← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 108

Sashe 55

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Na sani Sultan, nasan abinda zaka iya da wanda ba zaka iya ba, sai dai na kasa daina ganin laifin ka,kasan saboda me? Saboda ni uwa ce, da bata san komai ba sai son samun lafiyar d'anta."

"Me zanyi ki daina ganin laifi na dan Allah Mah-Mah? Ke uwa ce a gareni, babu kuma wanda zai so fushin mahaifiyar sa."

"Kana so kasan abinda zaka yi na daina ganin laifin ka anan Sultan??"

"Eh..."

"Ka tabbata zaka iya?"

"In Sha Allah zanyi duk abinda kike ce."

Taku tayi kad'an zuwa gaban gadon da Safwan din yake kai, ta taba saman goshin sa tana tuna abinda suka tattauna da yan uwanta, shawarar da suka bata tayi matukar tasiri a zuciyar ta. Juyowa tayi tana fuskantar sultan din sosai.

"Inaso ka fita daga rayuwar mu, kayi nesa da mu ta inda zamu manta da wanzuwar ka a cikin gidan nan, sannan kafin ka tafi, inaso ka sakar ma Safwan Amrah ya aura!

_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )

💙

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥[4/12, 11:04 PM] Maman Maryam: ©® Hafsat Rano
Page 26

Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi da ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan*

*0903 234 5899*
Or
*09033181070

***Da sauri ya dago, yana son ganin ainihin gaskiyar abinda tace din,be yi tunanin abinda zata ce kenan ba. Sosai ya shiga shock har ya rasa me ma zai ce

"Mah-Mah?"

"Abinda nake so kayi kenan, a matsayin rama alkhairi da alkhairi, a matsayin tukwuicin abinda mukayi maka, idan kayi wannan bani da sauran komai a kanka."

Juyawa tayi da nufin barin dakin, sai kuma ta tsaya ta juyo

"Karka manta, kayi alkawarin zaka yi ko menene."

Ta karashe sannan ta fice daga dakin. Bin inda tabi ta fita yayi yana ganin kamar be ji daidai ba, kamar ba abinda Mah-Mah take son fad'a ba kenan, kamar ma ba ainihin Mah-Mah da ya sani bace ba, an chanja ta ne da wata daban ko kuma anyi brainwashing dinta ne.

"Zan iya? Zan iya?" Ya shiga tambayar kansa, sai kuma ya girgixa kai

"No...Ba zan iya ba, aure ba wasan yara bane, aure abu ne me girma da be kamata ayi irin wannan wasan dashi ba."

Ya bawa kansa amsa a fili yana girgiza kansa.

"Amma Safwan fa? Be chanchanci komai ba a wajenka? Ko da hakan shine abu na karshe da zaka aikta?"

Wata zuciyar daga chan bayan kansa ta tunasar dashi

"Toh ita kuma Amrah fa? Baku tunanin rayuwar ta sai Taku? Me take so menene zabin ta? Babu wanda ya damu sai kanku kuka sani?"

Wata zuciyar ta sake haska mishi. Damke hannayen sa yayi a kirjinsa yana jin zafi Sosai, zafin yadda abubuwan suke kasancewa, me yasa abubuwan ke masa kwan gaba kwan baya ne? Ya riga ya gama gane wani abu guda daya, Mah-Mah ta zama selfish woman, babu abinda ta sani take tunani sai Safwan, ba kuma wai Kawai saboda Safwan din ne take masa abubuwa ba, ya lura kamar harda tsanar sa da tayi a yanzu da kuma rashin son ganin sa da bata yi kusa da ita ko Safwan, tana ganin kamar shine ke kara saka Safwan din a halin da yake ciki.
   Sultan mutum ne me matukar zuciya Amma zai wuya kai tsaye ka gane hakan, ya iya danne zuciyar yabi ka a yadda kake so, musamman idan yana mugun ganin mutuncin ka. Dukkanin su basu taba ganin dayan side din sa ba wanda yayi matukar kokari wajen daidaita kansa , saboda inda ya samu kansa da kuma yadda suka karbe shi, shiyasa yayi ma kansa alkawarin zama a karkashin su da bin dukkanin umarnin su, indai be saba wa Mahaliccin sa ba. Sai dai anzo gabar da ya kamata shima a rayuwar sa ya nuna yasa me yake, ya kuma nuna yana da zuciya a kirjin sa. Kuma shima tsayayyen namiji ne. Allah da kansa ya halarta saki amma baya so. Saboda haka, da ba'a daura ba toh tabbas yayi niyyar barma Safwan, amma tunda haka ta faru ba zai zama me butulce ma Allah ba.
  Taku daya yayi ya isa gaban gadon, kallon sa yayi kad'an sannan a hankali yace

"I'm sorry Safwan, I'm so Sorry."

Sai ya juya cikin wani irin taku da be san yana dashi ba, ya fice daga dakin, ya kuma bi ta hanyar da yasan akwai karancin mutane ya bi fice gaba d'aya daga gidan.

***A hankali ta d'aga idon ta, ta kalli matar da suke tare tsawon lokacin nan, ta kuma kalli kofar taga masu tsaron nasu sun dan matsa daga wajen saboda rana. Sai ta dan matsa k'adan jikin ta, ta tallafi kanta ta dora a saman kafarta, sosai take cikin wahala bata komai sai fitar da numfarfashi.

"Zaki iya sanar dani dalilin da yasa kike cikin wajen nan?"

Cikin muryar da kana ji kasan tana jin jiki tace

"Zan iya, ko da hakan na nufin katsewar numfashi na."

"Ina sauraron ki..."

"Sunana Aminatu, ina daya daga cikin hadiman gidan nan a tun zamanin adalin sarki, Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji."

"Aminatu, Kece dama? Duk zaman nan da mukayi tare amma ban taba gane ki ba? Dama tsawon wannan lokacin kina cikin wajen nan, amma babu wanda ya sani?"

"Ina nan tun ranar da abin nan ya faru, tun ranar ko hasken rana basu barni na sake gani ba, me yasa hakan ta faru dani? Me yasa suka kashe min rayuwa tah?"

"Zaki iya bani labarin abinda ya faru?"

"Eh zan iya."

"Madallah." Tace tana gyara mata zaman kan nata.

"Watanni goma sha takwas na dauka ina goyon ciki, cikin da aka saka min shi ba tare da izini na ba, saboda bani da galihu,bani da wanda zai ce dan me, nasha bakar wuya matuka, wanda sai da aka saka min sau uku yana zubewa sannan aka samu ya zauna. Tun ranar da na bar Masarautar ban kuma shigo ta ba, ina chan garin na Lagos inda muke zaune a wani babban gida ni da Yabi da masu yi mana aiki, sai masu duba lafiya ta mutum biyu nurses sai likitan da yake zuwa ko yaushe ya duba ni."

"Cikin hukuncin Allah, na haihu lafiyw, na haifi yara maza biyu tagwaye, girma da lafiyar su ya bawa duk mutanen da muke tare dasu mamaki, sai dai bayan zuwan su duniya da mintunan da basu gaza talatin ba, suka dira a garin bisa umarnin maidakin sarki, su biyu ne, sai dai mutum daya na gane, Babbar amintacciyar baiwar Gimbiya, suna zuwa suka ce an umarce su ne da tafiya da yaran. Hankali na ya tashi,na hau kuka sosai ina rokon su da su bar min yaran duk kuwa da nasan dama za'a yi haka, tun kafin suzo duniya Gimbiya ta fad'a min abinda zai faru duk ranar da suka zo duniya. Sai dai ba abu bane me sauki raba ni da yaran, wanda ban taba sanin ina son su ba sai bayan da suka iso duniya, naji zan iya yin komai akan a bar min su. Na dinga rokon su akan dan Allah karsu tafi dasu, suka nuna min dole ne su tafi dasu saboda umarni ne da basu isa su ketare ba. Ina ji Ina gani suka tafi da yaran. Nayi kuka sosai har sai da naji kamar ido na zai fita daga gurbin sa. A k'asa na durkusa ina kuka sosai, sai na lura da alamun takalma a tsaye a gabana, na daga ido na da sauri. Yana tsaye a gabana, banji shigowar sa ba, ko dan halin da nake ciki ne? Ya karasa matsowa ya tsuguna a gabana yana bina da kallo

"Kina kukan rabuwa da yaran ne?"

Yace yana kallon cikin ido na, da sauri na daga masa kai ina jan numfashi

"Tashi tsaye." Yace min yana matsawa baya. Tashi nayi ya mika min wani k'yalli

"Share hawayen ki."

Karba nayi na share sai dai basu daina zuba ba hawayen. Da hannu yayi wata alama sai gasu sun shigo, Maza ne manya majiya karfi, suka rissina a gaban sa.

"Ku wuce da ita da kakarta, zan biyo bayanku."
Chapter 55 · 0% Book details