Sashe 78
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sadik ya shafi sumarsa yace "Aikin gama ya gama Yarinya, ko na sakeki kin zama bazawara ba zaki taɓa komawa yadda kike ba, kuma ma abun tausayin da kike bani, 'ya'ya biyar ne a cikin na ki, Allah sarki shikenan zaki zama Mama, ga 'ya'ya na binki ba karatu ba gayu, inje a kuma Auramin wata gallaliyar Yarinyar.
Kuma wallahi ki kai wani ganganci akan cikin nan sena ɓata miki rai"
"Na shiga uku ni Asma'u, wallahi ka gama dani, Allah seya saka min wallahi, kuma nasan mutuwa zan yi, ta ina 'ya'ya biyar za su zauna a cikina, shikenan ratuwata ta zo ƙarshe"
Sadik ya rungumota jikinsa yace "Allah sarki, nima kin bani tausayi wallahi, É—an yaron mijinki ya jefaki a wani hali sorry baby" yai maganar yana mata dariyar mugunta.
Yayin da gefe guda kuma zuciyarsa cike take da zullumin yadda ze fuskanci wannan ƙalubalen da ke gabansa, na bayyanar ciki a jikin Nana.
COOL CE
Contact me at 07063065680 to subscribe, at affordable price or visit Arewabooks to purchase.
Kafin Lilly da mamanta su ƙaraso tuni major yai umarni aka ja motar, aka barsu a nan, ƙarshe se daidaita sahu suka hau zuwa gida.
Suna tafe Lilly na kuka, a fusace Mummy tace "ki rufen baki ko in jefaki kan kwalta dan uwarki, kalli halin da kika jefamu a ciki, ƙanƙanuwarki da ke wai kin san ki bi namiji har yai miki ciki ki zubar, turr da halinki" haka Mummy tai ta mata masifa har sukaje gida.
Suna zuwa gida suka shiga falo, suka tarar da Major yana muzurai, a fusace yace "ban ce karki dawo min da Yarinyar nan gida ba? Tun wuri ki san in da zaki kaita ta barmin gida"
"Wasa ma kenan, ai kaima kasan wannan Magana faÉ—a kawai kake, ina ka ke so in kaita?"
"Duk in da ki ka ga ya dace, tun da a garin sokoncin ki da hauka, kika bari harta ke yawo baki sani ba, kina uwa 'yar ki na bin maza amma kika gaza ganewa"
A ƙufule Mummy tace "haramun ne kai a matsayinka na ubanta idan ka gano hakan? Ina ni da ita duk a ƙarƙashin ka muke, alhakin kula da mu a wuyan ka yake, ko kuma ni kaɗai Allah ya ɗorawa Alhakin kula tarbiyyar yaran?, su sauran da nai tarbiyyar su har su kai Aure, ka taɓa zaunar da ni kace ka gode naiwa yaranka tarbiyya ba su lalace ba, se yanzu dan wannan ta lalace zakace inje in san yadda zan da ita, 'yar ka ce kaima zaka iya ɗaukarta ka kaita duk in da ka ga dama"
"Ni kike gayawa haka?"
"Na gaya maka ɗin, akan me zaka ɗaga min hankali? Bari in tuna maka wani abu da kake ƙoƙarin mantawa, barewa ba ta gudu ɗanta yai rarrafe, a yawace yawacen aikinka kai meye ba kai ba, ko ka ɗauka ka ci bulus ne? Better get back to your sense, ka ɗau mataki a cikin hankalinka, kar ka yanke hukunci cikin fushi abunda ba kai zato ba ya biyo baya"
Sororo Major yai yana kallon Mummy, tai wucewarta É—aki ta bar su a tsaye shi da Lilly.
Wata uwar ƙwafa yayi, sannan shima ya bara falon, Lilly ta durƙushe a gurin tana kuka, tabbas koma meyafaru ita ta janyo shi, ta ɗora laifin kacokan akanta, take taji nadamar abubuwan da ta aikata suka baibaye ta, shikenan yanzu ba ta da sauran wata kima da mutunci, ta zubar da su a dalilin banza da na wofi, yanzu Allah ne kaɗai yasan matakin da mahaifinta ze ɗauka a kanta.
Abbas mussaman yaje har gida yai sallama da baban Farhan, Abba baze manta da Abbas ba, duba da irin taimakon da yai lokacin rashin lafiya Farhan.
Abba cikin fara'a ya saki fuska suka gaisa da Abbas, yake ce masa "Nikam yaushe rabon da in ganka, harna manta"
Abbas yai murmushi yace "da yake watana kusan goma bana gari, naje ƙaro karatu ne"
Abba yace "Allah sarki, Allah ya yi jagora ya dafa"
Ya amsa da Ameen Sannan ya É—ora da cewa "dama Abba na zo muyi magana ne akan lamarin Farhan"
Jiki a sanyaye Abba yace "wani abun tai maka ne?"
"A'a ko ɗaya, se dai in baka manta ba tun bayan rashin lafiyar ta, na baku shawarar sa ido akanta da kula da ita, sedai bayan dawowata banji daɗin yadda na tarar da ita ba, tun kan in tafi na lura akwai damuwa me yawa a tare da ita, tana cikin yanayi na son wani, ku kuma kuna yunƙurin aura mata wani, kuma ba zata iya yi muku musu ba.
To a yanzu ma nai interview da ita, na gano meye damuwar ta, sedai ina son ku bani haÉ—in kai gurin ceto rayuwar ta"
Abba yace "tayaya kenan?"
Abbas yace "Masha Allah, dan Allah Abba duk da halin da take ciki a yanzu, na san baya muku daɗi, amma dan Allah banda tsangwama, kar a tsangwameta, ayi haƙuri a ja ta a jiki, yana daga cikin abunda ta rasa harta faɗa soyayya me zurfin gaske, rashin ja a jiki, da ba ta samu a gida ba shine taje ta samu a waje, wanda ya jefa ta cikin soyaya RUƊIN ƘURUCIYA"
Abba ya nunfasa yace "hakane, dama ni ban tsangwameta ba, ina mata Addu'a ne Allah ya shirya ta, dama matsalar daga mahaifiyarta ne, kuma ita ma tayi nadama yanzu"
Abbas yace "Masha Allah, sannaan abu na gaba shine, Abba nace idan ba damuwa ina Neman wata alfarma guda É—aya a gurinka"
Abba yace "wace alfarmar ce haka?"
"Ina son ka bani Auren Farhan"
Abba ya kalli Abbas yace "Malam Abbas ka san me kake faÉ—a kuwa? Ba ka ga yadda ta koma bane, ba Farhan É—in da ka sani a baya bace ba fa"
"Eh Abba na sani, ina son in temakawa rayuwarta ne, dan Allah ka duba lamarin"
Abba yai shiru Sannan yace "komai nufi ne ne Allah, bana son sake maimaita kuskuren da nai a baya, amma ka nemi yardarta in dai daga gareka ba wata matsala kuma ta amince shikenan"
Abbas yai murmushi yace "nagode Sosai Abba"
Abba yace "bakomai, ka gaida gida"
Su kai sallama da Abba, sannan ya nufi gidan Hajiya, se a lokacin wata fargaba ta zo masa, dan be san ya abun ze kasance ba, Hajiya za tai murna da hakan ko kuma zata ce ba ta yadda ba.
Abba ya je wa da Umman Farhan abunda suka tattauna da Abbas Umma tace "Anya kana ganin wannan lamarin ze yuwu, Yarinyar nan ta riga ta ɓata rawarta da tsalle, ba na jin mahaifiyarsa ma za ta yadda"
Abba yace "to, ni dai ba ni da ta cewa, na bar komai a hannun Allah, Allah ya iya mana"
Umma tace "Ameen".
Ranar gardaution É—in su Tasleem, ana party a makaranta, ana ta kaiwa ana komowa, yara cikin shiga kala kala, ta arziki da ta banza, se cahsewa ake, ana ciye ciye da shaye shaye, labari ya karaÉ—a makaranta an kama sir Nazir, amma babu wanda ya san dalilin kamun nasa.
Ba zato babu tsammani 'yan sanda sukai dirar mikiya a makarantar, aka kama Director makarantar, da principal, aka kama 'yan ajinsu Lilly, a nan 'yan Sanda su kai katarin kama su Nas da ƙwayoyi a jkinsu ranar graduation ɗin, dan haka aka tattarasu duk zuwa police station.
Aka kori kowa gida, aka garƙame makarantar.
A station director se masifa yake, wai anci zarafinsa ana neman a ɓata masa sunan makaranta, an kama shi da ɗalibansa anci zarafinsa.
Aka shiga da shi wani Office, da sauran malamai aka zo da Lilly da malam Nazir, aka warware abunda yake faruwa a tsakanin su, ga kuma su Nas da aka kama da ƙwayoyi a wannan shekarun nasu.
Nan aka shiga kiran iyayen yara suka cika police station, yadda aka faÉ—i da yadda Lilly ta lalace, ya bawa iyaye da yawa tsoro da Mamaki.
Su kansu su Haseena da Yasmin akace ba'a yadda da su ba, se anje anyi musu screening tun da tare suke karance karancen, a nan allura ta dinga tono garma, dan a É—aliban har da masu Implant a jikinsu, banda wanda aka samu da ciki, banda masu É—abi'ar neman jinsin su (Subhanallah).
Baban Lilly yace "baze bar wannan rashin Albarka ba, se an bi masa haƙƙin 'yar sa.
Labari ya karaɗa gari, akan irin ta'asar da aka bankaɗo a wannan makarantar, wadda tai ƙauran suna akan makaranta ce ta yaran masu hannu da shuni.
Abbas ne a gaban Farhan, ya zuba mata idanunsa, ita kuwa ta É—auke kai gefe se tura baki take.
Fitilar wayarsa ya sa ya haskata, ta sa hannu ta rufe fuskar ta ta saboda hasken fitilar.
"Farhan" ya kira sunanta. Ƙin kallonsa tai gaba ɗaya.
"Farhan, meyasa ba kya so na?"
"Ni na ce maka ba zan yi Aure ba"
"Meyasa? Kin fi so ki cigaba da rayuwa a haka?"
Farhan tace "meyasa zaka auri ragowar wasu, ba ka cancanci Auren yarinya iri na ba"
Abbas ya nisa yace "ke kika cemin ba kya zina ai, kuma ma ni ba wannan nake dubawa ba, makomar rayuwar ki nake dubawa"
"Kai in ba abunda nake kenan ba, a ina kake tunanin nake samun maƙudan kuɗaɗe? A banza maza za su dinga bani kuɗi ne ba wani dalili, ai maza ba kwa abu dan Allah se da dalili"
Abbas yai murmushi yace "kar ki mana kuÉ—in goro mana, ke dai kawai ki ce min har yanzu Sadik kike so"
Take ta haɗe rai ta kalleshi tace "bana buƙatar ko sake jin sunan sa a ratuwata, dan Allah kar ka kuma sako min zancensa"
"To in ba Sadik kike so har yanzu ba, meyasa ba kya so na? Na miki tsufa ko?"
Murmushi tai tace "kai nagartaccen mutum ne, me tausayi da sanin yakamata, ni kuma 'yar shaye shaye ce kuma.....