← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 115

Sashe 99

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan awa guda su Mother na waje, sedai likitocin da Nurses su zo su wuce su, ba wanda yace musu komai, Mother ta kira dr. A waya ta sanar masa halin da ake ciki, ba daÉ—ewa se gashi da Jidda sun zo Asibitin.

Se bayan kusan awa É—aya da mintuna sha biyar sannan babban likitan ya fito yana cire safar hannunsa ya cewa Abba suje Office É—insa.

Bayan sunje suka sake gaisawa, doctor ya kalli Abba yace "Yallaɓai, ya akai aka bar abokina ya shiga wannan yanayin haka a wannan ƙananan shekarun nasa?" Da yake likitan da Familyn Abba sun daɗe tare suna zuwa Asibiti sosai, dan haka ya san Sadik sosai mutuminsa ne.

Abba yace "meya same shi ne haka?"

Likitan ya É—anyi ajiyar zuciya yace "well, jininsa ya hau ranka ya daÉ—e, hawa ba na wasa ba kam, da shekarunsa sun ja sosai fiye da haka, yadda jinin nan nasa ya hau, kuma ya faÉ—i da ya kamu da paralyse" Abba ya zaro ido yana kallon doctor.

Doctor ya cigaba da cewa "na sa an ɗebi jininsa an kai lap, dan yin wasu gwaje-gwaje, yanzu kuma zan rubuta hoton ƙwaƙwalwa da na zuciya idan ruwan da aka saka masa ya ƙare, se kuje ayo a waje, dan nan bama yi"

Abba ya jinjina kai yace "Ikon Allah, to Allah ya bashi lafiya".

Doctor yace "Ameen, se ai ta kula ana kwantar masa da hankali, amma a shekarunsa ace jininsa yana irin wannan hawan gaskiya akwai matsala"

Haka Abba ya fito jiki a sanyaye, yaiwa su Mother bayani, Usman ya hau faÉ—a "yanzu akan an ce baze Auren ba shine yake nema ya kashe kansa? Aikuwa sedai ya mutu dan ubansa a wannan karon ba ze samu yadda yake so ba".

Jidda tace "haba dr., Dan Allah ka tausayawa halin da yake ciki ka bar wannan Maganar dan Allah, a bari ya samu lafiya".

Mother na shirin yin Magana, wayarta ta fara ringing kan ta cirota ta katse, missed calls É—in Nana kusan guda Ashirin, Mother ba ta sani ba, ta bi lambar Nanan, tana É—agawa kukanta ta fara jiyowa, Nana tace "Mother ya jikin nasa? Ya tashi kuwa?"

Mother tace "ki kwantar da hankalinki, yaji sauƙi an masa allura ne yana bacci".

Tace "to Mother in biyoku?"

Tace "A'a, ki zamanki likita yace a barshi yai baccinsa karki damu, tare zamu dawo gida insha Allah".

Nana tace "to, dan Allah a masa sannu, amma ba abunda ya same shi ko?x

Mother tace "eh, malaria ce, kuma an ba shi magani".

"To Allah ya ba shi Lafiya".

Mother ta amsa mata da Ameen.

Zuwa jimawa se ga Mummyn Khairat ma, tare da Khairat sun zo duba Sadik, nan suka dinga jajanta lamarin wai Sadik da hawan jini.

Har akaje gurin hoton ƙwaƙwalwar da zuciya Sadik be san anyi ba, saboda ƙarfin Allurar da a kai masa.

Abu Kamar wasa Sadik se bayan sallar isha'i sannan ya farka da ga nannauyan baccin da ya wuce da shi bayan suman da yai, likita ya zo kansa ya dudduba hoton ƙwaƙwalwa da akai masa, da na zuciya duk lafiya ƙalau ba matsala.

Likita yace "Alhamdilillah, zuciyarsa lafiya ƙalau haka ƙwaƙwalwarsa, amm he is at risk of stroke, saboda jininsa yadda ya hau, yanzu dai muna ta ƙoƙarin jinin ya sauka zuwa normal, gashi can ya farka a samu a bashi Abinci, yai salla zamu kuma yi masa Allurar bacci, amma kar a matsanta masa se yai Magana, sannan kar a ɗaga murya a ɗakin nasa, komai ai masa a hankali".

Mother ta amsa da "to".

Usman ne ya kai Sadik ya kama ruwa, ya zo yai salla ba wanda yace wa Uffan, aka kawo masa Abinci ba wani ci yai ba, ya É—auke kai, ya gyara kwanciyar sa ya lumshe idanunsa.

Se jera masa sannu suke, amma babu wanda ya amsa.

Usman yace Su Mother su tafi gida, shi ze zauna a gurin Sadik, musamman saboda Nana da ta na can cikin damuwa.

Jin an ambaci Nana Sadik ya buÉ—e ido yace "Nana tana ina?"

Mother tace "tana gida, ita da Sahal"

"Ace mata tayi haƙuri dan Allah, Mother ku bata haƙuri dan Allah".

Sadik kamar yana cikin magagi ne, be san meyake faÉ—a ba, surutai kawai yake yi.

Mother da Abba su kai sallama da dr., Suka tafi gida, dama Jidda tuni ta koma gida tai musu girki ta aiko musu da shi.

A falo Mother suka tarar da Nana, tai shiru kana ganinta ka san a cikin tashin hankali take, tana ganin su Abba ta miƙe tana faɗin "Abba, ina yake? Ina baban Sahal ɗin?"

Abba yace "kwantar da hankalinki, se Allah ya kaimu da safe, Sannan za'a sallame shi".

Nana tace "to waze kwana da shi a can?"

Mother tace "Usman yana can, tare da shi zasu kwana"

"Mother da ma ni aka bari na kwana da shi"

Abba yace "ba damuwa, ki kwantar da hankalinki, ya warke ai, ai gobe in Allah y kaimu za ki je ki duba shi"

Da kyar suka kwantar wa da Nana da hankali, sedai se aikin kuka take tana Allah ya ba shi Lafiya.

Ba Mummyn Lillyn ba, shi kansa Major ya ji baƙi ciki da takaicin abunda 'yar uwassa ta aikata, dan da fari cewa yai ya barta da Allah, dan ba ya jin ze iya yafe mata abunda ta aikata, taje ta yi abu ya dawo kan 'yar sa.

Mummy ce tace "kaga Major kayi haƙuri ka yafe mata dan Allah, ka san kaima Akwai naka laifukan da ka aikata, mu bar hakan a mazaunin ƙaddara kawai, Allah ya ƙara shirya mana zuri'a".

Major yace "wannan abu da me yai kama? Ina amfanin irin wannan rubutu da tai, Yanzu idan ta mutu yaran mutne suka cigaba da karantawa suna lalacewa fa? Allah kaɗai ya san adadin yaran da suka gurɓace a sanadin abunda ta rubuta, Wallahi ji nake kamar in mata Allah ya isa"

"A'a Major, kayi haƙuri tun da har tai nadama, Aikin gama ya gama, se fatan Allah ya kiyaye gaba"

Haka Mummy tai ta bashi baki, tana kwantar masa da hankali.

Bayan fitar Major, Lilly ta shigo É—akin Mummy, gaba É—aya tai wani iri ta zama saliha sosai da sosai.

Mummy ta kalleta tace "ya dai?"

Jiki a sanyaye tace "Mummy alfarma na zo nema a gurinki".

"Wace irin Alfarma kenan?"

"Mummy, dan Allah karki bari Daddy ya auran wannan sojan bana son sa, ya min girma sosai, dan Allah kuyi haƙuri ku yafemin ba zan sake ba, kuma bana son a maida ni garin nan, dan Allah kumin rai".

Mummy tace "A'a, ba dai ba kya jin magana ba, ba ruwans duk hukuncin da ya yanke a kanki daidia ne, tun da ubanki ne".

"Mummy dan Allah, ku min rai Wallahi bana son sa".

Mummy tace "ba kya son sa to wa kike so?"

"Mummy, dan Allah ki saka Daddy ya sa a saki sir Nazir, idan aka sake shi se muyi Aure, tun da shine.... Se kuma tai shiru.

Mummy tace "ƙarasa mana, sarauniyar marasa kunya, ashe ma haryanzu ba ki nadama ba

Lilly ta girgiza Kai cikin hawaye tace "Mummy nayi nadama, ina neman afuwarku, amma haryanzu ba zan dena zargin kaina, da ni nai silar komai ba, Sir Nazir Mutumin kirki ne, RUƊIN ƘURUCIYA da tashen balaga ya kai ni ga yi masa tarko, kuma ya kasa tsallake tarkon nawa, muka afka ga wannan ramin da muke nadama a yanzu haka, dan Allah Mummy ku bari in Auri Nazir"

Mummy ta kalli Lilly tace "ba ki da hankali, ke kina tunanin idan ya Aureki zaki daraja a idonsa, duk abunda ze wa ɗokin kin riga kin miƙa masa a waje, har kin yiyyi ciki kin zubar dan haka babu abinda zaki burge shi da shi, kuma baze taɓa yadda da ke ba, ke a wannan rayuwar ka kaiwa ɗa namiji mutuncinka gidansa ma, cin ubanka yake balle ke da kuka gama watsewa a waje, kullum a cikin zarginki ze kasance kuma kaf danginsa ba wanda be san meyafaru ba yanzu, ba zasu dinga ganin laifinsa ba, se naki laifin, dan haka ki maida hankalinki tun wuri, tun da Allah ya sa shi wannan be san ta'asar da kika aikata ba, kuma ya ɗan kwan biyu, ze kula da ke kuma ba lallai ya damu ba, tun wuri ki manta da wannan yaron"

Lilly ta share hawayenta tace "to Mummy, nagode"

Mummy tace "kije ki nemi guri ki huta"

Lilly tace "to Mummy, da tun da farko Daddy ya Auramin Nazeer, wataƙila da wannan abun be faru ba, amma dan Allah ku yafemin"

Mummy tace "daga ni har mahaifinki, munyi kuskure, Allah ya yafe mana baki É—aya".

Ƙarfe takwas da rabi na safe, Nana tana cikin Asibitin da aka kwantar da Sadik, Nana kasa haƙuri tai, Mother ta sa direba ya kawota kafin su zo, Nana a rikice ta shiga ɗakin da akace Sadik yana ciki, ta ƙarasa gaban gadonsa, ta zuba masa ido, rana ɗaya amma har ya rame, ga ruwa yana shiga jikinsa a hankali.
Ta ja kujera ta zauna ta zuba masa ido, a hankali ta kwantawa da kanta a ƙirjinsa, ta fara kuka.
Ji tai ya sa hannu ya riƙo nata hannun, be mata Magana ba se hawaye dake bin gefen idonsa, ta ɗan ɗago ta kalle shi tace "Sannu"
Be amsa ba se ƙara matse hannunta da yai a nasa.

Dr. Ne yai sallama shi da Khairat da Jidda, Dr. Ya ƙarasa gaban gadon yace "meye haka zaka saka yarinya a gaba kana kuka, kamar wani ƙaramin yaro salon ka sake ɗaga mata hankali?".

Jidda tace "Baby ka ƙyalesu dan Allah, kana gani tun jiya be wani yi ƙwaƙwƙwaran mosti ba, alama ce ta ya fara samun sauƙi".

Dr. Yace "duk da haka ai se ita ma ya É—aga mata hankali".

Nana kasa É—aga Sadik tai, shima kuma ya kasa sakin hannunta, "Allah ya baka lafiya, in dai nice kayi Aurenka in dai hakan zesa hankalinka ya kwanta"

Usman yace "ke tashi in maida ke gida, ba ze Auren ba".

Nana ta girgiza Kai tace "dan Allah Yaya Usman ku bar shi yayi, kar ya rasa ransa".
Chapter 99 · 0% Book details