Sashe 65
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A'a ya zo"
"Shikenan, ina fatan ba wata matsala dai?"
"Ba wata matsala, am just missing You mum"
Mother tace "Allah sarki Autana, ya makarantar?"
"Makaranta Lafiya ƙalau, komai normal"
"To Masha Allah, Allah ya bada sa'a, ka kula da kanka sosai da sosai, ina kuma jadadda maka ba kai ba yarinyar nan, karka kuskura kaje in da take, ina nan ina wani shiri yadda zan raba Auren nan kan ku dawo, ba tare da mahaifinka ya ji haushin mu ba"
Kallon Nana Sadik yai, ya ga She's busy siffin her Coffee, tana yi ta na kalle kalle.
Ranar da Steve ya zo gidansu, ya haÉ—a shi da Abba a waya, Abba ya ja kunnensa sosai sannan yai masa Nasiha yace "Yanzu Sadik, idan ni ko mahaifiyarka ya mutu, ya zakaji?"
Sadik yace "haba Abba, dan Allah ka dena irin wannan maganar"
Abba yace "ina son ka bani amsa ne"
Sadik yace "zan shiga damuwa, ban san yadda zan misalta halin da zan shiga ba"
Abba yace "idan kuma ka rasa mu duka fa?"
"Abba, dan Allah ka dena wannan maganar, kar ka sa zuciyata ta karye"
"To ina son ka misalta kanka a matsayin Nana, haka fa ta tashi ba uwa ba uba, ba ta san daɗinsu ba sam, ta dai tashi tsakanin kakaninta, ka sanya kanka a matsayin da Nana take na maraici, duk gatan da za'a maka ba kamar gatan iyaye ba ne, ni ba zan takura maka se ka sota ba, amma dan Allah ina roƙonka, kar ka cutar da ita, ka yi haƙuri da ita ka dubi maraicinta, akwai falala me girma a cikin riƙon maraya, ba ita tai maka laifi ba, kar ka huce a kanta, kayi haƙuri, ina lallaɓaka a yanzu, amma idan kaje ka aikata son zuciyar ka, to duk hukuncin da Ubangiji yai maka sedai in kalleka"
Wannan maganganu na Abba ne ya sa jikinsa Sadik yin sanyi sosai, ya zamana da ya kalli Nana, se yaji tausayinta haka ta tashi ba ta san mamanta ba, ba ta san babanta ba ta rasa wannan Soyayyar ta su har abada, wannan dalilin ne ya sa ya ɗan sassauto da ga wannan ƙiyayyar da yake mata.
"Kai wai ba ka jina ne?" Se yanzu Sadik ya tuna waya yake da Mother, yace "Ina jinki, dan Allah ki turomin lambar bro, da yake amfani da ita yanzu"
Mother tace "shikenan, zan turo maka"
A hankali ya sauke wayar daga kunnnsa yana kallon Nana, da take ta lunshe ido alamar bacci take ji.
Ya miƙe tsaye ya kalleta yace "mu tafi"
Ya samo taxi suka ɗauki siyayyar da sukai, suka tafi gida, sedai kan suje tun ta ɓingire ta na bacci a Mota.
Kallonta yake, yana tunanin yadda ze tashe ta ba tare da ta masa ihu ba, dan ya san kaÉ—an da aikinta.
Ya fita daga Motar, ya sassauke kayan, ya buÉ—e gida sannan ya dawo ya É—auketa, zuwa cikin gida.
A kan gadonta ya ajiyeta, Sannan ya shigo da kayan da suka siyo.
Duk wannan budurin da Sadik yake ba ta san yanayi ba, saboda baccin nata yai nisa sosai.
Bisa ga umarnin Abba, Farhan ta komaa Makaranta, ta cigaba da zuwa, sedai ba ta gane Komai, kuma ba ta son mutane gaba É—aya.
Yau an fita break, Lilly ta shigo da ledar takeaway a hannunta, Farhan ta kalli Lilly tace "dan Allah Fatima, ina Mubarak Babba?"
Da mamaki Lilly tace "meyasa kike nemansa? Ina bakwa shiri da shi?"
"Eh na tambaya ne kawai, naji kamar rannan kince an kama shi ko?"
Lilly tace "eh hakane, ai dama shi wannan kusan kullum cikin kama shi ake, Amma karki mamakin yanzu haka ya fito, saboda babansa ya tsaya masa"
Farhan ta jinjina kai tace "shikenan Nagode"
"Ko dai ya cigaba da bibiyar ki ne?"
Farhan tace "A'a na tambaya ne kawai"
Amma a ƙasan zuciyar ta, so ta ke ta haɗu da Babba dan ta samu abun rage damuwa, hatsarin da ke cikin hakan be dameta ba, ita mafita kawai take nema.
Nana taji daÉ—in siyayyar da sukai, sedai Assignment ne da ita na Maths, na ta rasa yadda za tai solving É—in sa, ga shi yanzu tsoron Sadik take ji.
Ba ta da zaɓi illa zuwa ta sameshi, yana aikin na sa na video game tace "Amm.. dan Allah Assignment zaka koya min"
Ya É—an É—ago ya kalleta ya cigaba da game É—in sa.
"Dan Allah ka koyamin in ka iya"
"Ban hanaki ki zo kaina ki tsaya ba, kina min magana a haka ba, me nace ki dinga kirana da shi"
"Yi hakuri, na manta ne"
Ya miƙa mata hannu, alamar ta bashi littafin.
Ba musu ta miƙa masa, ya ɗan kalli Assignment ɗin sannan ya kalleta yace "ke wannan ne se an koya miki? Meye abun wahalar a nan?"
"To ba nayi na kasa ba" tai maganar tana cuna baki.
Tsaki yai ya karɓi biron hannunta, ba tare da yace mata komai na, ko yayi using calculator b, ya fara solving.
Abun ya bata mamaki sosai, ba ta taɓa ganin Sadik na karatu ba, sedai video game ko litattafan turanci, se kuma yawonsa.
Amma cikin nutsuwa yake solving ɗin, a mintuna ƙalilan ya kammala ya miƙo mata, ya karɓa ta kalla tace "to ai ban san yadda kai ba, idan kuma aka tambaye ni ya akai nayi fa?"
"Se kice, yi miki a kai ke ba ki iya ba"
"Hmm Allah sa ma daida kai min, kar in kai inci zero, kawai ka karɓi biro ka min rubutu a cikin littafi"
Kallonta yake da mamakin tsiwa irin ta Nana, sedai yaji gabansa ya faɗi, gani yake kamar abu makamancin wannan ya taɓa faruwa da shi a gaske, kamar wannan abun ya taɓa faruwa.
Take kansa ya fara juyawa, ya fara kokawa da memory É—in sa, akan ya tuna meyafaru, wani abu me mahimmanci yana cin sa a zuciya, amma ya kasa tuna ko meye.
Jifa yai da remote É—in hannunsa yana dafe kansa, a gigice Nana ta kalleshi tace "Subhanallah, meke faruwa ne meya same ka?"
Cigaba da rintse ido yai Sosai, yana jujjuya kansa akan ya tuna wannan abun, amma se yaji kamar kansa ze rave biyu.
Ta jefar da littafin hannunta, ta yo kan Sadik da sauri tace "baka da lafiya ne?"
Ya girgiza mata kai alamar a'a, da sauri taje fridge ta ɗakko ruwa ta kawo masa tace "karɓi ka sha ruwa"
Ba musu ya karɓa, ya ɗaga kai ya sha sosai, Sannan ya ajiye.
A sanyaye tace "ko Steve za ka kira, a kaika Asibiti?"
Ua girgiza mata kai, ya nemi guri ya kwanta yana ajiyar zuciya.
Nana ta zauna tai tagumi tana kallon sa.
Ya kai awa guda a wannan yanayin sannan ya watstsake, ya tashi ya fita.
Yau saura sati biyu, Auren Farhan ta sake susucewa, gaba ɗaya ta koma wata wujiga wujiga, kamar korarriya, banda azabar ƙiyayyar Sunusi da kuma son Sadik ba abunda yake ɗawainiya da ita.
Yau bisa ga jagorancin makauniyar zuciyar Farhan, me cike da neman mafita ta tafi ajinsu Sadik, gurin Tasleem.
Tasleem tayi mamaki da Farhan tace wai gurinta ta zo.
Farhan tace "dan Allah temaka min nake son kiyi"
Tasleem tace "wane irin taimako kenan?"
Farhan tace "da daÉ—ewa naji kuna cewa, akwai maganin rage damuwa da sa bacci, shine nake son dan Allah zan siya ba na iya bacci sam"
Tasleem tai murmushi tace "duk tunanin Sadik É—in ne?"
Farhan tai shiru ba tace komai ba, Tasleem tace "welcome to the jungle Yarinya, Allah ya baki kyau da ƙira, ki mori ƙuruciyar ki, amma kika tsaya biyewa Soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, a wannan surara ta ki, ba iya kayan caji Yakamata ki tsaya ba, Yakamata ace kina ehhhh" Tasleem tai maganar tana shafa bayan Farhan...........
ME KUKE TUNANIN ZE FARU? FARHAN BA IYA DAMUWA KE DAMUNTA BA, HAR DA MATSANANCIN FEELINGS, ZATA SHIGA GANG ÆŠIN SU TASLEEM, LET'S DISCUSSED THIS BEFORE ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLA)
(Amin afuwa, typing ba yawa, saboda yanayi na Salla, in Allah ya kaimu gobe ranar Arfa, zanje hutu se Allah ya kaimu bayan salla insha Allah zamu É—ora, dan Allah kar ku manta da ni a cikin Addu'oin ku a ranar Arfa.)
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Kasa ɗaga ƙafarta tai da ga in da take tsaye, tai shiru ta shiga tunani "yanzu idan ki ka fita ina zaki a Wannan dare? Wa kike da shi da zaki gurinsa? Idan ki kai haka kin wa kanki adalci kenan? Mutuncinki da kimar ki za su zube a idon duniya, kuma ki bawa iyayenki kunya, ace kin gudu ranar ɗaurin Auren ki.
To amma ai auren dole za'aimin, yanzu shikenan nai bankwana da farinciki? Shikenan haka rayuwata za ta ƙare, in rayu da mutumin da babu alamar Soyayyar sa a raina? Ta ya zan iya Rayuwar Aure da Soyayyar wani a raina? Abba meyasa kuka kasa fahimtar kawaici nai muku? Bana son wanda zaku Auramin?" A hankali wasu siraran hawaye suka fara zirarowa daga Idonta.
A hankali ta ja ƙafarta ta koma cikin ɗakinta, ta ɗakko maganin da Babba ya ba ta, ta ɓallo ɗaya ta ɗau ruwa ta shanye, a tunanin ta ko tai bacci ta samu sassauci.
Ta nemi guri ta kwanta ta ƙurawa guri ɗaya ido, tana tunani daban daban a zuciyar ta.
Befi mintuna goma da shan maganin nan ba, ta ji kanta yana mata wani irin abu, Kamar duniyar na jujjuyawa, ta rintse idonta ta buÉ—e amma ta ga komai yana juya mata, gani tamkar ginin É—akin da take ciki ze ruso kanta.
Hannu ta sa ta danne kanta, ta rintse ido, wani irin gumi ya shiga kwaranyo mata, ta rasa gane a wace duniyar take, a zahiri abunda take gani ne, ko kuma ita kaÉ—ai take ganin abunda take gani.
Haka ta wanzu a wannan hali, ba tare da sanin in da kanta yake ba.