Sashe 42
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rabon Nana da Abinci tun jiya da safe, Inna tayi tayi tai kurarin amma Nana taƙi cin Abinci, har zuwa yanzu ba ta ci Komai ba, ga yunwa ga damuwa nan da nan kanta ya hau ciwo, har da zazzaɓi.
Se bayan Abba ya idar da sallar la'asar ya shirya ze fita, sannan ya zauna a gefen gado, ya kalli Mother yace "Hauwa"
Tace "Na'am"
Yace "Na sani kin sani, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yacewa Sahabban sa, shin bana sanar da ku manya-manyan zunubai ba, Sahabbai sukace gayamana ya ma'aikin Allah, yace da su 'Shirka da Allah, saɓawa iyaye, da kuma shedar zur, Kin sani saɓawa iyaye laifi ne me girman gaske a gurin Allah, sannan kowane mumini ba ya zama mummuni se ya yadda da ƙaddara, me kyau ko akasinta, ɗa baya taɓa girma a gurin iyaye, kamar yadda haryanzu mukewa Usman kallon yaro ƙanƙani har muke zaɓa masa wasu abubuwan game da rayuwarsa, to muma haryanzu hakane, ba'a girma a gurin iyaye, kuma duk hukuncin da suka yanke akan ɗa, in dai be saɓawa mahalicci ba to tabbas be dace ga ɗa na gari ya bijire ba, dan Iyaye ba zasu Cutar da ɗan da suka haifa ba.
Dan haka nake son ki tayani yiwa iyayena biyayya, Kamar yadda ban taɓa yunƙurin ganin kin saɓawa naki iyayen ba, nima ina so ki bani ƙwarin gwiwar da zan bi nawa iyayen, tunda iyayena naki ne.
A dawowar mu kinga abubuwa da kike buƙatar bayani, na zo da Yarinya ba tare da na gaya miki meyasa na taho da ita ba, duk da hakan ba abun damuwa bane, dan ina da hurumin ɗakko duk wanda nake so ya zauna a gidana.
Wannan goron da kike gani, na É—aurin Auren É—anki ne!!!"
A zabure ta kalli Abba tace "ban fahimce ka ba, wanne daga cikin 'ya'yan nawa?"
"Abubakar Sadik!"
"What! Sadik É—in akaiwa Aure?"
"Eh shi ɗin, tun wancan Zuwan da nayi, Hakimi yace lallai in nemawa Nana karatu a ƙasar da Sadik zeje karatu, jiya kuma bayan sallar juma'a ya ɗaura masa Aure da Nana, ban san dalilin Hakimi na yin haka ba, amma koma dai menene nasan dalili ne me ƙarfin gaske, dan haka ina fatan ni da ku mu karɓi hakan a matsayin ƙaddara mu riƙe yarinyar nan kamar tamu, danni 'yata ce kin sani, Hakimi ya gindayamin hatsari me girman gaske, akan idan wani abu ya samu Auren nam be yafemin ba"
Miƙewa Mother tai tace "Ya isa haka, wannan kai kanka ka san ba abune me yuwuwa ba, shikenan ni bani da iko ko martabar da za'a tuntuɓe ni kan a yankewa ɗa na hukunci? Wane irin abune wannan za'aiwa yaron da be san komai ba Aure? Me Sadik ya sani dudu guda nawa Sadik ɗin yake da za ai masa Aure, kuma a rasa wadda za'a aura masa se wannan yarinyar? Shikenan ni bani da iko akan yarana? Sedai ai duk hukuncin da ake so akansu, ko hakan yaimin ko be min ba? Da sake a wannan karon baze yuwu ba"
Dama Abba ya san hakan zata faru, dan haka Abba yace "na biyo miki ta laluma amma naga baki gane yaron rarrashi, kiyi abunda kike ganin shine daidai, nima zan abunda ya dace"
Fuuuu tai waje daga É—akin, ta wuce É—akin Sadik ta tarar da shi akan sallaya alamar salla ya idar, yai shiru yana tunani.
"Kai dama abunda aka ƙullo kenen? Har nake tambayar ka menene kace min bakomai, wato kana sane kaje kace musu Aure kake so ko? Me ka sani a game da Aure? Shikenan ka gurgunta rayuwarka, kazo matsaloli su addabeka ka bi ka tsofe"
"Haba Mother, tayaya kike Tunanin zance sumin Aure, in ma hakane ya za'ai ince A auramin wannan baƙauyiyar, tausyawarki nake buƙata ba wannan faɗan da kike min ba"
Se kuma jikin Mother yai sanyi, ta zauna a kusa da shi tace "kana nufin baka son Auren nan?"
."Mother ya za ai ince ina so, na tsani Yarinyar nan ko ganinta bana ƙaunar yi"
"Shikenan, ka kwantar da hankalinka, in dai wannan ne an gama, dole Auren nan ya mutu"
"Amma Mother, Hakimi yace be yafe ba idan wani abu ya samu Auren"
"Kana son Auren kenan?"
"Mother dan Allah ki dena faÉ—an haka, wallahi bana so"
Tace "in dai baka so ai shieknan, shi Hakimin ai ba ubanka bane da Allah ya isansa zata bika, tsabar son zuciya ne irin nasu, da kuma tasanar da suke min ta shafeku shiyasa aka maka wannan Auren, dan a cusan takaici, zan nuna musu nima 'yar yauce, dan an gaji da wannan abun nasu, ka kwantar da hankalinka kaci Abinci"
Sadik ya jinjina kai cike da jin ƙwarin gwiwa, akan kalaman mahaifiyarsa.
Da Yamma Abba yazo sake duba jikin Farhan, yaga da sauƙi sosai dan har hira sukayi.
Abbas ya shigo É—akin, yana ganin Abba yai murmushi yace "Baba sannu da zuwa"
Abba yace "Yawwa, Sannu da ƙoƙari, muna ta godiya fa Allah ya saka da Alkhairi"
"Ai bakomai, insha Allah zuwa gobe in Allah ya kaimu zamu iya sallamarta, muna monitoring É—in hawa da saukar jininta ne, amma in ba zaka damu ba, ina son muyi magana da kai a Office É—ina"
Abba yace "badamuwa"
Kallon Abbas take, tana fatan Allah ya sa ba zancen Sadik zewa Abba ba.
Bayan sunje Office ɗin, suka ƙara gaisawa, Abbas ya kalli Abba yace "wato Baba, a yanayin jikinta abunda binciken mu ya tabbatar mana shine, damuwa taiwa Yarinyar nan yawa, ko kai a shekarunka idan jininka ya kai kamar nata, dole a ɗoraka akan magani, tayi ƙanƙanta da fara shan maganin hawan jin"
Abba ya dafe ƙirji yace "hawan jini kuma?"
"Yes of course, hawan jini gashi shikansa jinin be wadaceta ba, saboda bata cin Abinci, abu na farko Baba Al'ada ba addini bace ba, babu in da akace dan ka haifi É—a shine na fari kai watsi da shi da lamuransa, Yakamata mahaifiyarta ta ajiye wannan al'adar ta ja 'yarta a jiki ta san meye damuwarta, naso in bugi cikinta inji amma na fuskanci tana da tsananin kunya da zurfin ciki, ko kasan ta rayu tsawon shekara guda da tunanin tana É—auke da ciwon Cancer wanda ba haka bane?"
Abba ya zaro ido cike da Mamaki "Mahaifiyata yakamata ta san wannan, wanda in Asibiti ya kama a kaita a duba a kaita, amma babu wanda ya sani, Mutane masu hali irin na Farhan suna buƙatar ja a jiki da nuna musu soyayya, yadda zasu saki jiki har a dinga jin matsalolin su, idan aka cigab da tafiya a haka sakamakon da ze biyo baya baze daɗi ba, Mutane masu irin personality ɗinta are at risk of having depression, daga lokacin da ta samu depression ƙwaƙwalwata zatai ta gayamata abubuwa ba daidai ba, zata tsame kanta daga Mutane, da tunanin kowama baya sonta, in a kai rashin sa'a za'a iya wayar gari aga ta kashe kanta, ko a ganta a wata mummunar hanya wadda ba'a fata.
Yanzu babban abunda nake ƙoƙarin yi shine, inga ta kwantar da hankalinta, yadda ko bata faɗi meye damuwar tata ba, a samu jininta ya sauka aita sa ido dan Allah"
Abba yai ajiyar zuciya, dan yaji tsoron bayanin doctor Abbas, Abba yace "Nagode sosai da wannan bayanin naka doctor, Insha Allah za'a sa ido a kanta, Allah ya wuce mana gaba"
"Ameen" Abbas ya amsa.
Daga nan Abba ya tashi ya tafi yana tunani daban daban a ransa.
Bayan fitar su Abba kuwa, Anty Uwani ta sa Farhan tai wanka, ta fito tai salla ta bata Abinci, ba wani ci tai ba, Anty Uwani tai mata sallama tace zata gida ta dawo.
Fitar Anty Uwani ba daÉ—ewa, kawai sega Sunusi ya shigo É—akin da Farhan take shi da Huzaifa, Huzaifa se tuttura baki yake.
Nan da nan Ta haɗe rai kamar ba ta dariya, taƙi ko kallon in da yake, yana shigowa ya turare ɗakin da warin hannatarsa me maƙaƙi a wuya.
Huzaifa kuwa juyawa yai ya bar É—akin, dan ya tsani Sunusi shima.
Ya ƙarewa ɗakin kallo Sannan yace "Ya jikin naki?"
"Da ssauƙi" ta amsa a ciki.
"Ki dena Wannan cunkusa fuskar, dan ba abunda ze sauya, a satin nan za'a kawo kuÉ—in Aurenmu"
Ko kallonsa ba tai ba ta É—auke kanta daga kallonsa.
"Hmm yarinya kenan, ai ranar a idona aka ɗakkoki daga gida, wani shinƙimemen ƙato ya ɗakkoki kamar inje in bazar da shi, ai an san ina unguwar saboda tsabar wulaƙanci ni ba a aika an kirani na ɗakkokin ba, se wani zindiƙin ƙato za a kira ya ɗauke ki ina mijinki, wannan ai ba yi bane"
"Karka ƙara kiranka da mijina, na gayamaka"
"Wallahi ko kinƙi ko kin so, nine nan mijinki ke mallakina ce"
"Ke tawace Farhan, babu wanda ze mallakeki seni, duk wanda yai gangancin yin hakan, zan nuna masa abunda zan iya yi akanki" Maganar Sadik ce ta dawo mata, gaba É—aya taji jikinta yai sanyi.
A hankali ta furta "come back to me Prince"
"Me kike cewa ne?" Sunusi yai maganar yana zuri kansa daf da ita.
"Dalla meye hakane, karka sake ka sa jikinka a nawa"
Buɗe ƙofar akayi, wanda yasa Sunusi daidiata nustuwar sa.
"Farhan did they serve your medications?"
Abbas ya shigo yana magana.
Ta girgiza kai alamar a'a, sam be lura da wani Sunusi a gurin ba.
Sunusi kuwa ya gane shi, dan ya kan ganshi a layinsu, yazo gidan Hajiya, sedai yaga Abbas É—in yai masa kwarjini sosai.
Farhan tace "A'a, amma a bari se anjima" ta faÉ—a a Sanyaye.
"Ni, yanzu ne lokacin yi, nasan allura ce ba kya so, sedai kiyi haƙuri, ba kiga because you are so special yasa nake miki allura da baki magani da kaina ba, bana son Nurses suyi miki me zafi"
Tai murmushi ba tace komai ba, yayin da Sunusi ya cika yai fam.
Abbas ya haɗa allura, ya kamo hannun Farhan, ya buɗe canula yana mata, yanayi yana shafa kan jijiyar da canulan take, saboda kar tai mata zafi, amma shi Sunusi se yaga kamar da Iskanci Abbas yake hakan, kuma tai fusuƙi da kai tana kallonsa.
Ya kalli Fuskar Farhan yace "Ai ba zafi ko?" Tai murmushi tace "eh"