Sashe 37
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wannan damuwar dake kan fuskar ka ba damuwar karatu bace, damuwa ce irin ta wanda ya rasa wani abu muhimmi a gareshi, me yake damun ka?"
Me zai ce? Ya shiga tunani, babu abu daya a labarin sa da zai taimaka wa Baban Idan yaji, haka kuma babu wani abu da zai iya yi masa, ba kuma yason fad'an abinda zai sa a ga laifin Mah-Mah ko Safwan balle har a fadi wani abu mara dadi akansu, sai ya girgiza kai
"Babu komai Baba, karatun ne wallahi akwai wahala, amma yanzu tunda na gama nasan komai zai tafi yadda ya kamata."
"Toh Allah ya bada sa'a, gashi zaka gudu ka barmu, Gimbiya ba zata ji dadi ba, idan ta fito karka fad'a mata maganar tafiyar, ka barni zan mata bayani daga baya."
"In sha Allah, dama Baba nace idan babu damuwa ina so naji karshen labarin ku, idan yaso sai naga ko akwai abinda xan iya akai Idan na koma."
Da sauri yace
"Kul Muhammadu, karka soma saka kanka a sha'anin nan, ni kaina babu abinda zan iya akai dan da zan iya wani abu da baka ganni anan ba, hatsabibancin mutanen cikin masarautar nan yana da yawa, na roke ka karka shiga abinda zai zamar maka matsala."
"Babu abinda zanyi Babah, kawai da wai na zata ko zan iya wani abu akai ne shiyasa.'
Murmushi me ciwo yayi sannan ya kamo hannun sa ya nuna masa wani tangameman hoto dake makale a saman falon,be taba lura da hoton ba sai a lokacin, tashi yayi ya isa wajen hoton ya tsaya yana kare masa kallo, mutum biyu ya gane a cikin hoton sai ya dawo ya zauna kusa da baban yana masa kallon son jin karin bayani
"Labarin da Maruama ta baka ba komai bane akan wanda zai sanar dakai a yanzu, anan zaka tantance abinda nake fad'a maka, labarin cike yake da sark'akiya wadda duk iyakar hasashen ka ba zaka hasaso wanda yake mana zagon k'asa ba."
Nannade kafar sa yayi ya tankwashe ta, ya jingina da jikin kujerar yana bawa Baban dukkan attention din da yasan yana dashi dan da gaske akwai wani abu me kamar maganad'isu da yake fusgarsa akan labarin nasu.
(Idan kun shirya, mu waiwaya mu shiga Masarautar Saji muyi wani abu da ake cewa waiwaye adon tafiya, karku manta akwai zaren labarin mu da muka ajiye a baya, kowa ya dauko shi domin had'e shi.)
***A hankali karatun suratul Al-Khaf ke tashi a dakin, daga chan gefe yana sanye da short da singlet ya hargitsa dakin baki daya yana gyara tun bayan da ya samu labarin dawowar su sati me zuwa, shiyasa tun yanzu ya soma gyara dakin dan gaba daya komai aka fitar na dakin aka yi sabon fenti me kyau, aka sauya komai hatta curtains da komai na dakin, yana aikin yana bin karatun a hankali yana jin dadin yanayin, Mubarak ne ya shigo kasancewar jum'ah ce a shirye cikin shigar farar shadda kafad'ar sa rataye da sallaya, da mamaki ya dubi Safwan din
"Wai karfe nawa ne?" Yace tun kafin Mubarak din ya samu damar yin korafi, agogon hannun sa ya saito daidai fuskar sa, da sauri Safwan din ya dafe bakin sa, sai ya ajiye abinda ke hannun sa yayi saurin zarar towel yayi hanyar toilet
"Wallahi bansan lokaci yaja haka ba, two min bari na watsa dan Allah."
"Kayi sauri toh." Yace masa ya zauna yana kare kallon dakin. A gurguje yayi wankan ya fito ya shirya cikin manyan kayan shima suka fita. Sun ci sa'a sun samu complete raka'oin sai bayan da aka gama aka watse sannan suka nufi gidan Hajiya.
Da fara'ar ta, ta karbe su tana tsokanar ga angon ta ga angon ta, sunne kai kawai Safwan yake dadi fal ransa suka gaishe ta, sannan aka gabatar musu da tuwon shinkafa miyar taushe da ya zama al'adar gidan Hajiyan tun suna yara duk jum'ah tuwon ake suzo suci suna santi, hakan ce ta kasance yau ma, bayan sunci sun koshi sannan suka taba hira zuwa la'asar sukayi mata sallama suka tafi bayan sun ajiye mata kudi.
Satin nan Safwan jinsa yake kamar shekara, kullum da sabon abinda xai yi na shiryawa ranar, sababbin dinkuna yayi musu shida Sultan din iri day kala biyar, ya had'a musu da takalma da set din turarukan da yasan Sultan din na so, komai ya zama ready ranar kawai yake jira, ranar da zata zamar masa daban da sauran ranaku, ranar da zasu sake haduwa da ita bayan tsawon lokaci, yasan akwai abubuwa da yawa dangane da ita da basa bayyana a hotunan ta da yake gani, he's eager to see her, irin eagerness din nan da mutum shi kad'ai yasan yadda yake ji.
Gidan su Amrah ma yasha gyara sosai, dama yan haya aka saka a ciki da zasu dawo aka tashe su aka gyara shi tare da sauya komai na gidan hatta da Windows duk sai da aka sauya su. Sai gidan ya dawo sabo fil sai jiran masu gidan kawai.
Ranar da sassafe ya tashi ya hau shiryawa, kamar wani mace haka yake ta bin komai daki-daki, a karshe yayi wanka, ya bata lokaci wajen kayan da zai saka, kowanne idan ya dauka sai yaga kamar be ba, haka yayi ta sawa yana cirewa har ya samu daidai wadda yayi masa, ya fito sosai kamar wata a daren sha bakwai, sai shining yake kamar wani Ango fuskar sa dauke da madaukakin murmushi.
Cikin gidan ya shiga ya sami Mah-Mah da mai aikinta da Umaimah da tazo a satin jin zuwan Sultan din suna ta aikin girke-girken tarbar su Umman, sosai Mah-Mah take farin ciki da dawowar su dan dama tayi kewar Umman da kawancen su, shiyasa take cike da farin ciki a gefe kuma Safwan dinta zai hadu da abin da zuciyar sa keso.
Da kallo tabi Safwan din yadda yayi kyau sosai, ya fito a cikakken mutum, sai ta hau gode wa Allah tana kuma addu'ar samun cikar burin sa. Ganin ya shigo kitchen din sai ta kasa hakuri sai data magantu
"Kayan nan sun karbe ka sosai." Tace tana murmushi
"Allah Mah-Mah?"
"Allah kuwa, kamar wani ango."
Dariya yayi yana shafa kansa, Umaimah dake gefe tace
"Hala dai gasar kyau zaka je ba wai airport ba ko?"
"Duk yadda kika dauka haka ne." Yace yana hararar ta a wasa, sai ya maida kallon sa wajen Mah-Mah yace
"Zanje Mah-Mah, mota biyu zamuyi data Mubarak kar su karaso suyi ta jiran mu."
"Shikenan Allah ya kiyaye."
"Amin." Yace ya juya ya fita yana jin kamar yayi fiffike ya ganshi a airport din, sha d'aya jirgin zai sauka amma gashi tun 10 ya gama ya fito yaje yasa Mubarak a gaba shima ya shirya suka dauki hanyar airport din.
***Sallama sukayi fa kowa da suka saba, sannan suka dauki hanyar airport din cikin wani irin yanayi da ya kasu kashi kashi, farin cikin komawa kasarsu cikin yan'uwansu da kuma bakin cikin barin mutane masu kirki da nagarata musamman Anty Muhsina da family dinta da suka zama kamar wasu yan'uwa dan sosai suka shaku da ita har sukan fad'a mata damuwar su daga ita har Afrah, bangare daya kuma tunanin abinda zasu tarar a chan din ya saka Amrah jin kamar tace ta fasa tafiya, tana jin kamar tana barin wani abu me muhimmanci behind her, kamar komai ya kare ne a lokacin da ta dora kafar ta a kan matattakalar jirgin tana jin iska na hudata ta ko'ina, yana bayan su shida Adnan sai dai fuskar sa a toshe take da bakin glass baka ganin ko kwayar idon sa saboda duhun sa, a wajen bincike suka hadu amma sai yayi kamar be ganta ba har aka gama musu komai suka wuce zuwa jirgin suka shiga, ita da Afrah na gaba shi da Adnan na take musu baya, a wajen zaman ma shi ya zauna a daidai saitin bayan ta, muryar sa da yake ma Adnan magana da ita ta saka jinin ta daskarewa, dunkulewa tayi a kujerar ta lafe tana shakar kamshin turaren sa na hugo boss da ya zama kamar dan shi kawai kamfanin ke yin shi.
Tafiyar sai ta zama masa kamar fami akan ciwon da yake son rufewa wanda ya gaza rufuwa har yanxu, ganin ta so close to him ya kara taimakawa, dake wa yayi yana kokarin saita kansa lokacin da Adnan yayi mata magana ta juyo idon ta ya sauka a nasa,duk da ya lullube su acikin bakin gilashi amma sai da wani abu kamar mayen karfe ya makale shi har ya kasa dauke idon nasa.
"Ya Allah." Ya furta yana shafa sajen fuskar sa, yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa da sauri da sauri kamar wanda yayi gudun tsere, ko da yake shi dinma ai gudun tseren akeyi between zuciyar sa da soyayyar Amrah, be san wanne ne zai tsare wa wani ba, dan yanzu sam zuciyar tashi bata bashi hadin kai kamar farko, gaban kanta takeyi ba tare da shawara ko neman zabin sa ba, balle akai ga ta dauki command din da yake bata na cire soyayyar Amran ta karfin gaske.
Filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano cike yake da mutane, daga gefe Safwan ne tsaye suna d'an taba hira da Mubarak duk da hankalin sa kusan rabi baya wajen ya kafa wa wajen da aka rubuta arrival ido, yana so ya zama idonsa na wajen sanda zasu fito,wani ne yazo giftawa ta kusa dasu yaji yana waya yana cewa jirgin ya sauka, wani irin tsalle zuciyar sa tayi kamar zata fito, yasa hannu wajen, taba shi Mubarak yayi ya juyo adan firgice
"Man ya kamata ka nutsu fa, get hold of your self."
Bece komai ba, shi kad'ai yasan abinda yake ji da kuma abinda yake tunani.
So sorry 😐 nayi typing ya goge gaba d'aya wallahi
Da kyar na yi wannan. Ignore the typos 😸 Abinda Ke Cikin Zuciya
Page 18
©® Hafsat Rano
Wattpad @HafsatRano
instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac.
_*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_*
_*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _*
_*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*
_*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*
_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*