Sashe 1
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[3/4, 11:35 PM] Maman Maryam: *_Abinda Ke Cikin Zuciya_*
©®_Hafsat Rano_
(1)
****Yara ne yan kasa da shekara biyar masu yawan gaske cike da harabar babban gidan marayun, kowanne na harkar gaban sa wanda mafiya yawancin su wasa suke daidai da karancin shekarun su. Kasancewar yau asabar ce babu karatu sai na yamma, yasa harabar ta zama iya yaran ne kawai inda manyan cikin su ke chan baya suna wanki da gyare gyaren da ya zama kamar al'adar gidan a kowanne mako.
Zaune yake jikin ginin dakunan kwanan su ya tattare kafafuwan sa sama yana kallon su, yaro ne shi mara son hayaniya da rashin ji irin na sauran sa'oin sa, mafiya yawancin lokuta zaka ganshi zaune ya zura musu ido kawai yana kallon su ba tare da ya shiga wasan ba. Duk kuwa yadda Maman Yara take kokarin ganin ya sake a cikin sauran yara sam yaki, sai dai duk da haka wayon sa daban ne, yana da kaifin basira da saurin daukar abu, kokarin sa har mamaki yake basu, duk wani abu da anyi shi yake zama daram akan sa. Babban abinda ya zamar masa jiki shine tausayi, duk da rashin son hayaniyar sa, amma yana da mugun tausayi da kaunar duk wani yaro da yake cikin gidan nan.
A hankali gate din gidan ya shiga budewa,chak yaran suka tsaya da wasa suka zubawa kofar ido cikin son ganin me zai faru. Mota ce karama ta shigo cikin harabar gidan, ta samu gefe ta tsaya, da sauri duk yaran sukayi wajen motar da murnar su, mikewa yayi shima yana murmushi ya nufi motar har da dan gudun sa, kafin ya karasa sun fito, wani mutum ne da a kalla zai yi shekara arba'in ya fito hannun sa rike da dan karamin Yaron da bazai wuce shekara hudu zuwa biyar ba, yadda yaran suka zagaye shi zaka gane cewa ba karamin muhimmanci yake dashi a wajen yaran ba. Wata leda ya ciro a motar sa ya fara raba musu sweet yana shafa kansu d'aya bayan d'aya, duk wanda aka bawa sai ya tafi yana murna. Haka yayi ta raba musu har ya sallame su dukka kafin ya juyo wajen yaron dake tsaye gefe ya saka hannun rigar sa a baki.
"Sultan..." Ya kira sunan sa yana mika masa hannu, da d'an sauri ya karasa garesa yasa hannu ya daga shi sama.
"Baka saki jikin ka ba har yanzu my boy, me yasa ne wai?" Ya fad'a yana kallon Maman Yara data iso wajen
"Alhaji Sultan halin sa sai shi, baya son mutane gashi nan dai tun muna damuwa har mun hakura dan babu me chanja shi."
"Daddy waye shi?" Dan karamin yaron da suka zo tare ya tambaya yana kici-kicin bude ledar sweet din sa, rankwafawa Daddy yayi ya sauke Sultan a gefen sa, sannan ya kamo hannu yaron
"Sunan sa Sultan, abokin ka ne daga yau kaji?"
Sai ya daga kai kamar me tunani kafin yace
"Zamu tafi dashi toh muna wasa tare?"
Girgiza kai yayi sannan ya shafa kansa
"Zan dai dinga kawo ka wajen sa duk Sunday's sai kuyi wasan ko?"
Mak'e kafadar sa yayi irin yadda yara keyi, ya turo baki gaba kamar zaiyi kuka yace
"Ni dai yanzu nake so, dan Allah kaji Daddy."
"Alhaji mu je ciki ko?" Maman Yara ta katse maganar da zai yi, sai ya kama hannun su dukka suka nufi cikin gidan...
Takardu ta baje masa a gaban sa da bayanin duk abinda ya faru daga satin da ya wuce zuwa yanzu, karin yaran da suka samu da kuma karin NGO's din da suka sake hada kai dasu. Sosai yayi farin ciki ya kuma dauki Numbers din su da address domin su samu lokaci su sake zama sosai. Ya jima sosai a gidan yana aikace aikacen sa, da sauraron matsalolin da suke ciki da yin yadda za'a kawo saukin su. Da kyar aka nemo masa Safwan da zasu tafi ya shige cikin yara ana ta wasa kasancewar sa yaro me son mutane da faran faran. Sai dai duk in da yayi yana rike da hannun Sultan wanda a kalla zasuyi kusan sa'anni. A haka sai gashi ya dan saki jikin sa har yana dan shiga wasan. Ganin haka ba karamin mamaki ya bawa ma'aikatan gidan ba, musamman yadda kowa yasan waye Sultan da yadda yake. Har wajen mota ya raka su still suna rike da hannun juna Safwan har da kuka sai da Daddy yayi masa yawo sannan ya yarda ya tafi yana daga ma Sultan hannu.
****
*_(SMM OPANAGE)_*
Shine sunan gidan marayun, babban gidan marayu ne na wani bawan ALLAH wanda babu wanda yasan shi balle ya taba haduwa dashi sai mutum daya Alhaji Sulaiman (Daddy) , tun farkon kafuwar gidan Daddy ne yake kula da gidan har kawo yanzu da ya bunkasa sosai har kungiyoyin sa kai da yawa suka saka shigo ciki ake gudanar da komai tare. Zaka sha mamaki ganin irin yaran da gidan ya tara wanda mafiya yawansu tsintar su akayi wasu ko cibiya ba'a yanke musu ba gasu nan dai abun gwanin tausayi. Karatu da duk rayuwar su a cikin gidan suke yin ta, babu me fita waje daidai gwargwado basu nemi komai sun rasa ba, har su kan fi wasu yaran dake zaune gaban iyayen su.
Sultan yana d'aya daga cikin yaran da suke wannan gida, sai dai kamar sauran yara, akwai banbance banbance masu yawa a tsakanin su, tun daga zuwan sa gidan har kawo yanzu da yake ciki komai nasa daban Maman yara take masa. Bata yarda da kowa wajen kula da al'amuran sa ba,ita take masa komai da duk wani abu da zai nema tun kafin ma ya nema ta samar masa, hakan na bawa sauran ma'aikatan gidan mamaki sai dai babu me Ikon tankawa saboda itace shugaba kuma babu wani abu na rashin gaskiya ko rashin adalci da take wa sauran yaran.
***Kwana uku da tafiyar Daddy ya dawo, sai dai wannan karon ba kamar sauran zuwan da ya saba bane, muhimmin abu ne ya kawo shi, abun da zai zama mabudin dukkan wata kofa, kofar da zata zama alkhairi ga wasu ta kuma zama sharri ga masu sharri. Sun jima suna tattaunawa da Maman yara da manyan masu kula da gidan kafin a samu daidaita wa, hannu ya saka a gurguje bayan ya amsa kiran matar sa ya tabbatar mata yana kan hanya.
Ciki Maman yara ta shiga, ta dauko wata madaidaiciyar jaka ta bud'e tana bin komai na ciki da ido kamar me neman wani abu, ta dan dau wasu sakanni a haka kafin ta sauke ajiyar zuciya me karfi ta rufe ta maida ita ma'ajiyar ta ba tare da ta dauki komai ciki ba.
In da tasan zata samu Sultan ta wuce kai tsaye, ta riko shi har in da Daddy ke tsaye ya goya hannayen sa a baya yana kai wa da komawa, ganin su yayi saurin bude motar yana murmushi me bayyanar da tsantsar farin ciki.
"In sha Allah zan rike shi kamar yadda zan rike Safwan." Yace tun kafin tayi magana dan ya ga sanda take motsa baki tana tattaro maganar da zata fad'a. Daga kai kawai tayi ta zaunar da Sultan a kujerar gaba sannan ta dafa kansa tace
"Allah yayi maka albarka ya tsare ka a duk in da kake."
Sai ta kalli Daddy tace
"Yaran nan Amana ne a wajen mu, ina fatan zaka cika alkawarin daka dauka duk da bani da kokonto akan hakan."
"In Sha Allah." Yace da sauri sannan ya zagaya ya tada motar ya fita da dan sauri yana kallon wayar sa dake neman agaji, dagawa yayi ya kara a kunnen sa
"Muna hanya..." Kawai yace ya kashe ya bawa motar wuta.
*_Premier Clinics_*
A reception ya tarar da ita tana magana da staff din wajen, wuce ta yayi rike da hannun Sultan suka haura sama, kai tsaye dakin da aka kwantar da shi ya wuce ya tura, Dr na tsaye kansa yana gyara masa abin oxygen din inda wata nurse ta rike hannun sa daya tana shafa kansa, da sauri Daddy ya karasa shiga dakin ya tsaya gaban gadon yana kallon yadda tilon d'an sa yake battling da numfashi. Girgiza kansa yayi zuciyar sa na zafi still yana damke da hannun Sultan daya zubawa Safwan ido ganin abinda ake masa, sai da suka gama sannan bacci ya dauke shi, sai a lokacin Dr din ya bawa Daddy hannu suka gaisa sannan ya fita zuwa sauran ayyukan dake gaban sa.
Kujerar daya tashi Daddy ya zauna yana kamo hannun Safwan dake bacci a nutse alamun numfashin ya daidata, sai ya juya ya kalli Sultan dake tsaye ya kamo shi ya zaunar a gefen sa.
"Ka ga abokin ka ko? Bashi da lafiya yana ta cewa sai an kawo shi wajen ka, ina fatan idan ya farka ya ganka zai dawo daidai, komai tare zakuyi ka zama danuwan sa shima haka."
Kallon sa Sultan yake ba tare da ya fuskanci inda maganganun nasa suka dosa ba, ganin ya zura masa ido yasa ya d'an dafa kansa a hankali yace
"Na manta he's just a child, Allah yasa abinda nayi ya zama ya cike gurbin da muka rasa na farin ciki, Allah ya hada min kansu ya raya su ya bamu ikon tarbiyyartar dasu, Allah kar ya kawo abinda zai raba kansu."
"Amin..." Tace tana karasowa dakin, sai ya dago da sauri ya kalli inda take, karasowa tayi ciki tana kallon Sultan kafin ta kamo hannun sa ta dora shi a saman kafarta tana jin wani iri yanayi mara misaltuwa. Tana fatan hakan ya zama alkhairi a garesu baki daya.
Nace Allah yasa.