← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 108

Sashe 100

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

     Tashi tayi kawai ta wanko fuskarta a bayi, ta fito ta goge ta, ta dauki jakarta tayi hanyar fita daga dakin dan tana ganin zuwan nata gidan ma kamar wani tonan asiri ne gareta.

"Ya Ummah bari na wuce, kiyi hakuri ba wai bana son sanar dake bane,sai dan cewa ciki ba dan abinci kawai akayi shi ba, wannan maganar sirri nace, ina kuma fatan ba zaki ji komai ba akan hakan."

Rik'e baki Hajiya Umma tayi, sosai maganar ta daketa, me Mah-Mah take nufi kenan? Har ta fice daga dakin, ta kuma fice gaba daya daga gidan bayan ta gaida su Hajja Hajiya Ummah bata fito daga mamakin da ta shiga ba, jikinta yayi sanyi k'warai, ta k'asa barin wajen sai da k'yar ta ja kafafunta guiwa a sake ta bar gidan tana jin bacin ran wulakanci da Mah-Mah tayi mata, ko da yake bata ga laifin ta ba, ita da ta damu da ita ta cusa kanta a harkar da babu ruwanta ita ta jawo ma kanta wulakanci.
   Ko da ta dawo gida ma sai ta shige gidan su Amrah wajen Umma tayi zamanta dan tasan nan ne kad'ai wajen da zata samu nutsuwa, daga baya ma sai tayi kwanciyar ta a falon Umman ba kuma tare da Umman ta nemi tasan dalilin hakan ba duk kuwa da taga alamun babu lafiya amma bata tambaya ba saboda bata so ta shiga hurumin da ba nata ba.
   Har la'asar Mah-Mah na gidan bata tafi gida ba babu kuma wanda yazo neman ta anan taci abincinta dama gashi tana son girkin Umman, , tun da Daddy ya dawo yaga motar ta a waje ya kuma duba gidan yaga bata nan yasan tana gidan su Amran,be matsa mata akan lallai ta dawo ba, saboda yasan tana bukatar zuciyar ta, ta huta da abinda ya tunkaro su shi dinma dauriya kawai yake a matsayin sa na namiji amma har zubda hawaye sai da yayi. Ko da Safwan ma ya tambaye shi sai yace babu komai ya kwantar da hankalin sa ya maida jikin sa zasuyi magana idan Sultan ya dawo. Hakan ya saka ya kwantar da rabin hankalin sa yana jiran dawowar Sultan din.

****
Har suka isa gida hannun sa na cikin nata, kanta a saman kafad'ar sa, tun bayan da ya gama amsa wayar da ta gane daga Safwan ne taga ya sake yin shiru ya shiiga tunani, bata tambaye shi ba har suka karasa gidan. Da suka fito daga motar ma sai kowa yayi nasa waje ta nufi wajen Ummi shi kuma ya wuce wajen Babah. Bata san dadewar da sukayi tare da Baban ba dan har kusan goman dare Sultan din be neme ta ba. Tana shiiga daki ta tsaya a gaban mirror tana kallon kanta, ta kara haske tayi wani irin fresh banda yar ramar da tayi ta chanja sosai. Sai ta tuna abinda Aunty Muhsina tace mata akan aure, murmushi tayi ta shafi fuskarta, tana tuno wasu abubuwa.
Ta cikin mirror ta hangi shigowar shi, kafin ta juyo ya karaso, ya saka hannunsa ya zagayo dashi ta cikin ta, ta sakar masa murmushi suna kallon juna ta cikin mirror.

"My wife."

"Umm..."

"Me kike kallo?"

"Ba komai."

"Fad'i gaskiya, kina kallon beautiful fuskarki kina admiring ko, kina kuma godiya Allah."

"Um um, kawai gani nayi kamar nayi fari sosai." Tayi maganar tana kallon fuskar shi ta cikin mirror din, juyo ta yayi ta zama shi take kallo, ya kare mata kallo sosai sannan yayi murmushi

"Sai glowing kike kamar wata a dare sha biyar, menene sirrin?"

"Nothing, kawai dai..."

"Kawai dai kawai dai, ok ni ai na san sirrin."

"Menene sirrin?"

"Zan fad'a miki anjima."

"Um um please ka fad'a min yanzu, ni yanzu nake so na sani."

"Really? Yaushe kika yi baki haka?" Ya matso da fuskar sa kusa da tata sosai

"Jiya, yau, dazu, dama ina da baki kawai dai..."

"Kawai dai jan class." Ya karasa ya kai hannu ya lakace mata hanci

"Afrah ta koya miki magana wife."

"Dama ina yi fa."

"Um na yarda, baki tambaye ni komai ba, har nayi fushi na,na huce."

"Laaa, kayi hakuri Allah abun na raina, kawai naga kamar kana busy ne shiyasa."

"Toh naji, yanzu dai damuwa ta Safwan ce, tunda Abba yace min ya fad'a ma Mah-Mahn duk da dai abun ba sauki amma still yazo da sauki fiye da yadda mukayi tunani, yanzu damuwar mu Safwan ne, yadda zai dauki zancen shi da ba cikakkiyar lafiya ba."

"Ya Sultan..."

"Umm..?"

"Ya Safwan mutumin kirki ne, kuma ya riga yasan kaddara, kuma ya yarda da kai fiye da kowa da komai, kaine zaka fad'a masa saboda kai kad'ai ne zaka iya fad'a masan,nasan da farko zaiji babu dadi, amma kuma babu wanda zai samu iyaye kamar su Ummi yace zai ma Allah butulci, ko ta wanne bangare gata ne Allah yayi ma mutum."

"Tabbas Safwan bashi da matsala, matsalar daya yanayin da aka bi aka haife su, Kinsan wannan abun shi zai fi tsaya musu a zuciya daga shi har Muhammad din, wanda zan iya cewa tsawon rayuwar sa be san akwai wani abu wai surrogacy ba,be taba tunani ko hasashe ba, bayan haka karki manta Aminatu na raye ba mutuwa tayi ba, ga Ummi a gefe daya, kinga abun is somehow complicated."

"In sha Allah komai zai tafi daidai, ka daina damuwa abin da ya riga ya faru ya faru sai dai a kori gaba, Allah ya yafe mana."

"Haka ne, Amin ya Allah, I'm now relief, thank you so much wife."

"It's my pleasure dear."

"Umm, guess what?"

"What!?"

"Gobe fita zamuyi, zamu je wurare da yawa, inda ma baki taba sanin yana existing ba, and I'll make sure you have the best time of your life,."

"Umm really!?"

"Yess yess, zaki gani, just make your self ready." Ya kashe mata ido daya

"In sha Allah, I can't wait."

"I can't wait too." Yayi curving fuskarta da tafin hannun sa, with out another word ya had'e bakin su waje daya.

Early morning Amrah tashi, saboda zumudi ta hau shiryawa, dama tun a daren bayan Sultan yayi bacci ta fidda kayan da zasu saka ta ajiye musu a gefe, hatta shoe and bag sai data ajiye, tana tashi kuwa ta hau shiryawa, tayi light make-up ta saka wasu riga da skirt yellow and Red rigar zuwa wajen guiwar ta sai skirt din da ya kasance straight skirt, ta yane kanta da veil tayi kyau sosai, tana kokarin saka rolling pin ya fito daga wanka, ya tsaya daure da bathrobe yana kallon ta, tayi kyau sosai kamar ka sace ta. Lokaci daya abu yazo masa akan sa, ya juya ya koma toilet din, jim kadan ya dawo ya wuce wajen kayan da ta ajiye masa ya zauna ya dauki mai zai fara shafawa,

"Kamar karar ruwa nake ji, ko ban kashe ba?" Yayi maganar yana kasa kunne,

"Aikam naji nima." Tace tana mikewa, ta nufi toilet din ba tare da tunanin komai ba, tana shiga yayi wata dariya ya tashi yabi bayan ta har da dan gudun sa, a lokacin ta kashe fanfon ta juyo sukayi kicibis a dan corridor da ya raba toilet din da dakin ya saka hannu ya tokare kofar yana mata dariyar k'asa k'asa.

"Ya Sultan... Please please kar muyi haka da kai."

Tace da sauri bayan tayi figuring abinda yake shirin yi, shiyasa ma ya kunna fanfon ashe duk trap ne.

"Duk wayon amarya..." Yayi maganar yana matsowa ciki,

"Na shiga uku..."

"Na shiga uku..." Ya kwaikwayi maganar ta, kafin ta sake cewa komai ya riko ta, ya maida ta cikin toilet din tana mata dariyar mugunta. Duk magiyar da ta dinga yi masa be jita ba, sai da suka sake wani wankan tare suka bata lokaci sosai sannan suka fito, tana ta sunne kai tana ciccijewa ya dinga mata dariya, dole ta sake sabon shiri ta chanja wasu kayan.
Ranar Amrah zata iya cewa was one of the best days of her life, sun yi having fun sosai, taga soyayya iya kar soyayya, sun ajiye komai sunyi enjoying ranakun ba kad'an ba, su ne Niagara falls, Quebec City, Lake Ontario,Cape Breton Island , Montreal da sauran wuraren shakatawa a k'asar ta Columbia. Daga nan suka zarce Ice Hotel suka ci abinci a chan suka wuce resort dinsu, lokacin dare yayi sosai saboda haka kwanciya kawai sukayi. Haka suka yi kwanakin suna shakatawa karshe suka yada zango a Manitoba in da anan ne Amrah taga gata, sai da tayi kwallar farin ciki yadda Sultan yake tarairayar ta, tayi addu'ar Allah ya dawwamar da kauna a tsakanin su Allah ya kauda duk wani abu da zai shiga cikin rayuwar auren su da nufin ruguza su. Anan take jin ashe Ummi ce ta shirya musu tafiyar da kanta, kunya ta kamata da ya gaya mata, taji tana jin kunya idan suka koma.
Ranar da zasu dawo Ummi da kanta ta tare su, Amrah na sussunewa amma sai taga kamar ma Ummin bata fuskanta ba, kawai sai ta fuske aka shiga hira da labari gwanin sha'awa. Sulalewa tayi ana cikin hirar ta gudu daki, ta kunna wayar ta wadda ta barta a gida tun ranar, ta turawa Afrah message ta kwanta rigingine tana tuna komai tana murmushi.
Chapter 100 · 0% Book details