← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 115

Sashe 28

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To su dai 'ya'ya amana ce a hannun Iyaye, iya binciken da mukai bamu gano abunda yai dalilin rasa jinin Fatima haka ba, sedai shawarar da zan baku shine  a saka ido sosai a kanta, a kula da Abincinta sannan a kula da dukkan motsinta, da abubuwan da take yi"

Daddy be kawo komai a ransa ba yace "dan dai wannan ai bakomai insha Allah za'a kula, tunda ta samu sauƙin jikin nata harta fara complain, a sallame ta haka, kar a takurata da yawa"

Doctor yace "bakomai, yanzu zan sallame ta insha Allah"

Daddy yace "to shikenan, na gama clearing bills É—in mu ko?"

"Eh, tun ranar ai an biya komai, se fatan Allah ya ƙara lafiya"

Daddy yace "Ameen ya Allah, godiya nake doctor"

Suka sake yin musabiha, sannan Daddy ya koma É—akin da Lilly ke kwance.

Ya tarar da ita a zaune, tayi zuru zuru, kamar mara gaskiya.

Daddy uace "Baby na ya dai?"

Tace "bakomai"

Yace "nayi magana da Doctor, yanzu ze zo ya sallame ki, mu tafi gida zan kira Maman ki ba se ta dawo Asibitin ba tafiya za muyi"

Lilly tai murmushi tace "Amma Daddy meya ce maka?"

"Ina ruwanki da abunda yacemin? Bari ya zo ya sallame ki mu tafi gida.

Duk da be gayamata abunda likitan ya gaya masa ba, amma ta samu sassauci dan ta sam da an gano abunda ya sameta, to da tabbas zuwa yanzu kashinta ya bushe.

Washegari bayan an sallamo Lilly 'yan ajinsu suka dinga zuwa dubata, kowa yana mamakin abunda ya sameta da harta kaita ga ƙarin jini, ga fuskarta duk tayi wani iri ta kukkumbura.

Kasancewar yau Juma'a, Sunusi yaci ƙarfin aikin da yake akan Sadik da Farahn, kasamcewar aikin ba kaɗan bane, bayan an sakko daga sallar juma'a, zuwa la'sar yasa wani yadinsa ruwan ƙasa, ya tafi zance gurin Farhan.

Farhan kuwa tana É—aki, tana lissafin yadda kwanaki suke ja, amma babu É—uriyar Sadik ba ta san a wani hali yake ba, dama ya gayamata wayarsa ba caji.

Cousin ɗinta ne me suna Hauzaifa ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da Farhan ke ciki.

"Waye" ta faÉ—a cikin sassanyar muryarta.

"Farhan kinyi baƙo"

"Wane baƙon?"

Huzaifa yace "Wannan Almajirin ne, wai in masa sallama da ke, dan ya raina min hankali ma wai ni ya aika"

Tsaki Farhan tai, tayi shiru taƙi ko motsawa.

Umma ce ta fito daga É—akin ta tana faÉ—in "Huzaifa, kar ka sake ce masa Almajiri, ai ka san sunansa, kuma kasan shi ze Auri 'yar uwakka idan yaji kana faÉ—a masa haka baze ji daÉ—i ba"

"Umma dan girman Allah ku samu mutum nagari ku aurawa Farahn, wallahi basu dace da wannan Sunusin ba, haba dan Allah yaje ƙauyensu ya nemi dai dai shi mana, se wannan masha Allah ga ilimin addini da na zamani ka.."

"Kai Huzaifa ni kake gaywa haka? Shikenan dan mutum be ilimin zamani ba se ku dinga masa kallon be kai ba? Wace ita da ba zata aure shi ba? Masu ilimin bokon nawa ne sukai auren suke wahalar da matan, wannan da iliminsa da sana'arsa amma ka dinga kushe shi, kul kar ka kuskura in sake jin makamanciyar wannan maganar, ke kuma ki fito kije kin barshi a tsaye".

Farhan ta sako hijjabi ta fito, sedai idan har idon Huzaifa daidai ya gano masa, kuka Farhan take yi.

Gaba ɗaya yaji tausayinta ya mamaye shi, wannan wace irin rayuwa ce haka? Ace ba za'a bawa mutum zaɓin wanda ze rayu da shi ba sedai a zaɓa masa, hakan ba haramun bane amma babu tabbacin an tuntuɓi Farhan anji ta bakinta akan mutumin nan, kawai ake so a ƙaƙaba mata shi"

Farhan ta fita jiki a sanyaye, tana zuwa ta tsaya ta É—auke kanta daga kallonsa.

Yace "Hmm babu ko gaisuwa 'yan mata?"

Ko kallonsa ba tai ba ta cigaba da kallon Guri É—aya.

"Ki juyo mana in kalli wannan kyakykyawar fuskar tawa mana"

Wani banzan kallo ta watsa masa, tana ji a ranta wannan kalaman daga bakin Sadik suka dace su fito.

"Lokacin yayi da Yakamata ki kwantar da hankalinki, ki tsaya mu fuskanci juna, duk wannan haÉ—e ran da kike na ze canza Komai ba"

Hawaye na zuba daga idonta tace "wai dan Allah me kake so dani ne? Me nai maka haka?"

'ban fahimci me kike nufi ba"

"Meye dalilin da yasa kaje neman Aure gurin iyayena ba tare da amincewa ta ba?"

"Saboda haka Shari'a ta ce ayi, in nemi izinin su kan in zo gurin ki"

"Amma ko da shari'ar tace ai haka, ka san ba zan iya yiwa iyayena musu ba, kuma bani da niyyar wulaƙanta ka, amma zan gaya maka gaskiya wallahi Sunusi ka shiga hakkina, ba ka kyauta min ba"

Murmushi yai yace "Allah ko? Aikuwa sedai kiyi yadda zaki, ko ki haƙuri ko karki yi, mahaifinki ya riga ya bani ke, dan haka gara ma ki haƙura, idan ma saboda wannan ɗan yaron kike min wulaƙanci gara tun wuri ki cire shi daga ranki, idan ma baki cire shi ba ni zan cireki daga ransa"

"Ba zaka iya raba Soyayya ta da Sadik ba, saboda haÉ—in Allah ce, shi ka É—ai ze iya warware ta, idan kuma ka nace seka rabani da shi ka aureni, ni kuma zan barka da Allah yai ma hukunci dai dai da abunda kai mana"

"Wannan kuma iyayenki zaki samu ki gayawa, bani ba"

Wani irin malolon takaici ne ya tokarewa Farhan a zuciyarta, dan ba ta ƙaunar duk wani dalili da ze sa a ci mutuncin iyayenta.

Juyawa tai ta shiga gida, ta samu soro ta zauna ta saka kuka.

Huzaifa ne ya zo ze tafi, yaga Farhan a durƙushe tana kuka.

Cikin tsananin tausayinta Huzaifa yace "Farhan lafiya kuwa? Wani abun yai miki?"

Cikin hanzari ta É—ago, dan bata san Huzaifa ya zo gurin ba, tai saurin goge hawayenta tace "bakomai fa, har zaka tafi?"

Huzaifa cikin damuwa yace "haba Farhan, duk da babu wata tazarar shekaru a tsakanin mu, amma ni ba wanda zaki ɓoyewa damuwa bane"

Kawai ta kuma fashewa da kuka.

"Kiyi haƙuri Farhan, na san ba kya son Sunusi ko?"

Farhan ta jinjina masa kai da sauri.

"Kiyi haƙuri, wallahi ni kaina bana ƙaunar wannan Sunusin, amma dan Allah ki dena kuka, insha Allah ba me miki Auren dole, dan sam baku dace da shi ba, amma ki dena kuka"

Ta share hawayen ta tace "insha Allah na dena, Nagode sosai Huzaifa, ka gaida gida".

Sunusi kuwa harya bar ƙofar Gidan, ya haɗu da Abban Farhan yana dawowa gida.

Yana ganin Abban Farhan, ya zube har ƙasa yana gaishe shi.

Abba yace "A'a Alaramma, kwana biyu ka ɓuya"

Sunusi yace "wallahi Abba ina nan, Yanzu ma daga gidan nake"

"Ahh to Masha Allah, kaje gurin Farhan É—in kenan?"

"Eh naje" yai maganar yana ɗan sosa ƙeya, alamar da Magana.

Abba yace "ya dai ko akwai matsala ne?"

"Eh to Abba kusan akwai É—in kenan zance"

"Subhanallah, matsalar menene?"

"Eh wato Abba, ita Farhan ɗin ce na kasa gane kanta gaba ɗaya wallahi, da farko dai ta amince tana sona, to kuma katsam se naga wani ya kawota gida a mota, nai mata Magana amma naga kamar hankalinta yafi karkata kan shi wancan me hannu da shunin, kuma ma dai yarone ƙarami shine nace dan Allah Abba ai min rai, tunda an riga an bani ta dena kula wancan ɗin, ina jin ba daɗi a raina"

Jimm Abba yai, dan gaba ɗaya jikinsa yai sanyi da jin wannan maganar ta Sunusi, Farhan ba ta taɓa nuna masa ba ta son Sunusi ba, ko akwai wanda take so ba, amma babban abunda yafi ɗaga masa hankali be wuce zancen wani na kawota a mota ba.

Abba yai ajiyar zuciya yace "shikenan, bakomai ka kwantar da hankalin ka, zanje in shawara da mahaifiyar ta, zan ga abunda ya dace ayi haƙuri dan Allah"

"Bakomai Abba, sannan dan Allah kar ai mata faɗa, bana son ranta ya ɓaci a dai nemi wata mafita daban"

Abba ya murmusa yace "shikenan, kar ka damu" ya jiya jiki a sanyaye ya nufi gida.

Huzaifa kuwa da ya fito ze tafi, ya hangi Abba da Sunusi a wajen ƙarshen layi, Sunusi ya gurfana yana Magana, hakanan jikinsa ya bashi, wani abun Sunusin ke kitsawa.

Sunusi kuwa yana ganin Abba ya wuce yai ƙwafa yace "Ai naga alamar kan aikin nan da nake ya kammala se ina yi ina zagowa ta bayan gida, in ba haka ba Yarinyar nan za ta bani Matsala.

Abba haka ya shiga gidan jikinsa a matuƙar sanyaye, dan be taɓa tunanin faruwar hakan daga Farhan ɗin ba, ya yarda da 'yarsa matuƙa da gaske.

Umma daga yanaisa ta gane Akwai matsala, amma duk yadda tai ta tambayar sa Lafiya, ƙin gayamata yayi, dan be san ta in da ze fara mata bayanin ba, gashi ta fishi girmama abu irin wannan mussaman akan Farhan.

Sir Nazir yana nan hankali ya kasa kwanciya, saboda fargabar abunda ze taso, gashi ta dena É—aga wayarsa gaba É—aya.

A makaranta su Haseena suke zancen sunje sun duba Lilly, ta rame Sosai saboda rashin lafiyar da tai.
Sir Nazir ya sa aka kira masa Yasmeen, ya tambayeta ya jikin Lilly, tace "jikinta da sauƙi, amma har ƙarin jini a kai mata, amma da jikin nata da sauƙi"

Yace "ok to shikenan, jeki"

Bayan tafiyar Yasmeen ya kuma ɗaukar waya ya kira Lilly, Amma ta ƙi ɗagawa.

Yasan ba abunda ya faru, dan da tabbas in wani abu ya faru zuwa yanzu da an danƙo shi.

Kasancewar an kammala jarrabawa, ya sa Farhan na gida, saboda hutu za'ai, ga damuwa tayi mata yawa, ga ba abokin hira balle ta É—an faÉ—i matsalar ta taji daÉ—i.

Jiki a sanyaye Farhan ta fito daga ɗakinta, zata ɗebi abun karin kumallo ta tarar da Hajiyar nan maƙociyar su ta shigo yiwa Umma sallama zata tafi umara.

Farhan na ganin mutuncin Hajiya Sosai, har ƙasa ta durƙusa ta gaisheta Kamar yadda ta saba.

Cikin sakin fuska Hajiya ta amsa tace "ke Farhan ko gaisheni ba kya É—an shigowa kiyi, ni dama Ummanki ta barmin ke, 'yan jikokin nawa duk sunyi Aure ba me zuwa in da nake"

Murmushi Farhan tai, tana ƙoƙarin miƙewa.
Chapter 28 · 0% Book details