata babbar kofa bata ga gimbiya ko wani alamu da zai nuna tare suke, toh me hakan ke nufi? Suna isa kofar baiwar ta dakata sannan ta nuna mata hanya

"Gimbiya na ciki na jiran ki."

Kasa motsawa tayi, ta tsaya idonta na kawo ruwa, tace wa baiwar

"Dan Allah inane nan din da muka zo."

"Asibiti ne mana, baki ga alama ba?"

"Na gani, amma garin nake son sani."

"Kinsan Ikko? Birnin Legas? To nan ne, kiyi maza kar ta gaji da jira tare suke da maimartaba kuma."

Jan kafafuwan ta tayi da kyar ta tura kofar ta shiga, bakin ta dauke da addu'a, bata yarda da maganar baiwar nan ba da tace har da maimartaba sai da ganin ta ya sauka akansu, shida gimbiya zaune a gaban likitan suna magana k'asa kasa. Yau ne rana ta farko da ta taba ganin sa haka a zaune babu Taron mutane babu wani me tsaran sa, sai taji dakin ya karayi mata girma, durkushewa tayi a wajen ta chusa kanta a cikin kafafunta

"Wannan ce yarinyar ranka ya dade? Kana ganin zata iya dauka kamar tayi karama."

Likitan ya fad'a cikin harshen turanci, amsa masa sukayi sannan yayi rubuce rubuce a jikin takarda sannan yace ta taso su shiga ciki.

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________

_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )

💙

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Ignore the typos
*Wannan littafin na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin dake kasan LITTAFIN*

Page 9
©Hafsat Rano

***Da jan kafa ta isa inda likitan ya shiga, ta tsaya daga gefe kanta na sarawa,wata nurse dake gefe ta matso ta kama hannun ta suka shiga ciki, dakin daukar jini ne, haka tana ji tana gani aka dauki jinin ta, aka shiga gudanar da gwaje gwaje akan jinin.
Sannan suka wuce wani daki inda za'a mata gwajin STD da sauran tests da zasu tabbatar da lafiyar ta. Fitowa likitan yayi ya dubi maimartaba yace

"Ranka ya dade yarinyar nan ta kai 20years kuwa?"

"Ta kai." Inji gimbiya maryama

"Ok, but she looks very young,sannan kamar bata taba haihuwa ba, an fison wadda ta taba haihuwa shine ka'idar."

Kallon juna sukayi, ta marairace fuska tana kallon maimartaba,

"Babu damuwa Dr, you can carry on with your work."

"Owk." Yace ya juya ya shige ciki

Sai kuma ya dawo da baya yayi wata magana sannan ya koma ciki...
Chapter 13 · 0% Book details