← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 115

Sashe 107

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sha gyaran gashi da ƙunshi, sedai haryanzu Farhan gani take kamar a mafarki, wai zata auri Sadik, sedai ta kasa farinciki, musamman idan ta tuna irin ɗawainiyar da Abbas yai da ita, kuma ga mahaifiyarsa tana ta cigaba da yi mata ƙoƙari.

Sadik na zaune ya shiga social media, ya ga hotunansa nata trending, wai ɗan Auta  gidan Alhaji Abdullahi Rano, ze auri mata ta biyu yana da shekaru Ashirin a duniya, nan ya dinga ganin Comments kala kala, wasu suna cewa iyayen da suke ba shi yaran ne mahaukata, wasu suce tunda iyayensu ɓarayin ƙasa ne, dole suyi abund suka ga dama, nan ba da daɗewa ba ze sake su a aura masa wasu, haka dai kowa da kalar abunda yake faɗa, wani na alkhairi wani na sharri, Sadik ya rufe datarsa yace "Insha Allah, Allah baze bamu kunya ba".

A wannan karon ma Abbas da kansa ya kaiwa Farhan dubu hamsin, ta kasa masa godiya se kuka, kamar wadda a kaiwa mutuwa, yai ta bata haƙuri yana kwantar mata da hankali tare da yi mata Nasiha.

Babban abunda yake sake faɗarwa da Farhan gaba be wuce yadda ba zata kai mutuncinta gidan Sadik ba, ta san abu ne mawuyaci duk da son da Sadik hake mata tai mutunci a idonsa, saboda budurcin mace shine 'yan cinta a gidan miji, ga shi tana da abokiyar zama, tabbas ta san akwai damuwa a wannan lamari, gaba ɗaya jikinta ya ƙara sanyi sosai da sosai.

Sadik ba yadda be da Farhan ba akan ya kama mata guri, tai walima tace ba ta so, a layinsu a ka kafa runfuna aka kira malamai mata sukai lecture, akai mata kamu aka ci Abinci aka sha daidai gwargwado.

Duk yadda Nana ta so dakewa kasawa take yi, dauriya kawai take tana sabgoginta, amma abun yana dukanta sosai da sosai, gashi Sadik se kujiba kujibarsa yake yi, ko ganinsa ba ta samun yi sosai, sedai ta hange shi.

Faruk na zaune a falo yanawaa Sahal wasa, Khairat ta zo tana yauƙi ta ɗan kashe murya tace "Man a kawo coffee ne?"

Faruk yace "No thank you"

Nana da ke gefe tace "gaskiya Uncle ka yunƙura, zan tsaya maka bana son ganinka a haka ba Aure, karka fara tsufa fa"

Faruk yai murmushi yace "kedai bari kawai, ni da ban wani damu in Auren nan ba, amma tun da Allah ya sa aka haifi Sahal, na samu abun wasa, naji nima ina son in auren, a haifamin abun wasa ko Abbana" yai maganar yana É—aga Sahal sama.

Nana tace "gaskiya uncle ka motsa".

"To maman Sahal, amma kin san matan ne se a hankali, samun tagarin ne se a slow".

Su Nana ba rufi se cewa tai, "Ba wani se a slow, ga mata a gida se ka tafi dawa, naga ga Khairat nan tana ƙwanƙwasa, dan Allah ka bada dama a wuce gurin".

Shi kansa Faruk se yaji kunya, balle Khairat da Nana ta farkewa laya haka ba rufi, Khairat taji kamar ƙasa ta tsage ta nutse.

Nana tace "ya naji kun wani yi shiru ne? Ko na faÉ—i ba daidai bane?"

Faruk yace "da dai a bar wannan maganar?"

Nana tace "ba za'a barta ba, ai Magana ce ta gaskiya, a gaskiya a gida a na so ba zamu bari kaje waje ka auro ba, muna da wannan zuƙeƙen saurayi haka, ace a kai waje, gaskiya a'a tunda ana so a gida, shikenan mun maka mata, zan shigar da maganar ku da zarar an gama bikin Besty"

Sumsum Khairat ta miƙe, dan ba ta zata shishshigin da takewa Faruk ana ganewa ba, da sauri ta bar falon, Nana a ranta tace ina sane na faɗi haka, gurin mijina dai ba space wannan ma dan ya ƙallafa ransa ne, ni ba kishiyarki ba amma kin sani a gaba" a zahiri kuma tace. "dan Allah uncle a duba lamarin nan, save the innocent soul of your sister"

Faruk yace "Maman Sahal, gaskiya a tsarina bana son Auren Yarinya, nafi son me ɗan hankali, Khairat tai min yarinta da yawa, kuma ƙanwa kawai na ɗauketa"

Nana tace "haba Uncle, meye aibun Khairat ne?"

Faruk yace "ba ta da kunya, ga shigar banza, ga ta da abokai maza da yawa, kowa friend ɗinta ne, yarinya ƙarama da hak ai be dace ba, and at least yakamata ace ko level 2 ta shiga kan tai Aure"

Nana tace "Yanzu ni ban isheka misali ba? Ni ma lokacin da Besty ya Aureni bani da Kunya Wallahi, ka tambaye shi kaji, ni ga rashin Kunya ga ƙauyanci, duk da dai ƙauyancin nawa ba wani na azo a gani bane, amma gara Khairat tana da tsoro yin rashin Kunyar wasu lokutan, ni a lokacin bana son sa, kasan dai irin takun saƙar da muke yi da shi, amma a hankali da na fara sonsa duk na dena.
Ita mace in dai tana sonka, za tai duk wani abu dan ta burgeka, kuma zaka iya saita ta yadda kake so.
Auren Khairat da zakai ze iya cetota, idan ta shiga Jami'a ma ze zama tana da katangar Aure a Tare Da ita, hakan baze bari ta cigaba da kule kulen mazan da baka so ba"

Faruk yai shiru, yana mamakin yadda Nanan ke tsara magana cikin hikima.

Faruk kawai yai murmushi yace "Hajiya Nana kenan"

Nana tace "Uncle, ka taɓa soyayya kuwa?"

Murmushi yai yace "eh to, bana ce a'a ba na taɓa"

"No gaskiya ba ka taɓa ba, da ka taɓa ba zaka ƙi karɓar tayin Khairat ba, baka da nauyin Soyayar kowa a kanka, zaka iya farawa da soyayyarta, dan Allah kar ka bari ta shiga hatsarin soyayya, soyayya akwai wahala musamman idan kana son maso wani" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin goge hawayenta.

Faruk yace "Subhanallaahi, dan Allah Nana ki dena, ko Sadik É—in ne yake miki wani abu?"

Tace "A'a, sedai na fara son Sadik a lokacin da be kamata ba, lokacin da ban san akwai wadda take ransa ba, yana da kyakywar mu'amala, kan ka zauna da shi zakaga ya fiye izza, da raina mutane, amma ba haka yake ba a zahiri, hasali kyawawan ɗabi'unsa suka sa na fara son shi, sedai na makara, ina ta ƙoƙarin danne komai ya koma bakomai ba, amma na kasa bana jin daɗin yadda nake masa, amma ba yadda zanyi ne. Ni babban damuwata shine su Mother su dena jin hausinsa, su yi masa uzuri dan so ba shi da linzami. Dan haka uncle dan Allah kar ka bari Khairat ta cutu, idan har ba wata a ranka ka amince da ita dan Allah, tana sonka sosai za tai maka biyayya insha Allah, amma ni zan haɗa lefe kuma haihuwar fari sunana za'a saka, ko na Besty" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi duk da hawaye ne a fuskar ta.

Wani irin tausayinta ya kama Faruk, tabbas Nana 'yar halak ce, yayi mamamki da Mother tace masa Nana ce ta saka baki, da kuma maganar Hakimi sannan suka amince, yarinyar tana da sadaukarwa, kuma dagaske take son Sadik ba wasa ba, tabbas idan Sadik ya cutar da ita dan yana son wata Allah ze saka mata.

"Maman Sahal, naji dukkan maganganun ki, kuma insha Allah zan san abunda zanyi akan Khairat, and akan mijinki ki dena cewa kina son maso wani, Wallahi Nana Sadik yana sonki, so na gaske kuwa, ai kin riga kin gama da shi tunda har kika nema masa alfarmar a bashi dama yai Auren, wani babban abun burgewa da halayensa shine baya butulci Sadik, ba wai dan ɗan uwama bane no, ba goya masa baya nake ba, amma idan ki kawai Sadik alkhairi bayan shekaru yana sane a ransa, mutum ne me halacci sosai, dan haka ki sawa ranki ƙaddarar junanku ce a tare duk ku ukun, ki duba wani abu na ikon Allah, dokar gidan nan seka haɗa master's za kai Auren fari ma, amma shekarun sa sha bakwai zuwa sha takwas aka aura masa ke, kuka haifi Sahal, yanzu haka se nan da wata uku in Allah ya kaimu ze cika shekaru Ashirin dai-dai, amma kalli mata ta biyu za'a aura masa duk da tsananin zafi da Aƙida ta iyayenmu, amma wani ikon Allah, dr. Da ake cewa ya isa Aure yau kusan shekaru huɗu zuwa biyar da Aurensu ko ɓari matarsa ba ta taɓa yi ba, ni gani kalleni nima haryanzu ban Auren ba, nima idan nayi babu tabbacin in samu ƙaruwa, shine ƙaramin mu Amma Allah ku ya fara bawa ɗa, haka ya isa ya tabbatar miki da cewa rayuwa Allah shike tsarawa bawansa komai, kalli irin ƙiyayyar da Mother ta nuna miki a baya, fafur cewa tai se ta kashe Aurenku kin sani, duk da yadda yake akwai matukar shaƙuwa tsakanin Sadik da Mother, saboda yana sonki yai burus da umarnin ta be sake ki ba, saboda yana sonki, kuma da yake Allah baya ɗorawa bawansa abunda ba ze iya ba, cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya juya komai, Yanzu Mother jinki take kamar ita ta haifeki, kalli yadda yanzu take ta nan nan da ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, Allah yana tare da ke a Kowane hali, kuma albarkacin kin saka baki, ƙanwata ce ke da kika isa da yayanki, za duba maganganun ki akan Khairat"
Nana ta ɗago tana murmushi tana share hawaye tace "Nagode uncle, naji daɗin maganganun ka, sun bani ƙarfin gwiwa, insha Allah komai ya wuce, zan daure zuciyata in dubi Ni'imomin da Allah yai min, in yaƙi sheɗan da kishi".

A daidai nan Sadik ya shigo, ya tarar da Faruk da Nana a zaune, ga Nanan tana share hawaye, wani abune ya soki zuciyar sa ya tsuke fuska yace "ina son magana da ke"

Faruk yace "meye haka zaka shigo ba sallama?"

Nana tace "to ka gayamin a nan mana, naga Ai Yaya Faruk ne kawai a gurin".

"Cewa nai ina som magana da ke" ya faÉ—a a kausashe.

Tashi tai tabi bayan Sadik, suka shiga wani É—aki ya kalleta yace "Me yake ce miki?"

Nana tace "shi wa?"

"Faruk"

"Me kuwa yake cemin, hira muke yi"

"Hira kukeyi shine har kike masa kuka yana rarrashinki?"

Nana tace "Haba to meye a ciki, Yayans fa nima"
Chapter 107 · 0% Book details