Sashe 21
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya nemi guri ya kwanta, ya janyo filo ya ƙanƙame ya runtse idanunsa, sedai surar Farhan ce ke dawo masa, yana kuma jin sa a wani yanayi.
Wasa wasa bacci ya gagari Sadik kamar yadda dariya ta gagari kare, ba abunda yake se yarfe gumi.
Wani tunani yai, a irin hirarrakin da suke da su Nas, yadda suke shawo kan irin wannan matsalar in sun tsinci kansu a ciki, sedai galibi duk ruɓaɓɓen tunani da su, dan duk ta hanyar saɓon Allah suke samun mafita.
Tsaki yai ya miƙe ya nufi cikin gida, duk kowa ya kwanta bacci, ya lallaɓa ya shiga Kitchen, tea flask ya duba ya samu tea, ya zuba cofee sosai a ciki, ya zauna a Kitchen ɗin yana sha kaɗan kaɗan.
A hankali ya kammala sha, ya koma É—akinsa sedai babu wani canji sosai.
Æangaren Farhan ma seda ta tsarkake kanta, dan yau sun zarce Æ™a'ida, duk da fargabar tuhumar da ta fuskanta yau, be hanata jin ta aikata ba daidai ba na biyewa Sadik da tayi yau.
Abunda ba ta taɓa zaton zata aikata ba, se gashi cikin lokaci ƙanƙani Sadik yasa duk wannan kunyar ta ta ta ajiyeta a gefe.
A hankali ta furta "Yasalam, Astagfirullah, ya Ubangiji Allah kar kasa in rasa mutuncina saboda Soyayya, Allah ka yafe mana, Allah ka tabattar min da Alkhairi tsakani na da Sadik, Allah ka tsaremu aikata Zina ka nunamin Ranar da za muyi Aure" haka ta cigaba da Addu'a ƙasa ƙasa.
Umma kam kasa zaune tai ta kasa tsaye, seda Abba ya dawo gida, ta bashi Abinci yaci ya nutsu sannan ta kalleshi tace "magana nake so muyi"
Yace "ina jinki"
"Game da wannan yarinyar ne"
Abba yace "me kuma tayi?"
"Nifa na kasa gane kan wasu abubuwa da ke aikatawa kwanan nan, kusan kullum seta gota lokacin dawowa daga Makarantar dare, yau se goma da rabi ta dawo, na tambayeta tace wai sunje dubiya, gaba ɗaya alamu sun nuna ƙarya take, nifa gaskiya tsoro nake ji"
Abban Farhan ya numfasa yace "to yanzu meye abunyi? Ke ba wani matsarta kike ba balle ki tabattar da abunda kike zargi, amma meye abunyi a naki ganin?"
"Abunyi ɗaya a haƙura da wannan bokon, wannan Yaron ya turo ayi Auren nan, yanzu har an fara yarmin da magana a dangi, na bar Yarinya a gida muna haɗa kafaɗa, dan Allah kayi wani abu a kai"
"Banƙi ta taki ba akan Yarinyar nan, amma ni a jikina na yadda da ita, duk da ba'a shedar ɗan yau, tana da burin yin karatu a Rayuwar ta, dan haka bana fatan tauye ta, shiyasa nake son in bata dama, amma zan ga abunyi, idan Auren ne masalaha se ace ya fito ayi, amma nima kin jefa tsoro a raina, amma zanga abunyi insha Allah"
Umman Farhan tace "Aikam dai ya kamata a gaggauta sanin abunyi, tun kan ta jawo mana magana, kwanan nan duk ta canza gaba É—aya"
*****
Se gefin Asuba sannan Sadik ya samu bacci ya kwashe shi, da ƙyar ya tashi sallar Asuba, itama a ɗakinsa yai sallarsa, ko azkar be ba ya haye gado ya cigaba da baccinsa.
Ƙarfe takwas da rabi, Abba ya kintsa ya kalli Mother yace "Ina Auta ne?"
Mother tace "ina ga be tashi ba"
"Wane irin be tashi ba, ba shekaranjiya na gaya masa tare da shi zamu duba Hakimi ba? Faruk je ka taso min shi dan ƙaniyarsa"
Cikin bacci yake jin maganar Faruk a kamsa "kai Sadik ka tashi fa, Abba yana jiranmu wai ka manta yau da kai zamu tafi ƙauye?"
Wani uban tsaki Sadik ya ja, ya sake juyi ya cigaba da baccinsa.
"Wai ba zaka tashi ba, Abba fa ya shirya kai kawai ake jira"
Ai Sadik ko gezau beba, ya cigaba da baccinsa hankali kwance.
Faruk ya ƙyale shi, ya koma falo in da ya bar su Abba.
"Ina Sadik É—in?"
"Wallahi nayi nayi yaƙi tashi"
Abba yace "yaƙi tashi, bari inje da kaina ina taso shi, ko daga shi se gajeren wando ne haka zamu tafi"
Da sauri Mother tace "No baza'ai haka ba, yi hakuri bari inje in taso shi, yi haƙuri"
Mother ta fita ta nufi BQ, aikuwa tana zuwa ta tarar da Sadik a kwance abunsa yayi É—ai É—ai, yana kwasar bacci.
Ɗan ƙura masa ido Mother tayi, ganinsa take kamar jaririn da ta haifa jiya, haryanzu kallon abunta take wani ɗan ƙaramin yaro, da be wuce idan yana kuka ta rungume abunta ta rarrashe shi ba.
Ta ƙarasa gaban gadon nasa ta fara bubbuga filonsa.
Tura baki yai ze sake juyi.
Mother tace "dan ubanka ka tashi, in ba haka ba Abbanku yace ko daga kai se gajeren wando ne haka ze tafi da kai ƙauye"
A hankali ya buÉ—e idanunsa akan Mother, ya tura baki yace "ni wallahi Mother bana son Zuwa garin nan"
Mother ta sassauta murya tace "to ya zakayi, tashi za kai ka rufan Asiri kar Ya ce ni nake zigaka, tashi maza kaje kai wanka"
Sadik na tura baki haka ya shiga wanka, kan ya fito tuni Mother ta haÉ—a masa breakfast.
Da kanta ta zauna tana bawa Sadik ɗin Abinci a baki, yana ci yana zuba taɓararsa son ransa harya ƙoashi.
Ya saka ƙanan kaya, ya shafe sumarsa da mai sannan ya fito shi da Mother.
Abba na ganinsu ya ƙurawa Sadik ido daga bisani yace "Sannu ko"
Sadik ya sunkuyar da kai.
"Nace sannu, barka da warhaka ranka ya daɗe, ka shanyani ina jiranka ko? Harna aika amma kaƙi tasowa, da nazo kanka da zaneka zanyi"
Sadik dai bece komai ba ya koma gefe yana sosa ƙeya.
Wata jaka Mother ta samu, ta zubawa Sadik ruwan roba, da tarkacen cookies a ciki, wai ta san ba iya cin Abinci zeyi a can ba.
Sukai sallama suka kama hanyar tafiya.
Suna tafe a hanya suna hira da Farhan, yana tura mata messages.
"Beb kika hanani bacci jiya"
"Ta yaya na hanaka bacci kuma?"
"Through out the night am dreaming of you, gaba ɗaya na kasa bacci, gashi da sassafiyar nan Abba ya sa an tasoni mu tafi ƙauye"
"Eyya sorry, Allah ya kaiku Lafiya ya tsare ku, ka kulamin da kanka Please"
Murmushi Sadik yai ya tura mata "An gama Amaryar Sadik, Allah ya mallaka min ke Farhan"
"That's my prayer always"
"Dagaske kina mana Addu'a?"
"Hmmm, ni gani nake ma kamar nafi sonka"
"Ke 'yar Fulani Yaushe mu kai haka dake, kufa rigima ce da ku ga rinto, banda rinto ta ya kika fi sona?"
"Nice me rinto ko?"
"Eh mana kece, Yarinya dan baki san halin da nake ciki akan ki bane, ina sonki da yawa fa"
"Ya kai cikin kofi son da kake min?"
Kawai Sadik ya fara dariya, Faruk ya kalleshi yace "kai lafiyar ka kuwa?"
Sadik yace "Meka gani?"
"Gani nai kana dariya kai ka É—ai"
"No wata beb ce ke bani dariya"
Faruk ya girgiza kai yace "Allah ya shirye ka Sadik"
Sadik yace "meye kuma Allah ya shiryeni? Haram na aikata?"
"A'a ba haram ka aikata ba, amma gaskiyar Inna da tace be dace a kaika ƙasar waje karatu ba, zuwa za kai kai ta abunda Allah ya nufeka dayi, baka da wani zance sena mata da kuma Aure"
Sadik ya waiwaya baya, dan yaga Abba na jin hirar ta su, amma yaga Abba sam hankalinsa baya kansu, waya ma yake.
Sadik ya dawo da kallonsa kan Faruk yace "eh É—in anyi zancen Auren, lafiya ce ta kawo hakan"
Faruk yai murmushi yace "Ruɗin ƙuruciya kenan"
"Kaga ka kiyayeni da wannan zancen RUƊIN ƘURUCIYA"
Faruk yace "Allah ya ƙara lafiya Yariman Hausawa"
Sadik ya cigaba da hira da Farhan, ta hanyar musayar saƙonni, yana nishaɗi.
Da wuri suka ƙarasa garin, rabon da Sadik yaje garin nan harya manta Tsawon lokacin, dan gaba ɗaya garin nan be masa ba.
Ranar Asabar ne, ya kama ba Makaranta dan haka Nana tana gida ba in da taje.
Ta dawo daga aike taga motar su Sadik, fara'arta ce ta faÉ—aÉ—a, da taga Faruk ya sakko daga Motar.
Ya zaga ya buɗewa Abba shima ya sakko, har ƙasa Nana ta durƙusa ta gaida Abba, ya amsa mata cikin sakin fuska.
Faruk ya kalleta yace "Ina wuni"
Nana tace "A'a ai zan gaisheka, ina wuni"
"Ba zan amsa ba, tunda ni na fara gaisheki" yai maganar yana murmushi.
Abba yace "ƙyale wannan yayan naki, ya me jiki?"
A ɗan Sanyaye tace "jikinsa da sauƙi Alhamdilillah"
Abba yace "lafiya dai ko?"
Nana tace "eh Lafiya ƙalau"
Duk wannan maganar da suke, se yanzu Sadik ya buÉ—e motar ya fito.
Sumar nan se sheƙi take kamar gashin mace, ya ƙara fresh da shi kamar baya shiga rana.
Yana sanye cikin ƙanan kaya, wando jeans da baƙar T shirt, ya ƙara kyau sosai.
Ya ɗaga kai yana ƙarewa harabar in da suken kallo, ya ɗan kalli inda Nana take ya ɗauke kai.
Itama wata uwar harara ta wurga masa, irin ko da wacce ka zo daidai nake da kai É—in nan.
Suka É—unguma suka shiga gidan, Kai tsaye turakar Hakimi suka tafi dake cikin gidan.
Suka sameshi a kwance, hannunsa riƙe da carbi yayin da Inna ke sallar walha.
Hakimi ya yunƙura ze tashi zaune, Faruk da Abba sukai hanzarin zuwa suka ɗago shi.
Ya kalle su yace "Masha Allah, sannunku da zuwa kun sha hanya, Bawan Allah ka sai hanya kana ta zarya, Yakamata ka dinga hutawa"
Abba yace "Alhaji taya zan huta, ai duk inda nake hankalina yana nan baze kwanta ba, ka ƙi bari in tafi da kai"
"A'a bakomai barni a nan É—in, ina samun kulawa sosai"
Alhaji ya kalli in da Sadik ya ƙame a tsaye yana binsu da ido, yace "Yarima, yau an zo da kai kenan, manya gatan wasa"
Sadik ya É—anyi murmushin gefen baki yace "ina wuni, ya jiki"
"Jiki Alhamdilillah, ana dai yi mana addu'a ko?"
Sadik yace "eh ana yi"
"To madalla"
Inna ta idar da sallarta, ta shafa Addu'a tace "Sannun ku da hanya"
Abba yace "yawwa, yame jikin kuma?"
"Jiki Alhamdilillah da sauƙi"
Inna ta ɗaga kai tana ƙarewa Sadik kallo, irin kallon da ya tsana dan a haka take gano abunda za tai ta masifa a kai.
Ya É—an risina yace "Ina wuni?"