← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 115

Sashe 18

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Inna tace bakomai kar ka damu, mahaifiyarku ba zata bari ku zo ƙauye ba, amma duk da hakan da ka faɗa naji daɗi sosai, Allah yai maka Albarka" tai maganar tana jin ƙaunar Faruk, yaron ba dai jin ƙai ba da tausayi, baya son yaga wani a damuwa.

Suka cigaba da hira shi da Inna, yana bata labarin yanayin rayuwar turai.

Nana tai shirin tafiya Makaranta ta zo É—akin Inna tace "Inna zan tafi makaranta"

Inna tace "to a dawo lafiya, ban da biye biyen ƙawaye, banda tsayawa da namiji a waje, a tafi ana sa hannu a hijjabi, banda kalle kalle ko ciye ciye a hanya, kar wani yace miki je kij, banda bin lumguna abi hanya sosai.

Nana se signa ta kewa Inna akan ta É—an tsahirta da zubo wannan jawaban, saboda ga Faruk a gurin, amma ba abunda yai mata zafi se zuba take, tana sake jaddada mata.

Shi Faruk ma abun dariya ya bashi, wai wannan 'yar Nanan akewa wanna jan kunnen, Yarinyar guda nawa take, ana ta wani ta sa hannu a hijjabi, ɗan abunda ke ƙirjin nata be taka kara karya ba, yanzu yake fitowa.

Faruk ya miƙe yace "muje in rakaki Makarantar"

Nana tace "A'a Inna ta hanani jerawa da maza"

Faruk yace "Ikon Allah, Inna duk kin takura mana ƙanwa, ni gashi ban gama ganinta bama, ai shikenan sekin dawo Allah ya tsare ayi karatu da kyau, zan bawa Inna saƙo ta ajiye miki"

Nana tace "to ku gaida gida"

Yace "Ba zaki ce in gaida Sadik ba?" Yai Maganar cike da zolaya.

Nana tace "wallahi bana gaida shi" tai maganar tana fita daga É—akin.

Taje waje taiwa Abba da Hakimi sallama ta tafi makaranta.

Se bayan la'asar sannan sukai harmar tafiya, dan Alhamdilillah jin Hakimi da sauƙi.

Inna tace "ya dai kamata kaiwa kanka faÉ—a Abdullahi, ka nunawa iyalinka mahimmancin iyayenka, kakansu ko a daji yake yakama yaci darajar ya haifeka suzo su duba shi, amma ba su da uzuri ace su kasa zuwa suga jikinsa, dama ziyara ma su zo in da muke wannan mun yafe, tunda ba sa son Zuwa, amma halin rashin lafiya ai abune da Yakamata ace sun san yakamata"

Faruk yai saurin cewa "Ayi haƙuri Inna zamu dinga zuwa Insha Allah"

"Da kai nake Magana?" Inna tai maganar tana kllonsa.

Faruk yace "Allah ya bada haƙuri" yai gaba abunsa yana murmushi.

Seda Inna ta gama mitar ta sannan Abba yace "dan Allah kiyi haƙuri, insha Allah za'a gyara, kuma duk zamu sake dawowa mu duba shi haba ɗaya".

Inna tace "ya dai kamata kasan abunda ya dace"

Yai ta bata haƙuri, daga nan suka kama hanyar komawa gida.

ko da Nana ta dawo daga Islamiyya ta tarar sun tafi.

Nana tace "Inna har sun tafi?"

Inna tace "eh sun tafi, ga sababbun litattafai can, Yayanki ya bayar a ajiye miki, hadda jakar Makaranta sabuwa fil me kyau"

Nana tai murmushi tace "aikuwa nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi"

Inna tace "Ai nan ya zauna ya na min magiya akan lallai se na bar musu ke sun tafi da ke, ni kuwa ba zan iya ba, dan ban yadda da tarbiyyar wannan gidan ba, gidan nan nasu se a hankali"

Nana tace "taɓɗijan, ni ma ba zan zauna a wannan gidan ba, ba zan bisu gidan su ba, wannan masifaffayar babar ta su, me wa mutane kallon banza, ga wannan wawan masifaffafe wanda be san darajar mutane ba"

Inna tace "ke dan ubanki ba ki san kara ba? Ko dan yadda É—an ta ke nuna miki so ai kyayi kara, yanzu idan yaji kina cewa uwarsu me yiwa mutane kallon bamza zeji daÉ—i? kuma ban hanaki faÉ—ar mummunar magana akan wanda yake gaba da ke ba?"

Nana ta ɗan tura baki tace "yi haƙuri na dena, gaskiya dai Faruk ya na da kirki ba kamar wannan me hura hancin ba kamar wani kasa"

Inna tace "i taku dai ke da shi É—in"

"Ai wallahi Faruk duk yafi kirki" Nama ta faÉ—a tana murmushi.

Inna tace "wai ni meye tsakanin ki da Faruku É—in nan? Ko dai son sa kike? Ayi 'yar gida mu huta?"

Nana ta zaro ido tace "taɓ Wannan ne ze Aure ni, kina ganin sa ɗan birni me kyau, me ze da 'yar ƙauye, ƙauyen ma na ƙayau?"

Inna tace "in dai kina son sa ai shikenan, ba wata damuwa"

Nana tace "Inna ya ake jin son ne to?"

Inna tai murmushi tace "a bar wannan maganar, tashi kije ki karɓo zumar ki a gidan kuka, Hakimi ya bayar da kuɗi a kawo miki"

Cikin murna Nana ta tashi tana Allah ka yiwa Kakana Albarka".

Inna ta bita da kallo tana murmushi.

Se bayan magariba sannan su Abba suka koma gida, suka tsaya a masallaci su kai sallar isha'i, Abba yace suje restaurant su ci Abinci, se kusan ƙarfe goma na dare sannan suka dawo gida.

Faruk ya wuce BQ, Abba kuma ya shiga cikin gidan, kai tsaye ya wuce part ɗin sa ya rufe ƙofarsa.

Romeo Sadik kuwa baban Soyayya, yaƙi kula Farhan se wanata yake, har kiran wayarsa tai, amma ya ƙi ɗagawa, amma ya sa hotunan ta a gaba yana kallo, yana murmushi.

Seda Safe sannan Sadik ya san su Faruk sun dawo da suka haÉ—u da Asuba, Sadik yace "Ai na zaci a can zaku kwana da naga dare yayi baku dawo ba"

Faruk yace "A'a ba'a can muka kwana ba, jikin nasa ma da sauƙi sedai duk ya rame sosai"

Sadik yace "Aka bibiya ma ba wata cutar kirki bace, ake ta wannan kwaroroton ba shi da lafiya"

Faruk yace "Wai Sadik Yaushe za kai hankali ne? Nan Abba yai zazzaɓi da mura, har kuka kayi saboda damuwa, yadda fa kake son babanka shima haka yake son nasa, hawan jini ne fa yake damunsa"

Sadik yace "haba dai hawan jini kuma? wallahi na zaci be fi zazzaɓi ba"

"To hawan jini ne, duk ya rame ƙafafunsa sun kumbura"

Sadik yace "Subhanallah, Allah ya bashi lafiya, dole hankalin Abba ya tashi, dan naga hawan jinin nan shike kwashe mana tsofaffin nan, Allah dai ya bashi lafiya, shima ya tsufa ya haƙura da wannan Sarautar amma kamar da sarautar aka haife shi yaƙi haƙura"

"Idan ya sauka daga sarautar kai zaka je ka riƙe masa?"

Sadik yace "Allah ya kiyaye inje in zauna a wannan garin da ko ruwan roba babu, ba wata tsayayyiar wutar lantarki, gari duk se uban shanu da gonaki, ga ƙudaje ha warin kashin shanu, wai ma sarautar dole ce haba, ba abunda ya nema ya rasa da Abba ba ya ba shi, amma yaita wahala da ɗawainiyar mutane, wannan yace kaza wancan ma yazo da tasa matsalar, banda 'yan jarida da ke zuwar masa ba yau ba gobe, faɗan filayen magada duk fa haka Abba yake bada labarin wahalar da yake sha akan sarautar, sekace Dole ya haƙura mana"

Faruk yace "dan ubanka kai meya hana ka ajiye sarautar da akai maka ta yariman Hausawa, har wani taƙama kake wai kai Prince, daga zuwa rakiya ba'a bawa dr. Ba se kai a kaiwa Sarauta, banga uwar da kake tsinanawa a sarautar da a kai maka ba ɗin"

Sadik ya wani gyaÉ—a kafaÉ—a yana murmushi yace "ya ranka, You are talking to Prince, kayi magana da girmamawa mana"

Tsaki Faruk yai tsaki yace "dalla ware, ni zan kwanta saboda a gajiye nake in ka rigani tashi ka shiga cikin gidan, ka miƙamin gaisuwa gurin Mother kan in shiga"

Sadik yace "ok"

Faruk yace "Aff na manta ban gaya maka ba, Inna na gaishe ka, da kuma Nana"

Tsaki Sadik yai yace "Nifa bana son Maganar da ba shikenan ba, wannan tsohuwar yadda ta tsaneni ne za ta ce a gaishe ni, ai ko zan mutu ba zata faɗa ba, wannan Yarinyar kuwa me ɗan kai kamar an roƙo mata ita ma ba zata faɗa ba, ni harka ban haushi da kai zacen Yarinyar nan, dan na manta da ita ma a duniya"

Faruk yai dariya ya wuce É—akinsa, dama dan ya tsokani Sadik ya faÉ—a.

Sha ɗaya na Safe Sannan Abba ya buɗe part ɗin sa ya fito cikin shirin fita, Mother ta tareshi tace "Yallaɓi jiya da kuka dawo kan in fito na tarar ka rufe ƙofa, ya me jiki?"

"Ke kina da damuwa da me jiki ne? Ai mara lafiya na ne, dan haka ni ya shafa ba ke ba"

"Dan Allah Abba ka bar wannan maganar, kuskure ne na yadda nayi shi, amma dan Allah kayi haƙuri"

"Wane haƙuri kuma ban da wanda nake yi Hauwa'u, ai ba tun yanzu kike nunamin wariya akan dangina ba, kallonki kawai nake, dan haka kowa ya riƙe nasa, rashin lafiyar mahaifina ni ta shafa bake ba, dan haka ki ƙyale ni"

Cike da ƙwarewa da iya kissa ta fara kuka tana faɗin "haba Love, dan Allah kayi haƙuri Hakimi ai babana ne nima, bekamata ka dinga nuna ai basu shafeni ba, lokacin da mu kai waya ba su gayamin abunda ke damunsa ba, shiyasa ban zaci babban ciwone haka ba dan Allah kayi haƙuri"

Abba zeyi Magana ya É—aga kai su kai ido huÉ—u da Sadik, dan haka ya fasa ya janyo ta jikinsa, ya fara share mata hawaye yace "is ok ya wuce"

Sadik da ke tsaye yai murmushi, kawai ya nufi Kitchen.

Abba ya san illar dake tattare da bayyanar da saɓanin ma'aurata har 'ya'yan su su sani, saboda hakan na haifar da matsala da rarrabuwar kawunan Iyali.

Ma'aurata na iya faÉ—a su dawo su sasanta kansu, amma muddin 'ya'ya ko iyaye suka sani, ba sa mantawa kuma hakan ya na iya kawowa wannan Iyali matsala.

Dan haka Abba ya wayance, ya bar Komai ya ƙyale Mother Saboda Sadik da ya shigo, dan baze so ya ga mahaifiyarsa na kuka ba.
Chapter 18 · 0% Book details