Sashe 98
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da azahar rana tsaka Sadik yaje gidansu Farhan, se ya haÉ—u da Huzaifa ze shiga gidan ya tsaya suka gaisa da Huzaifa sannan yace masa 'dan Allah cikin gidan nan zaka shiga?"
Huzaifa yace "eh ciki zan shiga"
Yace "dan Allah in ka shiga ka cewa Farhan tana da baƙo a waje"
Huzaifa yace "to zan gaya mata insha Allah"
Shigarsa babu daÉ—ewa se ga Farhan ta fito, tana waige waige dan ta ga wake nemanta da tsakar ranar nan?.
Tana ganin Sadik ta haÉ—e fuska tace "lafiya?"
"Ba Lafiya ba, meyasa kike guduna kike wulaƙanta ni haka? Kulluma na zo seki ƙi fitowa"
Cikin ko in kula tace "idan na zo me zan maka? Sadik na gaya maka kar ka sake zuwa ƙofar gidan mu, na gaya maka, idan kuma ka cigaba da zuwa ka dinga ganin wulaƙanci da rashin mutunci da ga gurina kenan"
"Yanzu kina ganin wulaƙanta nin shine mafita?"
"Shine babbar mafita a gurina, a gurinka kuma dena zuwanka shine mafita, kowa yayi rayuwarsa".
"Kamar Sadik naji kina cewa?" Cewar Abba da yake ƙoƙarin fitowa daga cikin gida.
Gaba ɗaya suka sha jinin jikinsu, Sadik ya rusuna yana gaida Abba, Abba ya ƙare masa kallo tabbas ba ze ta ɓa mantawa da Sadik ba, ya sha ganinsa dan baze manta zuwan da yai kawowa Farhan kati ba.
"Kai ne Sadik É—in dama?"
Sadik yace "Eh nine Abba"
Abba yace "kaine dam silar duk wannan wahalar da ɓacin rai da na shiga akan Farhan? Kai ne ka dinga hure mata kunne da soyayya, ka tafi ka barta ta shiga mummunar rayuwa irin wannan, ni na ɗauka wani babban mutum ne ma ashe kaine, kaje ba zance maka komai ba, amma idan abunda kai dai dai ne, zaka gani a ƙwaryar shanka, ka tafi ka barmin ƙofar gida kar in sake ganinka, na samu wani ze Aureta ba ze yuwu ka zo ka cigaba da hure mata kunne bax
Sadik kamar ze yi kuka yace "Abba dan Allah".
Abba ya ɗaga masa hannun yace "ka ɓace min daga ƙofar gida kar in sake ganinka". Abba ya ƙarasa maganar yana nuna masa hanya.
Gaba ɗaya se jikin Farhan yai sanyi, Abba ya kalleta yace "ke kuma wuce gida, idan na kuma ganin ya zo kin fita sena ɓata miki rai, mara zuciya kawai" Farhan jiki ba ƙwari ta koma cikin gida.
Sadik kuwa kifa kansa yai a saman motarsa, ya rasa abunda yake masa daɗi, a hankali ya buɗe ƙofar motar, yana ƙoƙarin shiga, a dai dai lokacin kuma Sunusi ya kawo kai, ƙiƙifta ido Sunusi ya shiga yi dan tabbatar da dagaske Sadik yake gani ko gizo ne, sedai kan ya gama murje idon, Sadik ya bawa motar wuta ya bule Sunusi da ƙura.
Kusan a guje Sunusi ya ƙarasa makarantar su, yana son tabattar da in abunda ya ganewa idonsa gaske ne.
Mahaifin Lilly yaje har can in da ya kai ajiyar ta, saboda rashin lafiyar da akace masa tana yi, an kaita Asibiti amma ba wani cigaba.
Ya tsorata sosai da ganin yadda ta rame, tai duhu tana ganinsa se kuka, tana "dan Allah Daddy ka yafemin ka maida ni gida, na tuba ba zan sake ba Daddy" abunka da É—a da mahaifi, se tausayinta ya kama Major, dan haka yace da ita ze taho Kano.
Ita kanta Mummy ta tsorata da ganin yadda Lilly ta koma, fara ce jawur Lilly amma ta koma duk tai wani iri.
Ƙanwar mahaifin Lilly Anty Sa'a, tana gidan Major ya dawo da Lilly, tayi mamakin ganin yadda Lilly ta koma, nan ta tambayi ba'asin abunda ya sa aka kai Lillyn can kudancin Nigeria gidan abokin Major aka barta.
Mummy ba ta ɓoyewa Anty Sa'a komai ba, ta gayamata abubuwan da suka faru.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku kaico na".
Mummy tace "Anty Sa'a, lafiya kike wannan salatin haka?"
Anty Sa'a ba ta amsa ba ta kalli Lilly tace "Lilly, waye ya kawo muku irin wannan litattafan kuka karanta?"
Lilly bata ɓoye mata ba, ta gayamata yadda ƙawarsu Yasmeen ke tura a wayar yayarta ta turo musu su karanta, ko ta kawo musu su karanta a aji.
Anty Sa'a ta kalli Mummy tace. "Yanzu kuna me kuka bar yarinya ƙarama kamar Lilly da wayar hannu ba tare da kuna bibiyarta ba"
Mummy tace "wallahi saboda Assigment, kusan kullum cikin É—aukar tawa wayar take, wai tana Assigment shiyasa ya siya ya bata dan ta bar min tawa".
Anty sa'a tace 'ban taɓa dana sani a rayuwata ba kamar na yau, ina da sa hannu a lalacewar Lilly, kuma ba ita kaɗai ba yaran mutane da yawa, nayi nadama a lokacin da bani da halin gyarawa, mugun abun da na aikata ya riga ya cika duniya".
Mummy tace "to ai ni ban fuskanci abunda kike nufi ba".
Anty Sa'a ta share hawaye tace "irin litattafan da su Lilly ke karantawa, irinsa nake rubutawa, na fara wannan salon rubutu ne saboda ina burin in suna a harkar rubutuna, na fara irin wannan rubuce rubucen, ba irin nasihar da ba aimin ba, amma na ƙi na kasa denawa, katsam Allah yaiwa ɗaya daga cikin wadda muke irin wannan rubutun rasuwa, kuma rubutun be dena yawo a duniya mutane na la'antar rubutun ba, a gaɓar da jikina yai sanyi na dena, se gashi ashe 'yar ɗan uwana ta lalace ta sanadiyyar irin wannan rubutu, kaico na ba zan taɓa yafewa kaina ba wannan abu da na aikata, dan Allah ku yafemin, nayi ƙoƙarin sauke duk irin rubutun a kafafen da na san na ɗora, amma wasu site ɗin ba ni da bani na ɗora ba bani da ikon saukewa, dan Allah ku yafemin".
Mummy tai shiru ta rasa abunda yake mata daɗi, ta rasa abunda za tace, sam ba taji a zuciyarta zata iya yafewa Anty Sa'a ba, duk da kasancewar ta ƙanwar mijinta.
Sadik kam ya koma salihin ƙarfi da yaji, ya zamana rana zafi inuwa ƙuna, Amma duk da hakan sam baya jin ze iya janye ƙudurinsa na Auren Farhan, kuma mahaifinta ma ze cigaba da bibiyarsa yana sa ran ze haƙura ya ba shi ita. Da wannan ƙwarin gwiwar ya kuma tunkarar Abbansa yana masa magiya "Abba dan girman Allah ka fahimceni, kar ka duba ƙanƙantar shekaruna, tun da ka ga na dage akan lallai ina son yin Auren nan, Akwai dalilin hakan"
Abba yace "to meye dalilin naka?"
Sadik yace "Abba, a bar batun tona dalilin ni dai dan Allah ka amince min, Wallahi ba zan wulaƙanta Nana ba, ina sonta, Amma Farhan na fara so a rayuwata, ban san yadda a kai al'amura suka juye min ba"
"Yanzu kai Sadik ban da haÉ—ama ya za kai da mata har biyu, kai kanka haryanzu da saura ba ka gama hankali ba, ya za kai da mace har biyu saboda rashin hankali"
"Au Sadik haryanzu ba ka janye maganar Auren nan ba ko? Duk faÉ—a da cin mutuncin da nai maka a kai, kaje kai abunda ka ga ya dace da kai, tun da kai dai ba É—an Arziki bane, ban isa ince bana son abu ka bar shi ba, Allah sarki Faruk Wallahi da shi ne da tuni ya bar maganar nan, amma banda kai, nayi dana sanin sangarta ka da nai, to the extent da baka jin maganata".
Sadik kamar ze fashe da kuka yace "haba Mother, Dan Allah.....
"Rufemin baki, Aure ko kaje kayi amma ba da yawu na ba, kuma ka nemi wata uwar bani ba, wadda ta isa da kai"
Dummmmm haka Sadik ya ji kansa yayi, cikin jiri ya fara tafiya a hankali, ya bar sashin yana lumshe idonsa, da ya fara ganin duhu.
Nana na zaune a falo, tana yiwa Sahal wasa, tana babana ya fi na kowa, se ɓaɓɓaka dariya yake, yana kallonta tare da miƙa hannu ze kamo fuskarta.
Ba ta ji Sallamar Sadik ba, se ganinsa tai ya shigo yana dafa bango, ɗan binsa da kallo tai dan ta gano ma'anar hakan da yake yi, a hankali ya fara kiran sunanta yana miƙo mata hannunsa.
Tai sauri ta tashi ta ƙarasa in da yake tace "ya dai meke faruwa?"
"Jiri nake ji, kuma duhu nake gani a idona"
Nana tace "Yasalam, ta ya haka?" Ta riƙo hannunsa za tai masa jagora zuwa kujera, kawai ta ga ya faɗi ƙasa!
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680
A gigice Nana ta durƙusa akan Sadik, tana jijjiga shi, se dai ko motsi ba ya yi, kuma idanunsa sun rufe, gaba ɗaya jikinsa yai sanyi.
A guje Nana ta ruga cikin gida, ta nufi shashin Abba, se dai da ta je ɗin kasa magana tayi, se nuna masa hanyar waje take, ganin ta kasa magana ya sa da Abban da Mother suka biyo bayanta dan ganin meke faruwa, suna zuwa suka tarar da Sadik a ƙasa cikin fita hayyaci.
Nan suka shiga rafka salati, Abba yace wa Nana ta bashi ruwa me sanyi a fridge, ta je ta É—akko ta kawo, aka shashshafa masa a fuska, amma be ko motsa ba.
Abba yace wa Nana, maza je ki cewa Sabo ya fito da mota mu tafi da shi Asibiti.
Haka Nana ta kuma kwasa tai waje, taje ta gayawa Sabo saƙon Abba, bayan fito da motar, Sabo da kansa ya ƙarasa BQ suka ɗakko Sadik shi da Abba, suka kai shi mota, ita kanta Mother hankainta a tashe yake.
Abba ya kalli Nana yace "Nana, koma maza gurin Sahal, ki zauna duk abunda ake ciki ma kira ki a waya"
Nana da tuni hawaye ya wanke mata fuska tace "Abba dan Allah ku bari in biku"
Abba yace "A'a maza koma cikin gida". Daga haka ya shiga motar ya rungume Sadik a jikinsa, Mother ta zauna a É—aya gefen suka nufi Asibiti.
Kai tsaye Asibitin da suke da file suka tafi, A emergency aka karɓi Sadik, aka shiga da shi likitoci suka rufu a kansa, dan ƙoƙarin ceto rayuwar sa.