Sashe 95
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***Ta kasa zama tana ta zagaye a dakin, motsi kad'an sai ta leka ko zata gano su, yana kallon ta be ce mata komai ba, yasan dama zatayi abinda ma yafi haka, shi kansa misalta irin farin cikin da yake ciki ya isa, ko da likita ma yazo duba shi da safe cewa yayi he's good for discharge saboda yadda ya ganshi akan kafafunsa ba wani alamun ma ya kwanta.
Ganin taki nutsuwa ne ya saka shi saka baki ya kirata, ta amsa hankalin ta still yana kofar,
"Gimbiya zasu zo fa, kila sun makara ne wajen tashi kinsan sun yi tafiya."
"Amma ya kamata ace sunzo tuni, I'm damn worried."
"Don't be, zasu zo in Sha Allah."
"In shaAllah..."
"Assalamu alaikum." Sultan yayi sallama yana turo kofar dakin, yadda fuskar su ta fad'ad'a zuwa tsananin farin ciki zaka gane yadda jin maganar sa kad'ai ta saka su, ya shigo bayan sun amsa Amrah na biye dashi, fuskar ta fayau tana ta kokarin riga shi shiga domin ganin su waye wadannan lucky parents din da suka samu yaya kamar Sultan da Safwan? Ta san dole su din sun yi ta kowanne bangare, bata gama ayyanawa a ranta ba fuskarta ta hasko mata Gimbiya, Babbar mace yar gayu ta karshe, yadda tayi tunanin ta, ta wuce haka nesa ba kusa ba, a dah tana ganin Mah-Mah a jerin hadaddun mata yan kwalisa, amma ganin Gimbiya sai ta shafe Mah-Mah a idonta, hatta skin colour dinta abun kallo ne, koman ta kamar na Sultan sai dai basa kama, yafi dauko kalar fatarta da wasu abubuwan nata.
Rik'e ta, tayi ta rungume ta a jikinta tana jin wani irin yanayi na wai itace yau da d'an cikin ta a gaban ta, tare da matar sa kila ma har da rabon baby girl ko boy, bakin ta ya gaza rufuwa ta kuma kasa daina mika godiya ga Allah azza wa zalla,domin shi ne ya amsa mata addu'ar ta a lokacin da ba tayi zato ko tsammani ba.
Yadda suka sake da Amrah daga Maimartaban har Gimbiyar ya saka Amrah sakin jikinta dan ta lura su mutane ne masu sanin yakamata , masu matukar kirki da faran faran, yadda Maimartaba yayi ta jan ta da hira yana mata tambayoyi ya saka ta kaunar mutumin ganin babu girman kai ko izza irin ta wasu masu Sarautar, musamman ma shi da yake matsayin Sarki.
Babu kalar soyayyar da mutane biyun nan basu nunawa Amrah ba, dan hatta abinci Gimbiya ce tace su zauna ita da SULTAN ta basu, sukayi ta mata dariya Maimartaba yana tsokanar ta, ita dai bata damu ba, so take abinda ta dade tana hasashe ne, bata damu da girman da sukayi ba, ita kallon yara kanana take musu musamman Sultan da take ganin kamar dan babyn ta ne aka dawo mata dashi, so take ta nuna masa soyayyar da tasan yayi lacking duk kuwa da girman sa, shi dai duk ya rasa ina zai saka kansa saboda murna, wai shine yau yake gaban iyayensa suna treating dinsa kamar karamin yaro, iyakar rayuwar sa be taba jin sa haka ba, shi a kullum kallon babba yake baya taba tunanin kansa a irin matsayin, shiyasa yake wa Sultan acting din babban wa saboda baya daukar kansa kamar yadda shi Safwan din yake abubuwa musamman a gaban Mah-Mah, yayi ta sha'awar hakan idan yaga yanayi amma baya taba hasaso kansa irin wannan yanayi, sai gashi yau ya samu kansa a irin yanayi ya kuma ji yadda Safwan din yake ji musamman idan yaga yana wa Mah-Mah shagwaba duk kuwa da girman sa, ashe dai komai girman ka a gaban iyayenka kai din yaro ne karami, suna kuma kallon ka a yaro ne duk sanda kake gaban su.
Zaman asibitin dai sai ya zama kamar ba asibiti ba, gashi su akwai tsari ba haka kawai zasu sallami mutum ba, sai da lokacin da suka diba ya cika sannan suka zo suka sake duba shi sosai, suka tabbatar da jinin nasa ya dawo normal da kuwa yayi mugun hawa har sunji tsoron kar ya samu matsala, sai da suka tabbatar da komai normal sannan suka yi discharging dinsu, suka tattara sukayi gida inda Sultan ya wuce domin dauko musu kayan su daga hotel din.
Wani irin shiri Gimbiya ta saka hadimanta suka hau yi, daki guda aka ware aka gyara shi gyara na gaske, aka kawata shi da kayan kawa. Anan aka sauke Amrah a ciki, kafin ma Sultan ya dawo ta tare a ciki, yana zuwa Gimbiya ta saka masa full stop tun a kofa, tasa aka karbi kayan aka shiga dasu sannan tace ya wuce bangaren Maimartaba a chan ne masaukin sa yake, ya hangame baki zai yi magana ta tura shi ta jawo kofar tana dariya
"Yata tana bukatar hutu."
"Ni kuma fa?" Yayi managar yana langabe mata kai, dungure masa kai tayi, ya taba gurin yana sosawa.
"Wash kaina."
"Wuce muje." Ta tusa shi gaba har wajen Maimartaba, yana kishingid'e fruits a gaban sa sai dai ko kallon su be ba, ya yi zurfi a tunani, yana ganin su ya tashi zaune da sauri yana fad'ad'a fara'ar fuskar sa.
"Allah Nagode maka da ka dawo min da farin cikin gimbiya ta."
Dariya suka saka a tare,
"Ga danka nan na kawo maka,a barni na 'yata."
"Auw yar haka ce?"
"Eh."
"Shikenan zo Muhammad, rabu dasu idan tayi wari ma zamuji ai ko me Ake kullawa."
"Ba zatayi ba kuwa."
Juyawa tayi ta koma, Sultan ya zauna daga gefen Maimartaba, ya shiga matsa masa kafa a hankali.
"Muhammad ya rayuwa?"
"Alhamdulillah Baba."
"Kaga yadda Allah yake al'amuran sa ko?"
"Wallahi Babah, abubuwan sun zo a wani yanayi."
"Tsarin Allah kenan, wanda yafi na mutum, shekara nawa muna faman jiran wannan ranar, kuma kazo ba tare da sanin mu ba, ka tafi duk bamu san alakar da Ke tsakanin mu ba, idan ba Allah ba,waye ya isa? Shine yake fitar da rayayye daga cikin matacce, ya kuma fitar da matacce daga cikin rayayye, yanzu buri na daya ya rage Muhammad, shine ganin Aminatu."
"Idan na ganta bani da sauran damuwa Muhammad, an cutar da baiwar Allah an chanja mata rayuwa da komai, bamu kyauta ba sam Muhammad, bamu kyauta ba, shiyasa Allah ya saka kayi nisa damu nisan da har muka cire rai da kai."
"Na san inda take Babah."
Da sauri yace
"Ka san inda Aminatu Muhammad?"
"Na sani, suna tare da Maman Yara a gidana."
"Maman Yara?"
"Atika."
"Ta yaya suka hadu da Atika?"
"A Masarauta."
Sai ya bashi labarin komai da yadda sukayi da Madaki da zuwan sa kurkukun da komai da ya samu ta hannun Maman Yara,
"Sai yan biyu da suma suna nan a raye, Safiyya da ta tafi dasu ana tunanin tana Masarautar."
"Da gaske kake Muhammad? Da gaske suna da rai?"
"Suna raye..."
"Tafiya Nigeria ta zama dole a garemu Muhammad, dole mu koma inda muka fito,nasan mutane da yawa zasu ji mamakin dawowar mu, musamman idan muka dirar musu ta inda basuyi zato ba."
Sai ya daga hannun sa Sama
"Ya Allah ina kara Godiya a bisa ni'imomin da kayi min, Alhamdulillah ya Allah."
"Wannan labarin sai mun koma, yadda Gimbiya zata sake shiga farin ciki sosai, yanzu idan aka sanar mata zata daga hankalin ta ne akan tafiyar, ni kuma nafi son muyi komai a tsakane."
"Hakan ma yayi."
"Allah yayi maka albarka Muhammad, hakika Masarautar Saji tayi sarki irin wanda bata taba yi ba, dama Alhaji yana da rai yaga yadda burin sa zai cika."
"Sarki Babah?"
"Tabbas Muhammad, in Sha Allah da hannu na zan nada maka rawanin ka, kai ne ka chanchanta ka dace, ni yanzu nayi girma bana bukatar hayaniyar sarauta, zan huta a gida kai kuma ka kula da komai."
Shiru Sultan yayi yana jin yadda maganar tayi masa nauyi, Sarki fa? Sultan na gidan marayu, wanda su Mah-Mah da Daddy suka tausaya wa rayuwar sa suka tsamo shi suka chanja masa rayuwa, shine yau ake masa albishir da zai zama sarki, me zai ce ne wai? Yana da bakin magana ma kuwa?
Duk maganar da suka cigaba da yi akan sarauta ne, da yadda abubuwan suke wanda be taba tunanin hakan suke ba, sun dau lokaci suna hirar dan har abinci tare suka ci, Safwan ya kirashi, ya daga suka dade suna magana daga karshe sukayi sallama.
Sultan cike yake da zulumin yadda Daddy zasu kwashe da Mah-Mah, sannan yana tsoron har Safwan ya shiga tashin hankali, abubuwan suka hadu sukayi masa yawa shi yasa ma kai tsaye be gaya ma Maimartaba su waye Yan biyun ba ya bari sai sun koma tunda har ma an fara shirye shiryen tafiyar.
Tana kwance a dakin da yafi mata kama da aljannar duniya, ta kudundune a cikin bargo saboda sanyin da take ji, tafiyar Gimbiya kenan daga wajen ta sun dade suna hira itace ma gyara mata kai da kanta suka kuma ci abinci tare. Ita ta kwanta ita kuma ta fita domin kawo mata wata madara daga dakin ta.
Kansa ya fara lekowa ya tabbatar bata ciki, dan idan yazo kora shi Gimbiyar keyi wadda a yanzu Amrah ta saka mata suna Ummi.
Da karfin sa ya shigo ganin bata nan, ya lallaba ya shiga bargon, da sauri ta zabura zata mike, ya saka dukkan hannun sa ya danne ta,
"Wa na kama?" Yayi maganar yana bata fuska.
"Ka daga ni."
"Anki, wai ni kike ma wannan shan kamshin don kinzo wajen Ummi ko?"
"Ni fa ba shan kamshi nake ma ba."
"Menene Toh? Kinsan yadda na shirya ma zuwa kasar nan kuwa?"
"Please ka daga ni wallahi kayi nauyi."
"Anki din, sai Ummi tazo."
"Ummin?" Ta rufe baki cike da mamaki
"Eh ai ba kunyar ta nake ji ba."
"Tab lallai, babu ruwana wallahi."
"Ni da ruwana, an maida mutum marayan karfi da yaji."