← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 108

Sashe 106

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya dakin ya sake yin shiru, Jijiyoyin kan Sultan suka sake fitowa sosai suka yi manya manya dasu, yadda yake ji a ransa zai iya yin komai ga duk wanda yake da hannu a ciki, duk kuwa da har da kakan su da wan mahaifiyar su amma be damu ba, dole ne su fuskanci hukuncin abinda sukayi.
   Duk wani wanda yake da abin fad'a ya fad'a, tun daga kan Maimartaba, Ummi, Sarki Bello, Maman Yara, Madaki, Safiya da kuma sauran manyan Masarautar, masu jin kunya, sun ji duk kuwa da ance kunyar mara kunya asàara. Amma basu nuna nadamar su sosai akan abinda sukayi ba. Sultan da tunda aka fara magana be tanka ba, yana bin komai a nutse duk kuwa da zuciyar shi ba a nutsen take ba, a chunkushe take da abubuwan da suka dinga fitowa daga bakunan mutanen, da kuma yadda yasa aka fito da mutane daga kurkukun wasu tun farkon hawa mulkin Sarki Bello suke ciki, duk sun chanja kamanni saboda azabtarwa, a take ya ce duk ya yafe musu ko menene sukayi ya kuma umarci a fitar da wasu kudade mas yawan gaske a basu.
    Daga nan ya bada umarni aka tattare su Buzu da jama'ar sa da duk wani me hannu a ciki, aka zuba su a kurkukun zuwa ranar da za'a yi nadin  na sosai daga nan sai asan abinda ya kamata ayi dasu,da haka ne aka karkare zaman.
    A sabon bangaren da sarki Bello ya gina kwanan na da nufin komawar sa idan ya karbi mulkinsa a hannu Yarima Bilal Sultan da Amrah suka tare, katon waje ne gini irin na zamani wanda akayi shi a cikin kwanaki kad'an, aka kuma kawata shi da duk sani abun more rayuwa, su Safwan da Muhammad kuwa da su Maimartaba suma shashe guda aka ware musu, kowa da part din sa, aka kuma nemar wa Maman Yara, Safiyya da Aminatu suma nasu part din.
    Yar shara ce a jikin Sultan sai dogon wando,ya cire manyan kayan wanda ya gama korafin zafi su Gimbiya suna masa dariya, Safwan ne ya taso ya dawo kusa dashi ya riko hannun sa sukayi wa juna murmushi,sai kuma ya daki damtsen hannun sa bayan ya dunkule nasa hannun, rike masa hannun Sultan yayi da karfi yace

"Sarkin kake rik'ewa haka?"

"Matsoracin sarkin?"

Maimartaba ya fad'a cike da tsokana.

"Yarona ba matsoraci bane, maganar sa kad'ai ta isa ka gane za'a yi gagarumin Sarki."

"Kai dai kina tare masa ne, tsoron rawani fa yake yi."

"Zai daina ne, ko son?"

"Nama daina Ummi nah."

"That's my boy." Sai ta juya wajen Muhammad da yake murmushi kawai tace

"Baka ce komai ba Son."

"Shi ai baya son magana Ummi, shi har yafi Maimartaba Sultan rashin son magana."

A cewar Safwan yana rik'e still da hannun Sultan din shima kuma yana rik'e da nashin, yadda ya fad'i Maimartaba Sultan din ya saka su darawa baki daya, wai Sultan ne Maimartaba, gimtse fuska yayi ya kaiwa Safwan din duka da dayan hannun

"Ka raina sarki, zansa a baka horo me tsananin."

"Tuba nake Ranka Ya Dade." Ya makale hannun sa irin yadda ake wa sarakuna. Murd'e shi Sultan ya shiga ihu, da sauri Ummi ta taso ta rik'e shi, duk suka saka dariya

"Wai Ummi wa kika fi so ne?" Sultan yayi maganar yana zama a gefen Amrah da take murmushi,

"Dukkan ku ina so."

"Naga kamar kinfi son yan dunkurman nan."

"Suwa?"

"Gasu nan, basa magana sai murmushi kawai." Ya nuna Muhammad da Amrah

"Kar a damar mun my little Son, shi da yarinya ta babu ruwan su da hayaniya, ko dai da kuka saba sai kuyi tayi."

"Shiyasa nace kin fi son su Allah."

"Bar rantsuwaa, tafi son sun."

"Sharri dai kawai za'a min kawai."

"Ni kuma waye me sona? Babu farin jini wayyo ni Safwan."

"Kaine na gaban goshin ai." Ummi ta yi maganar cike da nishadi, haka sukayi ta hira suna tsokanar juna har sai da suka saka Muhammad da Amrah maganar da gaske.

***Suna zaune a masaukin da aka sauke su, hawayen ta yaki tsayawa babu irin bakin da Daddy be yi amfani dashi ba wajen lallashin ta amma taki , tashi yayi bayan ya bata hakuri ya fito ya bar mata dakin. Yana zama Safwan ya shigo, ya zauna a gefen sa yana kallon kofar dakin

"Daddy kuka take har yanzu?"

"Eh wallahi."

"Bari naje." Ya tashi ya shiga ciki, ta juyo ta kalle shi ya karaso ciki,

"Safwan?"

"Mah-Mah dan Allah ki daina kukan nan, kar ya jawo miki wata matsala."

"Dole ne nayi kuka Safwan, amma ba wai kukan wani abu nake ba, kukan rabuwa da kai ne, yadda naga Masarautar da yadda naga Maimartaba yana magana na tabbata suna bukatar ku dukka a kusa dasu, saboda ku karbi komai na sha'anin mulkin, zuciya ta, ta gaza daukar hakan, gani nake kamar mafarki nake Safwan, gashi naki na farka balle na gane mafarkin ne ko kuwa gaskiya?"

"Gaskiya ne Mah-Mah, haka Allah ya tsara ya kaddara, amma kuma ba hakan na nufin kin rasa ni ba, ina tare daku a koda yaushe, babu inda zai je na barki."

"Kayi alk'awari?".

"Nayi alk'awari, zan kasance da kowannen ku a duk lokacin da kuka bukace ni."

"Nagode Safwan, nagode."

Goge mata hawayen yayi, yayi mata murmushi tausayin kansu shi da ita na kamashi, yasan ba abu ne me sauki ba shi kansa a wajen sa balle ita.
  A dakin ya zauna suka cigaba da hira dan duk son ta kwantar da hankalin ta, ya samu kuma ta kwantar din har ma ta sake kamar babu abinda ya faru.

***Ranar da aka shirya domin yin nadi na musamman wanda ya kasance gagarumin taro ne Maimartaba ya shirya Masarautar ta dinke taf, babu masaka tsinke, tambura ne da ganguna ke tashi ta ko ina. Manya manyan baki ne daga kowanne lungu ke ta shigowa duk dan taya Maimartaba din murna, zuwan Maigirma gwamna ya saka aka shiga taron kai tsaye, akayi komai a tsari aka nada Muhammad SULTAN a matsayin sabon sarki officially, aka bashi kyaututtuka masu yawan gaske, akayi hotuna, abun gwanin ban sha'awa.
    Babu abinda ya kara kayatar da mutane kamar jawabin da Sultan din yayi me cike da ma'ana. Hajiya kakar su Amrah da yan uwansu duk sun zo tunda labarin ya bazu ko Ina, jikin Hajiya har rawa yake saboda tsabar murna bakin ta ya gaza rufuwa duk wanda ta gani sai tace masa ai Sulthan din mijin jikar ta ne, Afrah tayi ta mata dariya tana fad'a mata maganganu amma tayi mirsisi ta shafe idon ta da toka tace bata san tayi duk abinda Amrah take cewa ba, soke-soken ta ne kawai amma kam ita ta samu wajen zama dan dole Sultan ya nema mata wajen zama a Masarautar dan ba ta ba komawa gida tazo kenan. Kiri kiri ta nuna son zuciyar ta a fili, girgiza kai kawai umma tayi tana mamakin halin mutane wato dai wanda yake dashi yanzu shine mutum, mulki, kudi sune komai idan ka same su ka gama.

   Labarin da ya iske su Umaimah ya saka ta shiga tashin hankali, Hajiya Umma da kanta ta kira Anty amina ta sanar mata komai,jikin ta sai rawa yake wai Sultan din da ta raina ta tsana shine yanzu ta zama Sarki, Sarki me mai daraja ba wai kowanne irin Sarki ba. Suna gama wayar Umaimah ta kirata ta saka mata kuka, ita ce ta hanata aiwatar da abinda tayi niyya tace zata yi wani abu, gashi nan tana ji tana gani Sultan din yayi mata nisa, nisa irin na tsakanin sama da k'asa, tasan yanzu ko ganin sa bata isa tayi haka kawai ba. Sosai itama Hajiya Umman tayi dana sanin rashin yin abinda ya dace din, ta bari kiyayyar da take masa tayi tasiri a kanta, da tuni Umaiman ce zata shiga gidan Sarautar yanzu, ko babu komai zata ce yarsu na auren Sarki, darajar su zata dagu sosai. Da k'yar ta tattaushe ta, ta bata hakuri tace zata san me zatayi, ta samu ta ajiye wayar ta ma kashe ta baki daya dan tasan Umaiman zata iya sake kira ta tayar mata da hankali bayan ita kanta dana sanin abinda tayi ma SULTAN din kawai take yi, tana jin da za'a koma baya da babu abinda zai hana ta jashi jiki ta nuna masa kulawa. Cizon yatsan ta, ta dinga yi tana dana sani wadda aka ce k'eya ce, wanda yayi gaba yayi gaba ita da Sultan sai dai hange daga nesa ko kuma ta ganshi a telbijin idan ana wani taron.

***Bayan taron ya watse, kowa ya kama kansa, anan ne Sultan ya shigo shashen Ummin inda dukka bakin suke ciki harda yan uwan Ummin da be sansu ba, dasu Umma da Hajiya da dai duk jama'ar su na bangaren Gimbiya Amrah da wasu kuma matan abokan Maimartaban ne da yayan su. Tare yake da fadawa suna kare shi, ya gaggaisa dasu fuskar sa kusan rabi a lullube da rawani, kasa hakuri Hajiya tayi ta taso tayi wajen sa fadawa suka dakatar da ita bayan wani ciki ya daka mata tsawar da ta kusan zata sakin kashi a wando. Da hannu Sultan ya dakatar dashi, ya janye abinda ya rufe masa fuskar ya dan duka kad'an fuskar sa babu yabo babu fallasa yace

"Sannu da zuwa Hajiya."

"Sannu Sultan, yaron kirki, Allah ya sanya alkhairi Allah ya tayaka riko, Allah ya sa ka gama lafiya Allah ya..."

Dakatar da ita suka sake yi, tayi saurin yin shiru kamar ruwa ya cinye ta, murmushi Sultan yayi ya juya suka take masa baya suka fice daga shashen.
   Kai tsaye shashen sa ya nufa, ya shiga ya umarce su su barshi shi kad'ai, suka dawo bakin wajen suka tsaya kamar masifa, yana shiga ya fad'a saman gado.

"Wash Allah nah." Sai kuma ya tashi da sauri
Chapter 106 · 0% Book details