← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 108

Sashe 91

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa tayi ta zauna a gefen sa, ya jawo ta sosai ya dora kanta a saman kafad'ar sa, ya shiga sarrafa na'ura me kwakwalwar tana kallo,

"In sha Allah na gama mana arranging komai, har flight ticket na siya, tafiya zamuyi."

"Da wuri haka?"

"Toh me za'a jira umm? Hankali na bazai kwanta ba idan banje ba, ba na kuma so na tafi na barki again, kinga dai abinda ya faru da irin maganganun da mutane sukayi tayi akai, Allah yaso Umma da Abba sun sanni sun san halina da wasu bare bansan abinda xai biyo baya ba."

"Allah ya kaimu."

"Amin ya Allah." Yace yana rufe laptop din, ya dora ta saman bedside drawer, ya jawo ta jikin sa ya tallafi fuskar ta da hannun sa

"Did you missed me?"

Girgiza kai tayi alamar a'ah, da sauri yace

"Da gaske kike?"

"Da gaske." Tayi maganar tana dariya ganin yadda ya zaro ido.

"Ohh na gane, na gane, wayo zaki min ko? toh naji idan ma ke bakiyi missing dina ba nikam nayi, sosai sosai sosai sosososooi...."

Zatayi magana ringing din wayar sa ta katse ta, kamar ya share sai kuma ya dauka, ganin number kasar waje yasa ya mike sosai ya daga da sauri,

"Muhammad!"

"Na'am, barka da dare Hajiya."

"Muhammad ina ka shiga kwana biyu number ka bata shiga, Maimartaba yana cikin wani hali."

"Subhanallahi, me ya samu baban

"Muna asibiti ko motsi bayayi sai numfashi kawai. Suna ta binciken su amma har yanzu basu gano matsalar ba, na rasa yadda zan Muhammad gashi bamu da kowa."

"Ki kwantar da hankalin ki, in Sha Allah zai samu lafiya, nima ina hanya in Sha Allah, ki kwantar da hankalin ki Dan Allah."

"Shikenan Muhammad, Allah ya kawo ka."

"Amin ya Allah."

Zagaye ya shiga yi a dakin cikin tsananin tashin hankali, baya son wani abu ya samu maimairta har sai ya wanke shi, gaskiya tayi halin ta, gefe daya kuma yana so ya rayu da iyayen sa, da yan uwansa zuwa wani lokaci. Rik'e shi Amrah tayi, yayi saurin rungume ta chest dinsa na bugawa

"Babu abinda zai sameshi ko? Zanje na same shi muyi magana ko? Kice min zai samu sauki." Kuka ta saka ta dinga shafa Bayan sa tausayin sa na ratsata

"Babu abinda zai sameshi in Sha Allah." Tace muryar ta na rawa.

"In sha Allah." Shima yabi bakin ta ya fad'a yana daga kansa.

Alwala sukayi, sukazo sukayi nafila suka roka masa lafiya, sun dad'e kafin su kwanta duk kuwa da Sulthan baya jin zai iya runtsawa sai dai bacci barawo ya sace shi. © Hafsat Rano
Page 48

***
Alwala sukayi, sukazo sukayi nafila suka roka masa lafiya, sun dad'e kafin su kwanta duk kuwa da Sultan baya jin zai iya runtsawa sai dai bacci barawo ya sace shi.
  Kiran farko a kunnen sa, ya mike ya fara yin wanka sannan yayi alwala, yazo yayi nafila ya zauna yana karatun Al'Qur'ani har aka kira na biyu, ya rufe ya maida shi ma'ajiyar sa sannan ya matsa gaban gadon ya saka hannu ya shafa gefen fuskar ta, bud'e ido tayi a hankali, yayi mata murmushi.

"Lokacin sallah yayi." Yunkurawa tayi zata tashi ta maida ita.

"Ba'a mikewa haka kai tsaye daga tashi daga bacci."

Komawa tayi, yayi mata murmushi kad'an ya wuce ya sake daura wata alwalar domin ita alwala tana kankare zunubi ne shiyasa baya gajiya da sabun ta ta a ko yaushe, wasu mintuna ta dauka jin ta dawo fully yasa ta mik'e itama, ta mitsitsike idonta sannan ta sauko ta saka bed side slippers din ta nufi wajen wardrobe din ta, hijab ta ciro da doguwar riga ta ajiye a gefen gadon ta shiga tayi alwalar sannan ta fito sukayi jam'i a cikin dakin. Bayan sun idar sukayi azkar sannan ya koma saman gadon ita kuma ta dauki Al'qur'anin ta shiga karantawa a hankali.
   Yana kwance yana tunani bacci ya dauke shi me karfin gaske, ajiye karatun tayi ta cire hijab din ta samu gefen gadon ta kwanta dan idonta a cike yake da baccin itama dan ba wani yin sa tayi sosai ba aka kira sallah.
    Ita ta fara tashi, tayi saurin saukowa daga gadon tana kallon d'an karamin agogon dake gefe.

"Ya Salam!" Ta furta tana mikewa da sauri, goma ce zatayi. A hankali ba tare da tayi wani motsi sosai da zai tashe shi ba ta bar dakin. Kitchen ta nufa duk da har yanzu bata wani jin karfin jikin ta amma zata iya yi musu simple breakfast, ko fried yam and egg sauce ko tea da toasted bread ko dai wani abun. Duddubawa tayi taga abinda ya kamata tayi tayi saurin had'a komai ta gama ta ajiye anan tsakiyar falon ta koma ta dauki hijabin ta, ta saka ta nufi wajen su Maman Yara, a zaune ta tadda su da alama sun jima da tashi, ta russuna ta gaishe su suka amsa cikin girmamawa kamar ko yaushe, ta ajiye kayan a gefe

"Ba dai girki kikayi ba?" Maman Yara tayi maganar tana zaro ido

"Uhum..." Tayi murmushi bata ce komai ba

"Kayya, ke da ba lafiya ce dake ba, ai da bakiyi wahala ba, mu nan kingan mu Yarima ya kawo mana kayan shayi ga flask dinmu da biredi tuni mun sha ma."

"Babu komai." Tace tana mikewa

"Akwai abinda za'a yi miki ne?" Aminatu tayi maganar tana tashi, girgiza kai amrahn tayi da sauri tana tuno abinda Sultan ya fad'a mata akan matar da matsayin ta a wajen Safwan,

"Babu abinda za'a yi Umma, nagode."

"A'ah ko shara ce, ga kwanukan da aka bata jiya da yau duk sai na wanke ai."

"Allah da kin barshi sai na wanke."

"Ko alama, ba zaki wanke ba, akan wanne dalili? Menene amfanin mu toh mu?" Tayi maganar tana kallon Maman Yara

"Gaskiya." Tace

"Karki damu kuje kinji 'yata?"

"Toh." Tace ta fita aminatun tabi bayan ta, tare suka shiga falon ta shiga gyarawa duk da babu komai na datti, ta gama duk da kusan tare ma sukayi da amrahn duk da hanatan da take dan ita nauyin matar take ji sosai, kitchen ta shiga ta wanke kayan tas ta gyara kitchen din komai ya fito neat, sannan ta koma wajen su. Dakin ta, ta koma ta tura a hankali, a zaune ta same shi yayi wanka ya saka kaya yana kokarin saka links a hannun sa.

"My wife."

"Har ka tashi?"

"Shine kika k'i tashi na ko? Kika saka na makara."

"Na zata ba da wuri zaka fita ba ai."

"Kin ga fa a yadda naso tara na bar gidan nan, amma ji har sha daya d wani abu, Allah Allah ni bazan yarda ba." Dariya ta saka ganin yadda yakeyi, shima yayi dariyar ya taso ya riko ta.

"Dariya ko?"

"A ah da gaske ba dariya nake ba."

"Toh mene? Umm?"

"Kawai kawai, umm umm bari nayi wanka."

Da sauri ya sake ta ya matsa baya

"What! Yan yan yan yan, wannan amaryar tawa wace kala ce?"

Kunya taji tayi saurin cewa

"Ai dazu fa nayi shine yanzu zan sakeyi."

"Kai anya? Wannan Amaryar tawa kuwa anya? Anya?"

Kin magana tayi ta wuce toilet din da sauri ta manta ko towel bata dauka ba. Gefen gadon ya koma ya zauna yana kunshe dariyar sa, he can't wait ayi diramar da za'a yi idan ta tashi fitowa. Yana nan zaune, wayar sa a hannun sa yana faman dannawa lokaci lokaci yana kallon kofar toilet din, knocking tayi ya tashi tana ajiye wayar sannan ya nannade hannun rigar sa, ya tsaya a kofar yana rike kugunsa.

"Ya akayi?"

"Please towel zaka bani da hijab dina."

"A nawa?"

"Na'am?"

"Nace a nawa? Kinsan ba'a aikin banza haka nan."

"Pleaseeeee."

"Pleaseeeee nima..." Ya kwaikwayi muryar ta

"Please, please please."

Dauko mata towel din yayi, ya tsaya a kofar yace

"Gashi." Hannu ta zuro zata karba ya dauke, ya sake cewa

"Gashi." Ta kuma miko hannu ya sake daukewa yana dariya

"Bari na shigo na baki." Da sauri ta rufe kofar ta murza key, ya kwashe da dariya sosai

"Allah ke matsoraciya ce ta gaske, bud'e ki karba kiyi sauri I'm hungry."

Budewa tayi ya mika mata, yayi kamar ya bar wajen, maimakon ya bar wajen sai ya hard'e hannayen sa a kirji ya jingina da jikin mirron dakin saitin toilet din, da karfin ta, ta fito a tunanin ta baya dakin, turus tayi ganin mutum a tsaye, tayi kamar ta koma gashi babu damar komawar, kamar munafuka haka ta wuce shi sum sum ta bud'e wardrobe ta dauko kayan da zata saka, ta sake zuwa zata wuce shi ta koma toilet ya sha gaban ta,

"Lemme help you." Ya mika hannu ya karbi kayan, da sauri tasa hannu zata karba ya daga sama

"Don't be stubborn, taimakawa kawai zan."

Kafadarta ya kama ya zaunar da ita a gaban mirron, ya bud'e mata man ya ajiye mata a gabanta, yana kallon yanayin fuskarta ta cikin mudubin kamar kace k'yet ta fita da gudu, murmushi yayi a ransa ya raya

_"Akwai lokaci."_

Rankwafowa yayi saitin kunnen ta,

"Mrs Muhammad Sultan ba dai tsoro ba, anyways za'a yi wani akai, yanzu dai ki shirya a nutse ina jiran ki a falo, kafin ki gama bari naje mu gaisa da su Maman Yara."

Juyawa yayi ya fita, ta sauke ajiyar zuciya tana kankame jikin ta, abubuwa da yawa suka saka take son Sultan, ciki har da wannan bangaren nasa, he's so caring, idan ka ganshi a haka kamar bashi ba, amma idan yana wani abun hmm. Sai kuma wani gefen na zuciyar ta ya tunasar da ita

_"Kiyi addu'a Allah yasa ya dore a haka."_

"In sha Allah." Ta furta a fili sannan ta shiga shiryawar a nutse kamar yadda yace din tana yi tana blushing ita kad'ai.

Ko da ta fito har ya bud'e breakfast din,ya had'a musu tea tana zama sukayi bismillah suka soma ci, har suka gama babu wanda yayi magana sai kallon ta kawai da Sultan din yake ta faman yi yana murmushi. Mikewa yayi, yayi hamdala yace

"Zan fita, take care of yourself, zan iya dawowa late, idan akwai wani abu just give me a call."

"Ok a dawo lafiya."
Chapter 91 · 0% Book details