Sashe 21
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
Wannan littafin na kudi ne idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin nan*
*0903 234 5899*
Or
*09033181070*
© Hafsat Rano
Page 12
***Bazai iya tantance tsawon lokacin daya dauka a wajen ba, ya dai san yana jin dukkan burarin da wayar sa take yi tana yankewa da kanta, bashi da karfin halin da zai iya daga wayar balle ya kai ga amsawa masu faman jera masa kiran, sai ya kashe ta gaba d'aya ya tura ta aljihun gaban dogon wandon sa. Hannayen sa ya hade waje d'aya suka bada sautin k'as, ya sake maida idon sa ya rufe su ruf yana jin dama komai be faru ba, dama za'a iya komawa baya a goge abinda yake a yanzu, idan yace dama komai yana nufin komai din, ciki har da kaddarar data kawo shi kasar, ya kuma shak'u da ita har yake jin rabuwar su zai masa wuya ainun, sai dai ya zamar masa dole, ya rabu da ita ya kuma toshe duk wata kofa da zata bar wani gibi da har Safwan zai sani, baya fatan hakan ta kasance, ba kuma ya fatan wani ma ya sanar dashi. Zai cika masa alkawarin da yayi masa, zai nemar masa soyayyar Amrah ko da hakan na nufin katsewar nasa numfashin.
Tashi yayi bayan shafe dogon lokaci, ya duba address din zuciyar sa na jaddada masa cewa nan ne kad'ai in da zai je a yanzu, yana jin kamar idan ya gansu dukkan damuwar sa zata tafi, be damu da ko karfe nawa bane, burin sa kawai ya isa garesu. Har kofar katon gidan ya tsaya, ya daga kansa yana duban gefe da kewayen gidan, yana kuma nazari, nazarin da ba zai iya cewa shi kad'ai yasan me yake yawo a saman kansa. Hannu yasa ya taba kofar, yana saran wani ya fito ya ganshi, a hankali yaga kofar ta bud'e, sai kuma yaga matashiyar yarinya ta tsaya a gabansa, cikin shigar kayan da yayi kama dana masu aiki, matsawa tayi baya kad'an cikin maganar ta, ta bahaushiya tace
"Wa kake nema?"
Sama ya kalla, cikin tunanin abinda zai ce mata, be san wajen wa zai ce mata ba, dan baya jin bayan hirar da sukayi ya tambayi sunan dattijon, ganin ta tsire shi da idanu sai ya dan shafa gefen fuskar sa, sannan yace
"Wajen Babah nazo, idan yana ciki kice wanda suka hadu dazu ne."
Bata ce komai ba, ta bi wata doguwar hanya ta haura saman wata baranda, yana tsaye ya zuba wa hanyar da ta bi ido yana kallon tsari da yanayin gidan. Bata jima ba ta dawo, ta kuma yi masa jagoranci har zuwa hadadden falon nasa, yana gishingid'e, fuskar sa tana kallon kofar yana dakon shigowar sa, kamar wanda k'wai ya fashewa a ciki ya shiga ciki, bakin sa dauke da sallama kansa a duke yana kallon k'asa
"Yaka Muhammadu." Yace yana mika masa hannu ganin yana neman zama daga nesa da inda yake, matsawa yayi da jan jiki ya zauna daf dashi, ya gaishe shi a sanyaye
"Karka yi mamakin kiran ka da nayi da Muhammad, duk wani namiji Muhammad ne."
"Haka sunan yake ai dama Baba."
"Ah toh Masha Allah." Sai ya dora
"Ban sa rai da zuwan ka ba kwata-kwata ma fa, sai kaga a lokacin da banyi tsammani ba."
"Zanzo dama Baba."
"Naji dad'i, da kasan yadda zuwan naka zai faranta rai na dana Gimbiya, da tun dazun zaka biyo mu, sai dai yanzu ma naji dadi sosai."
A jere suka shigo su uku dauke da tray kowanne su kansa a k'asa suka ajiye a gaban wajen sannan suka d'an rissina kad'an suka juya, har sun kai kofa ya dakatar dasu
"Ina take?"
Da baya da baya d'aya daga ciki ta dawo, ta rabe a gefe sannan tace
"Ta gargad'i kowa akan shiga shashen ta yau, tace tana bukatar hutu."
Kallon Sultan yayi, sannan yace
"Ka ci wani abu ina zuwa kaji?" Ya mike da d'an k'yar sannan ya soma takawa a nutse, yabi wata kofa daga chan gefen falon. Bayan ya rakashi da ido ya sauke idonsa akan trays din, baya jin a halin da yake ciki zai iya saka ko da ruwa ne a makogoronsa, balle wani abu me suna abinci. Karar AC da karar Tv suka dauke shi suka wurgashi chan wani bigire, farkon rayuwar sa kawo yanzu da ya zama mutum, cikakken mutum me cikar Iko, sai kuma ya dauki tunanin shi ya koma baya, rayuwar sa a orphanage din nan, da kuma abubuwan da suka faru kafin zuwan sa gidan da bashi, be ji shigowar su ba, sai jin maganar ta yayi a gefen sa, ya rasa me yasa, yake jin abinda yake ji a tattare dashi a tare da wadannan bayin Allah, yana jin kamar wanda yayi aiki ya gaji matuka ya iso gida cikin familyn sa,ko wanda yayi doguwar tafiya yana bukatar hutawa a inda ya zama kamar shine final destination dinsa.
Gaishe ta yayi yana ayyana abinda yake faruwa da ita, kallo daya zaka mata ka gane akwai abinda yake damunta me girma, wanda yayi nasarar dakushe kaso sabanin cikin d'ari na walwalarta, guzarin ta dama yadda take abubuwan ta, yaji yana son tambayar ta abinda yake damunta,sai dai bashi da wannan hurumin, be kuma ma san da wacce fuskar zata dauki abun ba.
Sallama yayi musu, ba a son ransu sukayi bankwana ba, yana shiga gidan ya tarar da Adnan a falo, da sauri ya mike
"Lafiya kuwa? Kira babu wanda ba'a yi maka ba amma no answer daga karshe ma sai aka kashe ta baki daya."
"Mun shiga wani aiki ne tare da manyan docs na asibitin, dole muka kashe wayar saboda yadda aikin yake." Ya amsa masa da haka dan be shirya fadawa kowa abinda ke zuciyar sa ba, ya wuce daki ya barshi tsaye yana rarrabe kalmomin
"Something is wrong." Yace yana bin bayan sa, yana shiga yaji karar ruwa a toilet, sai ya zauna yana jiran fitowar sa dan ya tabbata akwai babban abinda ya same shi din. Daya fito be yarda sunyi wata magana ba, yayi kwanciyar sa gami da jan duvet ya rufe har saman kansa, yana bukatar time yayi nazarin abinda ya kamata yayi, kafin Safwan ya nemi jin yadda aka kwana. Be runtsa ba har aka kira sallah, ya tashi dak'yar ya dauro alwala yayi nafila sannan ya fita inda suke jam'i dasu Abba suka yi sallah sai kawai yayi zaman sa awajen yana tilawar karatun Al-Qur'ani me girma, sai yaji zuciyar sa ta washe, nauyin da yake ji ya ragu sosai, karatun Qur'ani babban magani ne dake tafiyar da damuwa da kunci ya kuma sake tabbatar da haka. Tashi yayi ya koma ciki ya shirya a gaggauce dan baya son haduwar sa da Amrah, sai dai yana zuwa kofa ya tarar da ita a jingine jikin ginin tana rike da dan madaidaicin basket mai kyau, fuskar ta babu walwala, yana jin sanda ta sauke ajiyar zuciya, bata ce komai ba ta mika masa basket din ta wuce shi ta shige ciki, gaban kansa ya murza da karfi ya had'e bakin sa waje daya ya taune da karfi yana jin wani iri, ta yaya zai iya bawa zuciyar sa hakuri akan abinda ta jima tana burin mallaka? Ta yaya zai iya wannan babban aikin da shi kansa ganin ta yanzu ya sake jin kamar ba zai iya din ba, kamar bashi da karfin zuciyar. Da kallo yabi basket din, takarda ce fara daga d'an gefe yasa hannu ya ciro ta ya karanta
_"Karka manta kaci please, jiya gaba daya baka ci komai ba."_ Amrah
Sai ya kundundune takardar, ya chusa ta aljihun sa, ya tsuguna ya dauki basket din ya fita da d'an sauri, sakin labulen data makale a jiki tayi ta fad'a kan kujera zuciyar ta na harbawa da sauri, me yake faruwa?
***Har ya kusan gama aikin ranar be samu kwakkwaran idea abinda ya kamata yayi ba, yana jin jiki dan kansa yayi wani irin daure masa jijiyoyin na amsawa Kamar zasu ballo da jini amma be daina matsawa kan da tunanin mafita ba, mafitar da zata zama matakin farko na cika alkawarin da yayi masa.
***Waya Abba ya daga da niyyar kiran Daddy akan maganar, sai dai labarin rashin lafiyar Safwan din ta hanashi dauko masa maganar, yayi masa fatan samun lafiya sannan sukayi sallama. Ya kalli Umma dake gefe tana jiran jin yadda za'a yi, yace
"Kinji ashe Safwan din ne ciwon sa ya tashi, suna asibiti ma."
"Subhanallahi, yaron nan na shan wuya wallahi."
"Wallahi,baki ji muryar Alhaji Sulaiman din bama, abun tausayi."
"Allah ya bashi lafiya."
"Amin." Ya amsa sai kuma yace
"Shiyasa watakila sultan jiya bashi da walwala yaron, kuma da yake miskilin kansa ne kinga ai be fad'a wa kowa ba."
"Allah ya kyauta, zan kira Mah-Mahn anjima idan Allah ya yarda."
"Ya kamata gaskiya."
"In Sha Allah zan kira, ni yanzu wani tunani ma na tafi, Idan ace yaran nan su dukka biyun babu wanda yasan da zuciyar dan'uwan sa, ya kake ganin zamu warware wannan abin?"
"Muyi addu'a Allah ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi."
"Haka ne, Allah ya kawo komai cikin sauki."
"Amin." Ya amsa.
***
*Masarautar Saji*
Babbar masarauta ce, wadd take dauke da mutane masu yawan gaske, gari guda ce babu abinda ba'a saidawa a cikin ta,sannan akwai manyan makarantu da asibiti a cikin ta, babu abinda dai mutum zai nema a ciki be same shi ba.
Shiga yayi sak irin ta mutanen da ake kira da bararoji, kansa rufe ruf da wani yadi me kaurin gaske, baka ganin komai sai idanun sa wanda idan ba tsananin sani kayi masa ba, ba zaka iya ganeshi ta farat daya ba.