Sashe 69
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Amrah tayi bata ce komai ba
"Makociyarki ce anan baya, shine nace bari na shigo mu gaisa kafin ki shisshigo mana."
"Oh Allah sarki, bismillah toh." Ta wuce gaba ita kuma tabi bayan ta, tana satar kallon gidan. Suna shigowa Afrah ta tashi daga kwanciyar da tayi tace
"Bakuwa akayi ne?"
"Eh anan baya take shine ta shigo a gaisa."
"Sannu da zuwa."
"Yawwa sannu, wacece Amaryar ne?"
Karaf Afrah tace
"Nice."
"Toh bakya bace, ai amarya bata nuna kanta."
Dariya suka saka gaba daya, tashi Amrah tayi ta kawo mata ruwa da lemo, ta dawo ta zauna, suka dan cigaba da magana duk da ba sosai Amran ke saka bakin ta ba sai dai tayi dariya kamar kowanne lokaci, Afrah ce ta zage kamar sun saba da matar wadda da alama itama Eh ce indai a magana ce. Ta dad'e sosai dan har aka kusa kiran sallar magriba sannan tayi musu sallama ta tafi.
***Kwance take a saman cinyar ta, kanta da ya sha attachment sosai ya bazo ya rufe saman fuskar ta, ranta a bace yake tun lokacin data samu labarin banzan yarinyar nan ta tare a gidan Sultan, sai da tayi kuka sosai da k'yar Anty Amina ta kwantar mata da hankali amma a k'asan ranta bata jin zata iya hakura da Sulthan, son da take masa bana wasa bane, shine k'adai guy din da komai nasa yayi mata, kuma ita a iyakar rayuwar ta kaf bata san wani abu wai shi babu ba, komai ta nema tana samu har ma da wanda bata nema ba, a haka ta taso babu kuma abinda ya chanja sai ma gaba da yayi dan tayi girman da ko ba'a samar mata abinda take so ba zata samar ma kanta.
Ringing din wayar Anty Amina ya dan dawo da ita daga tunanin da ta tafi, ta cire kanta kad'an tana duban Anty Aminar da ta kara wayar a kunnenta tana magana.
"Kai har kun gama? Amma dai ba wucewa zakiyi ba ko? toh shikenan sai kin shigo."
"Waye zai zo?" Ta tambaya tana tashi zaune
"Wai Yaya Umma (Hajiya Umma) ce tazo wata seminar, na manta shaf munyi magana tace idan ta gama zata shigo sai ta kwana, sai dana ga kiranta wallahi na tuna."
"Wow amma naji dadin zuwan ta... Kwana nawa zatayi.?"
"Basa wuce kwana uku ai suke gamawa, ban dai sani ba amma."
"Ko kwana nawa ne ma dai naji dadin zuwan ta." Tayi tsalle cike da farin ciki, Hajiya Umma was her favourite, tasan abinda zatayi ta samar mata abinda take so no matter how cost, brain dinta was sharp wajen figuring abinda ya kamata shiyasa tasu tazo daya sosai. Irin mutanen nan ce ita no nonsense saboda haka bata ragawa kowa, and she's filthy rich, komai da aji da kud'i take yin sa, kuma bata tsoron spending ko nawa ne ma evil plan dinta.
Tana sauya kayan jikin ta, suka turo dakin tare, da wani irin mugun tsalle ta d'ane ta, suka saka dariya.
"Umaimah bakya girma sam." Tace bayan ta sake ta sun zauna a gefen gadon
"Allah ba zaki gane yadda nayi missing dinki ba, gashi yaushe ma muka rabu, amma dai i need you now more than ever ma, shisa na matsu kuma nakasa boye farinciki na."
"Toh gani,me kika ajiye min?"
Sai ta kalli Anty Amina ta turo baki
"Auw ba za'a yi a gaba na ba kenan?" Tace tana tafa hannu
"Toh dai kinji, magana ce tsakanin uwa da yarta."
"Ai shikenan, idan tayi wari maji."
"Aiko ba tayi warin da zaku ji."
"Shikenan, muje kici abinci idan kika huta sai ki saurari yar taki."
"Idan har zan iya cin wani abu ma kenan, ai sai naji uzurinta tukun."
"Lallai toh sai kun fito."
Ja musu kofar tayi, Umaimah ta kalli Hajiya Umma ta narke sosai, hawayen da take makalewa suka shiga saukowa a saman fuskar ta.
"Ashssha, kuka umaimai? Kuka fa? Lallai ko menene babba ne, waye ya taba min ke?"
"Sultannnnn..." Taja sunan tana sake matsar kwalla.
"Sultan? Wanne Sultan waye shi waye uban sa a garin nan?"
"Sultan fa,na gidan Mah-Mah."
"Mtsw..." Taja dogon tsaki
"Me yayi miki? Ni wallahi wannan yaron sam be min ba, kwata kwata yaron be min ba,da kika ce Sultan ni sam ma na manta da shi da rayuwar sa shiyasa ko kawo shi banyi ba wallah..."
"Wani abun yayi miki hala? An kwaso mana dai jaraba wallahi..."
"Kai Aunt, son sa fa nakeyi ni babu abinda yayi min." Ta tura baki cike da jin haushin abinda tace akan Sultan din. Tafa hannu Hajiya umma ta hau yi tana jera salati
"Mun shiga uku, yanzu kema yaron nan sai da ya lashe mana kurwar ki, Innalillahi amma wannan yaro, chan ana fama da Safwan yaron nan har yanzu be dawo daidai ba, kema kuma yanzu ki bullo da wannan babban zancen bayan na zata zancen wasa ne sanda naji k'ishin-k'ishin da biki."
"Toh wai ma ba yayi aure bane, me zaki ci dashi duk yaran dake kano da Lagos shi kad'ai kika gani kaf?"
"Ni dai wallahi shi kad'ai nake so, kuma na zata zaki taimaka min shiyasa ma na sanar dake, shikenan zan nema wa kaina mafita tunda babu wanda zai fuskance ni, ai nima yanzu nayi girman da zan iya maganin matsalata."
Sai ta tashi da sauri zata bar dakin, hannun ta Hajiya Umma ta riko ta dawo da ita ta zaunar tana kokarin saita kanta
"Ba haka bane shalele, ki gane shi fa yaron nan babu wanda yasan asalin sa, ba'a ma san daga wacce nahiya ya taho ba, da zaki duba dai ko a cikin family ne, sai na shige miki gaba ayi komai..."
"Allah ni shi kad'ai nake so, bana son kowa kuma ban damu ba ko daga sama ya fado, tunda mutum ne ba aljani ba ina sonshi a haka."
"Trkashi..." Tace tana rike habar ta
"Amma Umaimah...."
"Shikenan,tunda babu wanda zai taimaka min, shikenan, amma duk abinda nayi kar azo daga baya ace min dan me."
Ta juya mata baya tana harare harare, Tashi tayi ta dawo bangaren data juya ta kama hannun ta ta rike a cikin nata fuskar ta dauke da murmushi tace
"Zan taimaka miki,if that's what you want, duk da bana son yaron nan sam,amma zanyi kokarin ganin na soshi saboda ke, zai zo da kansa neman aurenki, I promise you that."
"Da gaske kike? Dan Allah da gaske?"
"Na taba miki wasa ko na miki alkawari ban cika ba? Wait and see, sai dai bana so kiyi komai, ko kiyi taking wani foolish decision, ki jira ki gani kawai."
"I love you, I love you so much, you are the best." Ta rukunkumeta tana kyalkyala dariya.
***Bayan su kawai yake iya gani, suna zaune suna magana daga gani kuma maganar da sukeyi me muhimmanci ce, amma shi maganar su ba damuwar sa bace, yazo ne akan maganar Ammin su, Alhajin yayi shiru be ce komai ba, ya ajiye su kawai ba wani bayani gashi ganin sa akwai wahala, anan ne kad'ai kake samun ganin sa freely shiyasa kawai yazo dan sun fara gajiya da ajiye sun da yayi. Ya kusa kaiwa inda suke yaji suna maganar da ta firgita shi, ya tsaya tsak yana jin duk abinda suke cewa, tsoron sa ya karu lokacin da mutanen da suke tare da Alhaji Safiyanu Madaki suka mike domin tafiya, wasu irin mutane ne marasa kyaun gani, kana ganin su kaga rashin imani a tattare dasu, da sauri Muhammad yayi k'asa da kansa yadda ba zasu iya ganin sa ba har suka wuce. Maimakon yayi abinda ya kawo shi sai ya samu kansa da bin bayan su da sauri har yana kokarin faduwa.
***Shafa'i da wutri tayi, ta kwanta a saman abun sallar wayar ta na gefen ta, tunanin shi take tana ayyana kalar girman abinda zai sashi irin wannan tafiyar rana daya tak da tarewar ta, tasan yadda Sultan yake son ta sosai, tasan kuma bashi da wani wajen da zai je bayan gidan su. Lallai akwai wani babban al'amari da ya saka shi yin komai, zata cigaba da tayashi addu'a Allah ya taimaka masa ya bashi nasarar komene yaje nema. Har wajen sha biyu tana kwance akan sallayar da yake akwai wuta, jin tana jin bacci ya saka ta tashi tayi nafila raka'ah biyu, ta dad'e a sujjada tana rokan Allah akan auren su da kuma ahinda ya sako mijin nata a gaba, sai da taji da gaske har cikin zuciyar ta tayi addu'a sosai sannan ta hakura, ta ninke sallayar ta dora ta saman bedside drawer ta cire hijab din ta ajiye, kallon Afrah da tayi d'aid'ai a saman gadon iska na hurata tayi, ta dan yi dariyar kwanciyar ta ta, ta cinye fiye da rabin gadon ko da kwanciya zatayi sai dai ta rabe ta gefen ta. Dakin ta fita ta rufo mata kofa kai tsaye ta wuce dayan d'akin. Tana shiga ta kunna hasken dakin, kamshin turaren sa tun ranar da ya tafi yaki barin dakin, gadon ta kalla da ido tana tuna komai, ta taka a hankali ta isa gaban gadon, ta tsuguna akan guiwar ta tana dora kanta a saman gadon. She's badly missing him, fiye da tunanin me tunani. Kamar da wasa taji wayar ta na vibration, ta cire kanta ta duba, sunan wanda bata yi zato ko tsammani bane,duk da tunanin sa da take a lokacin amma bata yi tunanin ganin kiran sa ba, a irin wannan lokacin kuma. Da sauri ta d'aga zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri. Shiru tayi tana jin yadda ya ke sauke ajiyar zuciya da karfi.
"My wife..." Ya kirata yana jin wani bangare na damuwar sa na melting,
"Please talk to me, ko fushi kike dani?"
"Um um..." Tace
"I'm very sorry, very sorry."
"Kana ina?" Tace sounding so worried
"Gani nan ne Amrah, bansan inda nake ba, ban masan me yake shirin faruwa dani ba, kawai addu'a nake bukata,I'm very weak, abinda nake nema da na rasa tsawon lokaci na sameshi yanzu amma cike yake da sark'akiya, da zubar jinin bayin Allah. Kiyi min addu'a kinji, adduar ki kad'ai ce yanzu domin ke kad'ai nake da."
"In Sha Allah babu abinda zai faru."
"Amin..."