← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 115

Sashe 95

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadik yai ajiyar zuciya yace "dan Allah ki dena damuwa masoyiya, Wallahi kin rame dan ki kwantar da hankalinki"

Nana tace "ai kwanciyar hankalinka its ce tawa, hankalina baze kwanta ba idan kana cikin damuwa"

Sosai take bashi tausayi, ta damu da shi sosai be san yadda zataji ba a lokacin da taji batun ze ƙara Aure.

Sadik yace "kije ki shirya, zan zo muje yawo Yanzu, ni zanyi magana da Mother"

Nana tace "to Besty, kuma ga Sahal na gurin Mother"

Yace "bakomai, zamu bar mata shi a gida ne"

"Ok, bari inje in shirya".

Sadik ya samu guri ya zauna, har Mother ta fito daga gurn Abba ta koma sashinta, Sadik yabi bayan Mother, ta waiwayo ta ganshi a bayanta tace "ya dai kake bina?"

Sadik yace "magana nake so muyi Mother"

"To ina jinka"

Sadik yace "Mother, na san Abba ya gaya miki maganar da mu kai da shi, na batun ina son ƙara Aure, kuma kinga dama ke kika ce zaki sake min wani Auren, dan Allah Mother ka bani goyon baya in ƙara Aure"

Mother tace "rufen baki, lokacin da na so ka bani haɗin kai har a kai ga yi maka wani Auren, ba ƙasa ka watsamin a ido ba? Ka bani kunya sega yarinya da ciki, ni yanzu na dena jin haushinta tausayin ta nake ji, yarinya ƙarama ga ɗawainiyar ka ga ta ɗanka kuma dai-dai gwargwado tana kula da kai sosai, kuma kawai yanzu se ka zo da wata maganar banza, dudu guda nawa kake zaka riƙe mata biyu, dama ba kwa tare ne da sauƙi, amma guda nawa kake da za kai batun ƙara Aure?"

Sadik yace "dan Allah Mother ki fahimce ni, na aikata wani kuskure ne a baya, na fara ajiye 'ya'ya, ba zan so hakan ta faru a kansu ba, dan Allah Mother ki bani goyon baya"

"Wallahi ba zan baka ba, tunda ba ka da hankali, fita ka barmin É—aki"

"Dan Allah Mother"

A fusace tace "zaka fita ko sena zageka, na ɗuɗɗura maka Ashar". Jiki a saɓule Sadik ya fice daga ɗakin Mother yana tunanin mafita.

Daga ƙauye aka kira Abba, wai Hakimi yana son ganinsa, abun ya ba shi mamaki sosai da sosai, da fari yayi tunanin ma ko jikin Hakimin ne ya tashi, seda yaje ya tarar da shi jikinsa da sauƙi sannan hankalinsa ya kwanta.
Hakimi yace da Abba "Na san zaka yi mamakin kiranka da nai, ba wani dalili ne ya sa na kiraka ba, shekaranjiya Sadik ya zo garin nan, Masha Allah ya kawo mana abun arzikinsa fal, Allah yayi albarka"

Abba yace 'ikon Allah, ai bamu san ya zo bama"

Hakimi yace "hakane, ya kawomin ƙara ne, ko ince ya zo neman alfarma ne"

Abba yace "wace Alfarma kenan ranka ya daÉ—e?"

Hakimi ya ɗanyi tari sannan yace "kan in tafi kai tsaye ga abunda ya sa na kiraka, lokacin da Sadik ya zauna a garin nan, na sha kama shi yana waya da Mace, yana iƙrarin idan har ta Auri wani ba shi ba ze iya hallaka shi, da kunne na naji wannan cikin dare, na fuskanci yana soyayya da wata yarinyar a wannan shekarun nasa, kuma da alama yarinyar Aure za'ai mata, to da ai haka yaje yai mana wannan gangancin da yanayin ɗabi'un sa, da abunda kakarsa ta gayamin ta gani a game da shi, hakan yasa na ɗau Nana na ba shi, a gefe guda na Aura masa Nana dan sanin Nana marainiya ce ina sa ran in suka zauna guri ɗaya, su sassautawa juna wannan ƙiyayyar da suke wa juna, kuma tunda 'yar uwassa ce ina sa ran ya riƙet da amana ko ba ranmu, banji ta bakin kowannensu ba na yanke wannan hukuncin.
Sadik ya zo min da cewar yana son ya ƙara Aure, kuma dama na bashi wannan damar a lokacin da na Aura masa Nana, nace idan yana da buƙata a nan gaba ze iya ƙara Aure, dan haka kar ku kalli yarintarsa tun da yana so, ba ku san dalilinsa na cewa yana son ya ƙara ba, ya min bayanin komai na fuskance shi, kuma na bashi goyon baya ɗari bisa ɗari, ya gayamin yana ƙaunar Nana yai min alƙawarin baze wulaƙanta ta ba, dan haka dan Allah ku bashi dama, kuyi haƙuri da yadda Allah yayi shi, ku bashi dama yayi, kuma zan bada kuɗi a sai masa isashen gida da ze ishe su, Allah yai musu albarka gaba ɗaya"

Abba be ji daɗin yadda Sadik ya kawo ƙararsa ba, kuma har Hakimi ya bada goyon baya, Abba bece komai ba, Hakimi yai tai masa nasiha, se Yamma sannan ya tafi Kano.

Sam be yiwa Sadik zancen ba, sedai ya fita daga harkarsa gaba É—aya.

Nana tana shirya Sahal tana masa wasa tace "bari in shiryaka in kaiwa Abba kai, yaga wankan juma'arka, ko É—an kyakykyawan Babansa"
Se shiriritar ta keyi, dama Talatu ce take zuwa taiwa Sahal wanka, Nana kuma ta shirya abunta tana shirya shi, tana masa hira kamar yasan me take faÉ—a.

Sadik ya samu Abba a falonsa ya gaishe shi, da ƙyar Abba ya amsa masa, jiki a sanyaye Sadik yace "Abba dan Allah laifin me nai maka?"

Abba yace "tambayata ma kake ko Sadik? Bayan kaje ka kaiwa Hakimi ƙarata na hanaka Aure ko? To shikenan kaje kai abunda ka ga dama"

Sadik yace "dan Allah Abba ka fahimce ni, Wallahi ba dan na ɓata muku rai nayi ba, Abba ina da dalilin da yasa nake son ƙara Auren nan, Farhan na fara so a rayuwata, saboda ita nai jumping na gama secondary School, dan Allah Abba ku amince in Auri Farhan, wallahi muna son juna sosai, Kasan lokacin da na Auri Nana ba sonta nake ba, Farhan na fara so".

Gani yai Abba ya ƙurawa ƙofa ido, Sadik na ɗaga kai yaga Nana a tsaye da Sahal a hannunta, hawaye harya cika mata ido, alamar taji duk abunda ya faɗa, juyawa tai cikin hanzari har tana tuntuɓe, hawaye na zuba daga idonta.
A falo ta haÉ—u da Mother, Mother tace "ke kula mana zaki yar da yaron hannunki"

Jiki na rawa ta miƙawa Mother Sahal, tai waje da gudu.

Sadik kuwa dafe kansa yai yace "ya salam, Wallahi ina son Nana ma, ina ƙaunarta sosai amma.....

Abba yace "oho maka dai, ya rage naka"

Mother ta shiga falon Abba tana faÉ—in "me a kaiwa yarinyar nan ne? Naga ta fito hankali a tashe tana neman ta yar da yaron hannunta?"

Abba yace "tambaye shi, bayan ƙarata da ya kaiwa Hakimi, akan in bar shi yai Aure, shine ya samu ƙwarin gwiwar tsayawa a gabana yana cemin dama wata yake so aka aura masa Nana, shi yana da wadda yake so, ita kuma ta ji, ina sane na ƙyaleka ka cigaba da zuba, kaga gara ka dena munafutarta, duk ta ɗaga hankalinta akan kana cikin damuwa baka walwala, kai kuma ba ta tata kake ba, wata kake so".

Gaba ɗaya Sadik ya rasa in da ze sa kansa, Nana ba taji maganar har ƙarshe ba, ya san da iya abunda taji za tai masa hukunci.

Jiki a sanyaye ya baro part ɗin Abba, ya tafi BQ, sedai ya daɗe a tsaye a bakin ƙofar shiga, be so labarin ƙara Aurensa ya zo wa Nana a haka ba, tabbas ya san za ta ji babu daɗi, jiki babu ƙwari Sadik ya shiga, ya tarar da ita a ɗaki, tana ta aikin kuka.

Jin motsinsa ya sa ta É—ago ido ta kalleshi, abunka da me manyan idanuwa, tuni idonta yai jawurr saboda kuka fuskarta duk ta kumbura.

Sadik ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, yace "dan Allah Nana ki fahimce ni, ki tsaya in miki bayani"
Ɗaga masa hannu tai tace "har akwai wani bayani da za kai min bayan wanda naji? Sadik ba sona kake ba ka dinga gayamin kana sona, har na yadda da kalamanka, ka yaudareni da kyautatawa da tausayawarka, ina tunanin nayi kuskuren ƙoƙarin bijirewa zama da kai a matsayin miji da nai da farko, na ɗauka na Auri mijin marainiya, ka san ba ka sona meyasa ka ɓoyemin kake nuna min soyayya, an tauyeni na Aureka maimakon a shekaruna ace ina makaranta, ka ɗau damuwa ka ɗorawa ranka, nima ka sani a damuwa, ashe duk dan kana son ka ƙara Aure ne, duk da ƙanƙantar shekaruna, da ka min bayani zan fuskance ka, ba ka se shiga damuwa dan kana son ka ƙara Aure ba, Sadik ko matan duniya duka zaka dinga aurar huɗu kana saki kaje ka Aura, amma ka tabbatar ka sakeni, se ka Auro duk wadda ka ke so, dan ba zan zauna da wanda ba ya  so na ba"

Sadik kamar ze kuka yace "Wallahi Nana ina sonki, baki ji ƙarshen zancen bane, meyasa zance ina sonki bayan ƙarya nake"

"Wai meyasa kake son rainamin hankali ne? Sadik da kunne na fa naji abunda kake faÉ—a, ka nemi wadda zaka rainawa hankali ba ni ba" ta sauka daga kan gadon ta koma É—aya É—akin.

Sadik ya dafe kai, ya rasa wani tunanin Yakamata yayi, ai kome za'ai sedai ayi, amma ba ze yadda ya rabu da Nana ba, duk da son da yakewa Farhan, Nana ba abar wulaƙantawa bace, kuma ya cancanci ta nuna fushinta akan abunda taji yana faɗa, ya san zata ji babu daɗi, amma Baze iya haƙura da Farhan ba ma.

Wunin ranar sam Nana bata shiga harkarsa ba, se kuka da take, ba abunda yake dukan zuciyar ta irin yadda da kunnenta taji yana cewa ba sonta yake ba, ko Abinci ba wanda ya iya ci a cikinsu.
ÆŠaki ma daban daban kowa ya kwanta, ta bar shi da Sahal, cikin dare ya dinga tsala masa kuka, haka yaita faman rarrashinsa, bacci kam duk ba su rintsa ba.
Chapter 95 · 0% Book details