Sashe 93
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"In sha Allah." Ya amsa a hankali yana hasaso yadda koman zai dawo daidai, yadda rayuwar sa da ta Safwan zata yi juyi zuwa wani bigire na daban, bigiren da basu taba tunani ko hasashen kasancewa a ciki ba, a yanzu yafi tausayin Safwan a kansa, yafi tausayin Muhammad a kansu baki daya, dan kusan shi akafi cuta duk ciki, babu wani isheshen ilimi sai wahalar rayuwa, ta wannan bangaren zai iya cewa su ba karamin gata Allah yayi musu ba, dan da sun taso cikin Masarautar ba lallai su samu ilimin kamar haka ba gaba daya zasu kudundune kansu ne a sha'anin sarauta.
Tafiyar 12hours da yan mintuna ta kai su, kasancewar dukkan su ba bakin k'asar bane yasa kai tsaye suka san abinda ya kamata su yi. Hotel din da Sultan yayi musu booking tun a gida suka wuce kai tsaye, nan yake so su fara sauka kafin su nufi asibitin duk da be riga ya kira Gimbiya ya sanar mata da zuwan nasu ba.
Sai da suka fara wanka suka gabatar da sallolin da suka tsere musu sannan yayi musu ordering abincin cikin hotel din suka ci. Suna gama ci ya mik'e, yace mata zai je ya dawo, kamar tace zata bishi sai kuma ta fasa, ta kwanta tana jin babu dad'i.
Yana fita ya kira wayar gimbiya, bata daga ba da farko, ya riga yasan asibitin da Maimartaban yake zuwa sai kawai ya nufi chan din. Kafin ya karasa ta kira shi back, ya daga yace mata ya kusa karasowa asibitin, murna ta hau yi ta fad'a masa inda suke idan ya shigo sannan ta kashe. Matsawa tayi gaban gadon Maimartaban daya farka tun dazu har ma sukayi magana inda yayi mata maganar da ta yi matukar bata mamaki, maganar da ta dau lokaci me tsawo tana bukatar ji daga bakin shi amma bata taba ji ba, tun zuwan su k'asar.
_"Gida zamu koma gimbiya, zaman mu ya kare anan."_ murmushi tayi data tuna maganar da ya gama yi mata daxu dazun nan, maganar da ta saka ta cikin matukar farin ciki mara misaltuwa, murnar ta, ta kasa boyuwa, ta kuma yi mamakin chanjawar Maimartaban bayan farkawarsa. Abinda ya kara bata mamaki dashi shine yadda gaba daya ya chanja, ya dawo ainihin Maimartabar sa, wanda ta sani a shekarun baya a cikin Masarautar Saji, ba Maimartaban da ta sani a Canada bane, kwayar idon sa kawai ta kalla ta yarda da cewa mulki ba karya gane. Tun bayan yayi mata maganar be sake cewa komai ba, yayi shiru kamar bashi ba.
"Sultan yana hanya." Tace tana tsayawa ta wajen kafarsa, be dago ba kwata-kwata kamar yadda tayi tunani, sai kallon ta da yayi, ya daga mata kai alamar toh, jiki a sanyaye ta koma ta zauna tana mamakin abinda zai sauya mijin nata haka farar daya.
Tsayawa yayi a kofar dakin, ya kurawa dakin ido, kamar an sassara kafarsa haka yaji, ya kasa daga ta, ya ja ta zuwa idan zuciyar sa ke tura shi, ya jima a hakan be san yaya zasu karbe shi ba, be kuma san takamaimai me zai ce musu ba kai tsaye.
_"Nine danku Sultan? Ko me?"_
Girgiza kai yayi, yayi sallama a hankali ya tura kofar, tun kafin kofar ta gama budewa gimbiya taga Maimartaba ya yinkura zai tashi, fuskar sa dauke da wani yanayi me wuyar fassarawa, da sauri ta karasa tayi kokarin taimaka masa amma sai ya dakatar da ita, ya zauna sosai ta saka masa pillow ta saman kansa.
"Sultan!" Ta kira sunan sa ganin ya kasa karasa shigowa
"Shigo ciki mana, kamar bako?"
Da hannu Maimartaba ya yafito shi, ya tafi kamar wanda ake ingizawa, ya isa gabansa, ya kasa daga kai ya kalle shi, yadda kwarjinin sa ya cika wajen ya kara taimakawa sosai wajen yadda Sultan din ya kasa sakewa.
"Babah...!"
"Zo Muhammad." Matsawa yayi sosai, Maimartaba ya kamo hannun sa zai rik'e, yayi saurin sakin hannun ya kurawa hannun ido
"Muhammad ina ka samu zoben nan?"
Kasa Sultan yayi da kansa, yaji kwalla na sake cikowa a idon sa, me zai ce masa?
"Dan Allah ka amsa min Muhammad, ina ka samu zoben nan, har ya kasance a hannun ka?"
Daga masa kai Sultan yayi ya kasa magana, hawayen da yake rikewa,hawayen farin ciki suka shiga gangaro masa.
"Bayan na koma Nigeria, na tafi da alkawarin yin abu biyu, dawo muku da farin cikin ku da kuka rasa wanda nake jin kamar wani hakki ne akai na wanda ya zama dole na cika shi, sai kuma neman iyayena, Wanda wani dalili me karfi ya saka ni bibiyar waye ni? Bansan cewa zaren zai jani ya had'e ni a waje daya bane... "
Abinda ya faru tun tafiyar sa har haduwar su da Maman Yara ya sanar masa, ya dora
"Tace nace maka Azizah ce"
Karkarwa jikin Maimartaba yake, gimbiya kuma da ta dago abubuwa da yawa a zancen ta durkushe a wajen kukan ta na fita a hankali
"Aziza tace maka Sultan? Itace ta kula da kai tun kana karami, har zuwa lokacin da gidan daka taso suka dauke ka? Sunan ta Aziza Sultan?"
"Sunan ta kenan, tace ina fad'a maka zaka gane."
"Alhamdulillah ya Allah, alhamdulillah ya Allah."
Ya ringa maimaitawa ba kakkautawa, hannun sa dake matukar rawa yasa a saman kan Sultan din yace
"Jini ba karya bane Muhammad ,tun da na ganka naji ina sonka, ashe kai din jinina ce, jini na da gimbiya, kai din gudan jinin mu ne da muka fi so fiye da komai a duniya."
"Taimaka min na sakko Sultan, ko yanzu Allah ya dau raina Alhamdulillah, zan wanke kaina a wajen mahaifiyar ka, duk da nasan hakan be isa wanke kan nawa ba, amma zan kwatanta Muhammad."
Taimaka masa Sulthan yayi ya sakko, ya matso gaban ta, ya daga ta tsaye ya kama hannun Sultan ya saka cikin nata
_"Ina cikin jiki na?"_
NoWannan tambayar ita ce tambayar da kika fi yi min fiye da kowacce irin magana ma, yau zan amsa miki Maryama
"Ga d'anmu nan, wanda zalunci ya saka aka so salwantar mana da rayuwar sa, da yake Allah yayi zai taka k'asa, sanadiyar rayuwar sa mutane da yawa zasu amfana dashi yasa Allah ya raya mana shi,ni da kaina na dauke shi na bawa Azizah shi, na kuma umarce ta da tayi nisa da mu, nayi imani idan Allah yayi akwai sauran rayuwar sa a gaba zai dawo da kafarsa, a lokacin da duk wani me sharri ba zai iya aikata masa komai ba."
Bata iya magana ba, tayi saurin rungume shi kukan ta na karuwa sosai, ita kad'ai tasan me take ji a yau, wanne irin hali take ciki, ashe dama zata ga wannan ranar? Amma me yasa Maimartaba be taba fada mata cewa yana raye ba, ba da shi yayi, yayi mata shiru ya bar ta, tana shan wahala tsawon lokaci.
"Kar kiyi tunanin da gayya na raba ki da danki Maryama, banyi hakan dan na kuntata miki ba, sai dan na kare rayuwar mutane da yawa da hakan zata shafa."
"Da ka fad'a min, da komai be baci haka ba, da ka fad'a min da mun yi tunanin abinda ya kamata muyi tare."
"Idan har muna da lokacin hakan kenan? Idan har wanda suke nufin mu da sharrin zasu bamu wannan damar ko?"
"Su waye? Sun isa suyi mana abinda Allah be mana ba?"
Shiru yayi, yanzu ba wannan lokacin bane, da sauran lokaci, da saura. Jin yaki cewa komai ya saka Gimbiya jan hannun Sultan, suka fita daga dakin, girgiza kai Maimartaba yayi wani irin dadi na ratsa shi, yasan idan har ba jin komai tayi ba, ba zata taba fuskantar shi ba, shiyasa ba zai ce mata komai ba, sai ranar da komai zai bayyana, ba tare da wani tunanin ko hakan ne ko ba haka bane, a ranar yasan zuciyar ta zata sake karyewa, amma abun zai zo da sauki. Baya jin wani sauran ciwo, sai wani karfi ma da yaji ya sake zuwar masa, karfin tunkarar azzaluman mutane, maha'inta masu fuska biyu.
Chan wajen wasu kujeru ta ja shi, suka zauna fuskarta ta gaza boye farincikin da take ciki, sunan sa kawai take kira sai kuma tayi shiru ta kasa cewa komai, shi kansa jin sa yake wani daban kamar bashi ba, kamar an chanja shi ne da wani na daban, be taba hasaso wadannan mutanen a matsayin iyayen sa ba. Rayuwar sa ta fara ne daga gidan marayun nan, zuwa tafiya da Daddy yayi dashi inda hakan ya zama sanadin budewar rayuwar sa, har ya zama abinda ya zama har suka ganshi cikin kyakkyawar kama da kyakkyawar tarbiyyar, bashi da kamar Daddy da Mah-Mah dan su din iyaye na nagartattu. Musamman Daddy duk da yasan ko daya cikin shi da Safwan basu da wata alaka dashi amma ya kula da rayuwar su ya inganta musu ita ta yadda kowa zai yi sha'awar su.
Tambayoyi masu yawa gimbiya tayi masa, ya amsa mata yadda yasan zata fahimci komai, yanayin yadda fuskarta ke fad'ad'a da tsantsar farin ciki kad'ai ya ishe shi. Basu san dare yayi sosai ba, har sai da suka ji kiran Maimartaba ta wajen wani ma'aikaci, tashi sukayi suka koma ciki, ya zuba musu Ido da suka shigo yana jin dad'i mara misaltuwa. A tsakiya suka saka Sultan din, suka hana shi yin komai, suka dinga tattalin sa, har yaso mantawa da baiwar Allah dake chan tana jiran dawowar sa. Ko da yace musu zai tafi masauki kin yarda sukayi, Gimbiya ta rikice tana ganin kamar shikenan ya tafi, yayi kokarin fahimtar da ita amma taki sauraren sa, sai ya matsa waje Maimartaba yayi masa magana k'asa k'asa. Shi yayi wa Gimbiya bayani aikuwa ta sake rikicewa tace dole ya je ya tawo mata da Amrah ta ganta, tana so taga matar dan ta. Hakuri ya bata akan gobe da sassafe zasu zo, da k'yar ta yarda duk da haka sai da ta rakashi har waje, ta kuma ta jaddada masa lallai suna sallah su tawo nan, su kuma tattaro kayan su, dan ba zata sake barin su suyi mata nisa ba