Sashe 53
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashi tai daga in da take zaune, ta zagaya in da yake ta hau kan teburin, ta ɗan ƙura masa ido sannan tace "ba zan iya rabuwa da kai ba"
"Saboda me?"
"Saboda dalili me ƙarfin gaske, kayi haƙuri da abunda mahaifina yai maka, ka bari ya wuce"
"Lilly ba zan iya mantawa da abunda mahaifinki yai min ba, dan ba wanda ya taɓa yi min abunda yai min a rayuwa ta"
Ta kai hannu kan sajensa da ke ta ƙyalli ta shafa, sannan ta ɗan lumshe idanunta ta buɗe akansa tace "na sani, amma na ari bakinsa na ci masa albasa, kayi haƙuri Please i miss You so Much, ba zan iya rabuwa da kai ba"
"Am missing you too, but is better to be apart, da Matsala ta afku"
"Meyasa kake kira mana matsala ne? Ba matsalar da zata faru Insha Allah"
Duk da ƙarancin shekaru irin na Lilly, se da tai abunda ta sa ya manta da matsalar da mu'amalarsu za ta iya haifarwa a gaba, sosai sheɗan yake ingiza su, suke ƙoƙarin sake biyewa son zuciyar su.
Takun da sukaji ne da surutu, alamar ana hawowa step É—in benen da Office É—in yake, ya sa Lilly saurin tashi daga jikinsa, ta daidaita nutsuwarta, ba tare da ta iya furta komai ba, tai masa alamar za su waya, ta fice daga Office É—in, yayin da shi kuma ya lumshe ido, yana maida numfashi a hankali.
Su Taslim ne suke hawowa benen, dan zuwa ya koya musu wani aiki.
Taslim ta kalli Meena tace " ke tayani gani mana, wai meke going ne tsakanin yarinyar nan da mutumin nan?, ku san kullm fa se mun ganta a nan"
Meena tace "ba ance budurwar sa bace, ai ba abun mamaki bane"
"Duk da haka, me suke a Office su ka É—ai a saman nan, kullum fa semun ganta anya ustazancin nasa na gaske ne?"
Meena tai dariya tace "a'a sedai ki bari in mun shiga ki tambaye shi" su kai dariya gaba É—aya suka shiga Office É—in.
Nana ce zaune akan gadonta, ta lumshe ido tana karatun Alkur'ani a hankali, cikin sauti me daÉ—in sauraro, kasancewar ita kaÉ—ai ce a É—akin Linda ba ta nan.
Seda ta kai aya ta buɗe ido, taga Linda da wata ƙawarta sun zubo mata ido, kamar sunga wani abu daban.
Cikin harshen turanci tace "Lafiya, meyasa kuke kallona?"
Linda tace "wai dan Allah me kike karantawa haka?"
"Is my holy book qur'an"
Linda tace "wow, kuma kin san abunda kike karantawa, na ga ba kowane musulmi ne yake jin larabci ba"
Nana tai murmushi tace "Yanzu balaraben da yake Kirista, idan ya karanta bible ya san abunda yake karantawa?"
"A'a, amma ai akwai bible na larabci"
Nana tace "to Kasancewar Alqur'ani da larabci, hikima ce ta Ubangiji, karanta shi kuma ko baka san ma'anarsa ba yana samar da nustuwa a zuciyar me sauraronsa, wani abun nasan fassarar abunda nake karantawa.
"Hakane, yana da daÉ—in sauraro kam, amma zan so wata ran ki karanta bible, shima zaki ji daÉ—insa"
Nana da hausa tace "kaji 'yar baƙin hali, ni zaki canzawa addini, amma da turanci tace "to shikenan babu damuwa"
Ƙawar Linda tace "amma meyasa kike saka hijjabi, da dogayen rigunan larabawa, ku Mutanen Africa kuna koyi da larabawa ne?"
"Ba da larabawa muke koyi ba, dokokin addinin mu muke kiyayewa, shi yai mana umarni da sanya hijjabi da suturta jikinmu"
"Amma da gaske Africa babu Abinci, duk matalauta ne?" Cewar ƙawar Linda.
"Ji shegiya da fuska kamar alade, Abincin gidan ubanki muke ci muka girma, ji 'yar banza me koÉ—aÉ—É—iyar fuska"
Linda tace "ba mu gane me kike cewa ba"
Nana tace "Addu'a nake da hausa, bacci nake ji yanzu, ma cigaba wataran"
Ta juya ta kwanta ta na cigaba da ƙunƙuni da mita.
Mother gani tai lamarin Abba dagaske yake, ya watsar da ita ya fita harkarta gaba ɗaya, sabgar gabansa kawai yake, haka ta dinga lallaɓashi, kamar ta zubar da makamanta, har ta samu ta shawo kansa da ƙyar, ya ɗan sakko ya rage fushin da yake, har suka koma cin Abinci tare da kwana guri ɗaya.
Faruk ma yana ta shirye shiryen komawa South Africa, in da zeyi master's ɗin sa, yayin da Khairat ta kamu da tsananin ƙaunarsa, tana ta nan nan da shi tana ba shi kulawa ta mussaman, sam shi be taɓa kawo wani abu ne a ranta na Soyayya ba, ga shi Haseena na ta takura mata, akan dan Allah wai ta haɗa da Faruk tana sonsa.
Kwanci tashi asarar rai, tamkar ana jan kwanakin, haka suka dinga gudu, awanni, da ranaku suna shuÉ—ewa, zuciyar Farhan cike da burin sake tozali da masoyinta ta kasa fidda ran Sadik É—in ta ze dawo gareta, ko ta samu ta rabu da Sunusi, dan yau kusan wata guda kenan da sa ranar Aurenta da Sunusi.
Ko a makaranta yanzu ba ta ƙoƙari, bata iya fahimtar karatu sam, in akai test ko jarrabawa ma faɗuwa take a wasu, grade ɗinta yai ƙasa sosai, kullum tana zaune shiru ba sawa ba fitarwa.
Kamar kullum, tana wannan tafiyar tata kamar wadda a kaiwa dole, fitowarta daga Makaranta kenan, ta miƙo hanya za ta fito titi ta samu abun hawa, taji ana mata horn, cikin hanzari ta waiga, zaton ta za taga Sadik.
"Sena buge ki ki lanjare ko? Kina tafiya kamar ba kya so, ko haryanzu jikin ne?"
Murmushin ƙarfin hali tai tace "ina wuni"
"Lafiya ƙalau, dama makarantar nan kike zuwa?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
Yace "Masha Allah, shigo mu tafi'
Ta girgiza kai alamar a'a.
"Wasa nake da ke, shigo mu tafi nace"Â yai maganar yana haÉ—e rai sosai.
Tana matuƙar jin nauyin Abbas sosai, ta buɗe baya zata shiga ya kalleta yace "waye direbanki, gaba zaki shigo"
Jin ta take kamar zata aikata zunubi, ba wanda ta taɓa shiga gaban motar sa banda Sadik, wata zuciyar tace idan Sadik ya ganki fa? Ze iya jin ba da daɗi.
Haka ta shiga tana wasi wasi, ya ja Motar suka fara tafiya.
Abbas yace "Lalallai Baba yayi ƙoƙari, wannan makarantar kike zuwa?"
"Scholarship ne na samu"
Yace "Masha Allah, you deserves it, dama nasan kina da ƙoƙari ai"
Tai murmushi tare da sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta, kawai Sadik take tunawa, ta kalli hannun Abbas da yake tuƙi, taji ina ma zata ga hannun Sadik me ɗauke da agogo da zoben azurfa, ta ɗaga kai ta kalleshi ya waigo ya kashe mata ido ɗaya Allah sarki Sadik. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, wadda se da Abbas ya waigo ya kalleta yace "Lafiya kuwa?"
"Lafiya ƙalau" ta bashi amsa a hankali.
"Baki tambaye ni ya akai kika ganni ba, bayan nace miki zanje ƙaro karatu"
"Mantawa nayi"
Murmushi yai yace "kinji ki, wai mantawa ki kai, ba ki niyya ba dai,na gama clearance next week zan tafi insha Allah"
"Allah sarki, Allah ya bada sa'a"
"Ameen, Farhan, idan kika kammala secondary School, insha Allah zan karɓi takaddun ki, school of Nursing zaki tafi, zaki dace da aikin jinya, duk da ban san meye ambition ɗin ki ba"
Ai kamar ya taɓo mata wani abu da yake damunta ta fashe da kuka.
"Subhanallah, meya saki kuka kuma?"
Cikin kuka Farhan tace "burina ba ze cika ba doctor, Babana Aure ze min"
"Aure kuma? Na zaci da wasa Hajiya take min da tace min an kawo kuÉ—in Auren ki"
Wani irin tausayin Farhan ya mamaye shi, yace "calm down please, yi haƙuri ki share hawayen ki, ai darajar 'ya mace in ba Gidan iyayen ta ba dama to ɗakin mijinta, in dai ze barki ki cigaba Alhamdilillah"
Duk da rashin son Magana, da tsananin zurfin ciki irin na Farhan, amma ta tsinci kanta da cewa "bana son sa, ba na ƙaunarsa, ban taɓa son sa ba"
Jiki a sanyaye ya kalli Farhan yace "kina nufin ba ke kika kaishi kika ce kina so ba?"
"Bana son shi, maganar Soyayya ba ta taɓa haɗani da shi ba, ya tura aka nema masa aurena a gurin Abba, Abba kuma ya amince, Amma bana son shi"
"Ya Salam, yanzu na ƙara gano dalilin rashin lafiya da ki kai, amma kin gayawa Abban cewar ba kya son sa?"
"Ai ba su taɓa tambayata ko ina son sa ko bana so ba, koma sun tambaya ba zan iya bijire musu ba, saboda sun min komai a rayuwa, ba zan iya bijirewa ba" tai maganar tana wata irin sheshsheƙa.
Ya É—an zuba mata ido, yarinya ce Sosai, sedai ba kowa Allah ke bawa yaro me nustuwa da biyayya a wannan zamanin ba, ba kowace Yarinya ce zata iya hangen nesa da kuma iya Magana kamar Farhan ba.
Yai ƙasa da murya yace "ni kin bani dama in tari baban in gaya masa ba kya son Auren?"
Tai saurin girgiza kai tace "wannan sirri ne na gaya maka, dan Allah kar ka gaya musu, nasan ba wani dalili da zesa a fasa Auren nan, dangin mahaifiyata ba zasu yadda ba, dan sune suka asassasa lallai a bar karatuna ai min Aure"
Abbas ya shiga mamakin wannan wace irin rayuwa ce, akwai banbancim zamani tsakanin rayuwar da su kai a baya da wadda ake a yanzu, amma an takura Yarinyar nan da yawa, gaba É—aya jikinsa yai sanyi wani irin tausayin ta ya mamaye shi gaba É—aya.
Ya kuma kallonta yace "to ya batun Sadik fa?"
Ta share hawayen ta tace "na fara yadda da maganar ka, na Sadik ya barni amma zuciyata ta kasa gazgata hakan, Sadik ba ze taɓa barina ba"
"How sure are you,ba ze taɓa barinki ba?"
Shiru tai ta kasa Magana.
"Ki bawa wanda zaki Aura É—in dama mana, he might be more than Sadik"
A hankali ta girgiza kai tace "Never, he is irreplaceable! Ba Wanda ze iya maye gurbin sa" Tana gama maganar ta fita daga cikin Motar Abbas, sedai tana fita É—in Sunusi na jikin pole a tsaye, yana binta da ido!.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.