Sashe 17
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥[3/16, 7:39 AM] Maman Maryam: *SULE BAYA TARE TA SAI TA WUCE*
*NANA HAFSAAT*
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE! KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SAYA DA KUDIN KI, KADA KI SHARING, TEMAKA KI SIYA NAKI A NAMBOBIN MU DAKE KASA*
*All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. *
*(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾*
*XII*
*KANO STATE*
**Abin ka da rashin sabo ga kauyanci da yake dawainiya dani, tunda muka fara tafiya ina kalle-kalle har bacci ya dauke ni. Ban farka ba sai da aka shigo garin kano, na gane mun shigo ne ta hanyar kokarin da nayi na karanta symbol da aka rubuta *'Welcome to kano'*. Na gyara zama ina ta kalle-kallen abubuwa na burgewa dake kan titi, ga tituna lafiyayyu babu ramuka, hakika birni lafiya ce.
Yadda kwaryar birnin kano ta cika shine zai tabbatar maka da cewa wani abun ake yi mai matukar muhimmanci, saboda din bin mutane ta ko'ina ba masa tsinke. Na kasa yin shiru tun ina lekawa ta glass din window har nace da drive ya zuge min na dinga lekawa kafin na tambaye shi me ake yi yace min.
“Mantawa nayi da wannan na’din (turbaning ceremony) da bamu biyo ta wannan hanyar ba, wallahi wani matashin saurayi za'a nada sarki, shi yasa kowa ya fito ya ganewa idanunsa ba sai an bashi labari ba, gashi nan duk an cika mana garin.”
Cikin mamaki nace.
“Kai..! Sarki fa kace?”
“Kwarai kuwa, ke ba kiji bushebushen abin sarauta ba?”
“Walle banji ba kadan-kadan dai kamar ake yi, dan Allah ka kai ni na gano na din.”
Ya yi saurin cewa.
“Kai..! Yo kafin mu kutsa cikin mutanan nan ai aiki ne, ballantana kuma karasawa wajan rumfar nadin. Kiyi hakuri wata rana zaki ganshi idan ya fito koda sallah ne.” Na jijjiga kai alamar na gamsu.
Bandamu da ganin saba dama mu kai wucewar mu gidah, Na san dai irin nad’in sarauta ne kamar na kauyen mu, Lokacin da aka nada sabon hakimin Alfundi, Bazan mantaba har can muka tafi a kasa. Ganowa idanun mu sabon hakimi da yazo daga birni, Sannan mai unguwa jamilu ma sanda mahaifin sa ya rasu aka nada shi haka akaita bushe bushe algaitu a karakar mu. Muna tafe akan titi ina karanta signboards din kan hanya, Kai birni da girma take, Na bawa idanu na hakkin su sosai, Kafin mu karasa gida
*DR ISMA’EL MUHAMNAD SINGA RESIDENCE*
Kai tsaye wata unguwa naga mun nufa mai matukar tsari, gine-gine ne wannan yana cewa d'an uwansa bani guri. Dr Isma'il Muhammad singa resident nan ne inda drivern ya shiga, ya yi horn a kofar wani katafaran gate wanda ya amsa sunan sa, mai gadi ya bude muka shiga.
Compound d'in kadai abin kallo ne yadda aka kawata harabar gidan da shuke-shuke na burgewa, ga manya da kananun motoci tamkar kamfanin su aka zo kala kusan shida. Baki na saki ina kallon aljannar duniya, ina mamakin wai dama muna da wani dan uwa mai dukiyar da zai iya yin wannan muhallin, amman aka barmu a kauye muna ta shirme. Muryar driver ne ya katse min tsantsar mamakin da ya addabi kwakwalwa ta inda yace.
“Muje cikin gidan.”
Ya yi gaba ina bin bayan shi kamar wata jelarsa. A bakin wata rantsatsiyar kofa muka tsaya, naga yasa yatsan sa tare da danna wani abu ya yi kara, ba dadewa muka ga an bude kofar.
“Yauwa shiga da bakuwar wajan Mami.”
Drivern ya yiwa wadda ta bude kofar maganar wacce yar aiki ce a cikin gidan. Tunda na saka kafata a ciki naji wani sanyi yana bude kayan jiki na ya na shiga cikin tsoka ta, ta matse jiki ina sake kundundinewa dan ban saba jin irin sa ba. Katon parlor tamkar a film din indiyawa, mai dauke da kujeru da suka sake kayata shi, tare da talabijin kamar mutanan ciki zasu fito waje saboda tsabar girmanta. Bene ta hau ni kuma na tsaya ina kallon yadda take hawa da sauri da sauri bama ta tsoron fadowa ita, sai da ta haye sannan ta juyo taganni tsaye ina hangenta tace.
“Taho mana muje.”
Cikin zaro ido nace.
“Ni..!?”
“Eh mana da wa nake yiwa maganar.?”
Na hadiyi miyau tare da sunkuyar da kai kasa, da alama yar uwar su ce ganin tana da fadin rai.
“Ni dai bazan iya ba.”
“Ba zaki iya mene ba?”
“Hawa inda kike so nazo.”
“Oh so kike nazo na goya ki na doroki ne?”
Nayi saurin girgiza kai nufin a'a amman har lokacin banji zan iya hawa ba saboda tsananin tsoro. Ta juya a fusace tana masifa tamkar wacce na yi mata mugun laifi, ni kuma tsakani da Allah ji nayi ba zan iya hawa ba, ina ganin tamkar zan gangaro saboda santsin tiles da yake ta sheki. Ina tsaye sai gata sun fito da matar gidan wacce naji suna kira da Mami, ta kalleni tare da cewa.
“Dije hawo mana.”
Na hadiyi kakkauran miyau saboda shiga tashin hankalin yadda zan iya hawa benan.
“Ba zan iya ba wallahi.” Nayi magana a sanyaye.
“Okay Jummai jeki riko mata hannunta.”
Ta taho tana zuba min harara ta rike min hannun dama na, ya yin da ni kuma na rike karfen binan da hannun hagu muna hawa da kyar.
“Ki saki jikin ki Dije babu abin da zaki ji.”
Cewar Mami, haka na hau ina rike da Jummai wace ke ta faman yi min dariya kasakasa. Ina hayewa kuwa na zauna ina sauke numfashi da kyar. Mami ta riko hannu na muka karasa parlorn tana ta dariya itama ganin yadda nake ta kallon tsarin parlorn ya matukar firgita ni dan yaci uban na kasa komai da komai. Muna nan zaune sai muka ji muryar mutane suna hawowa benan da gudu ko tsoro basa ji. Yan mata ne su biyu sanye cikin dogayen riguna na larabawa, sunyi kyau a ciki ba karya, suna shigowa suka haye kan cinyar Mami suna furta.
“Wassh Mami mun gaji.” Tace dasu.
“Gajiyar ce ta hanaku ganin bakuwa ko?”
Duk sai suka tashi suna kallo na a tare, na yi saurin sunkuyar da kai na ina wasa da mayafin jikina.
“Dije ko?!”
Suka yi maganar cikin alamun tambaya suna sake kallon Mami, ta gyada musu kai tana murmushi.
“Ayya! Allah sarki Dije, ya hakurin Baffan ki.?”
Hawayen da yake shirin zubo min sukai saurin komawa saboda bana son zubar su, Dara'ifa tace min kuka na azaba zai karawa iyayen nawa, addu'a zan dinga yi musu, nace dasu.
“Alhamdulillahi na gode.”
“Haba Dije meye na godiya, munso zuwa gaisuwa Allah be yi ba. Sai kuma Daddy yace ai dakko ki zai yi gabaki d'aya ki dawo nan gida. Welcome Khadija, munyi farin cikin zuwan ki cikin mu kinji?”
Daya daga cikin su tayi maganar cikin nuna kulawa, ta kare maganar da cewa.
“Ni suna na Hameedah, nice babba a gidan nan. Sai sister dina wato Shukrah yar auta kenan. Ba tare aka haife mu ba, na bata shekaru biyu amman kinga kan mu ɗaya saboda tsahon kafa gare ta.”
Duk aka yi dariya yayin da ni kuma murmushi na saki dan ji nake wata iri da ni. Duk baki na da rashin kunya ta ji nayi ina mugun shakkar mutanan gidan. Gashi dai basu nuna min kyama ba, suna nuna kulawa a gare ni. Amman a lokacin na kasa sakin ciki kamar wacce aka yiwa ture na rashin walwala. Daga nan Mami tace su tafi dani dakin su nayi wanka nazo naci abinci. Shukrah itace ta kama ni muka nufi dakin su, a nan naga aljannar duniya, wato yaran yan gata ne na bugawa a jarida. Komai na cikin dakin guda biyu ne kuma cikin tsari ta yadda tsarin ya kawata dakin matuka.
“Toh Dije ga toilet nan ki shiga, akwai ruwan zafi a heater.”
Ban san mene heater d'in ba kuma ban tambaye ta ba, haka na ajiye carbin hannuna dama na Baffa ne na dauka domin ya zame min madubi da zan dinga gani ina tunawa da shi a zahirance. Na bude kofar da suka nuna min sai dai na kasa shiga dan banga ya yi min alamar cewar bandaki bane.
“Dije shiga mana.”
Tamkar wacce zata saki kuka haka nayi magana.
“Banga bandakin ba ai.”
“Ikon Allah, gaki nan a kusa da kofar kin bude.”
“Daki ne fa.”
Ai sai kawai naji sun kwashe da dariya abin ya bani haushi na dawo na zauna akan wata kujera da na gani a cikin dakin ina ta turo baki, Hameedah ta juyo tana kallo na tace.
“Bandaki ne wallahi Dije, ya za'ai mu kai ki daki muce kiyi wanka a ciki? Zo ki gani na nuna miki.”
Ta shiga sannan na bi bayanta, Shukrah na daga bakin gado tana ta dariya ta kasa yin shiru saboda keta. Hameedah ta kunna wani guri ruwa ya zubo cikin wani abu mai dan zurfi da kuma tsaho da alama ruwa ake tana da a cikin sa, naji tana cewa.
“Idan ya kusa cika sai ki kashe nan wajan zaki ga ruwa ya dena zuba, sannan sai ki cire kayanki ki shiga cikin ruwan nan kiyi wankan. Ga sabulu nan da soso kiyi amfani dashi.”
“Jakar uban can kayyasa! Cikin wannan uban ruwan zan shiga sai kace wata kifi ko kwad'on ruwa?”
Dukan su kuma sakin dariyar suka yi, dan ita Shukrah har da hawayen ta tsabar dariya. Na kallesu cike da jin haushi ina turo baki tare yin gunguni ina zagin su a rai na. Meye na dariya bayan maganar gaskiya na fada, banda rainin hankali su kawo guri harda madubi da mayuka shegen jarkokin da malama Mardiyya take matsowa ta shafa shine zasu ci min toilet ne? Hameedah ta fita ta kira Mami suka taho tare.
“Kinga kira ni kina ta faman dariya menene wai?”
“Mami wallahi Dije dai taki shiga cikin toilet wai daki ne, kuma ta ya zata shiga cikin ruwa kamar wata kifanya ko kwaduwa.”
Itama Mami sai ta saki bakin tana rike habarta idanunta a kai na take cewa.