← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 115

Sashe 46

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Gigicewa Farhan tayi, cikin tsananin tashin hankali ta fara tattaro kalaman kare kanta, duk da ba ta da tabbacin kalaman nata za suyi tasiri a gurin Umman na ta.

"Umma, dan girman Allah, Umma ki saurareni dan Allah"

"Rufemin baki, ƙanƙanuwar ki dake, amma kin san munafunci, kin san ki yiwa namiji wannan kalaman, kin cuci rayuwarki, kuma kanki ki kaiwa ba ki min ba, dama dan babanki ya takura se kinyi bokon nan ne, amma dan tani gara ai miki aure"

Ta ƙarasa maganar tare da ɗauke wayar daga jikin Farhan, ta fice daga ɗkin.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, ya rabbi Allah ka shiga lamarina, Allah ka kawon mafita"

Take taji ƙirjinta saitin zuciyarta yai mata wani irin nauyi, ta dafe gurin hawaye na fita daga idonta.

"Dagaske Sadik ka barni? Shikenan haka alƙawarin ze tafi a banza, za'a Auramin wani bayan ka koyar dani abu me wahalar sha'ani, ka da sa shukar da ba zaka iya bata ruwa ba? Sadik zuciya ta ba zata iya jure tarayya da wani a matsayin miji ba kai ba, Please come back" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka.

Sadik kuwa sam ya kasa murna da wannan tafiyar, an sai masa sabuwar waya da Komai da Komai, Mother ta shirya masa kayansa da ze tafiya da su.

A ɗaki ta tarar da Sadik, yana shirin kwanciya ta nemi guri ta zauna a bakin gadon ta kalleshi tace "Sadik ina son ka buɗe kunnenka da kyau ka saurareni, ba kai ba Yarinyar nan, ba kai ba shiga sabgarta, tai rayuwarta kai taka ina nan zanyi duk me yuwuwa in ga nai Dalilin da zan kawo ƙarshen Auren nan"

Sadik yace "dama ni me ze haÉ—ani da ita, boarding fa za ai kata ni kuma ina hostel"

Mother tace "Yawwa, ai ni ban san da Wannan Maganar ba ma, shikenan ta kwana gidan sauƙi, babu wani dalili da ze dinga haɗaku ma, ka maida hankali kayi karatunka kaji Auta, na san you are gifted, amma kayi karatu da kyau, idan ka kammal karatu da kaina zan maka Aure irin na 'ya'yan gata, in aura maka wadda kake so, dan wannan yarinyar ba ajinka bace, ba tsarar ka ba ce son zuciya ne kawai na kakannin ka yasa su ka aura maka ita"

SADIK yai murmushi yace "shikenan Mother, Allah ya kaimu in gama makarantar Nagode sosai da kulawar ki My mum"

"Mentioned not dirling, am gonna Miss you so much"

"Me too mom" yai Maganar yana rungume Mother da tuni ta fara hawaye, ƙarshe Sadik ne yai ta rarrashin ta, tai masa sallama ta kashe masa fitila.

Har Sadik ya kwanta, yaji wani abu me nauyi ya tokare masa zuciya, wani abu me mahimmanci ya shiga cin zuciyarsa, wata irin damuwa ta baibaye shi, da farko ya danganta hakan da tafiyar da ze da kuma Auren da a kai masa, sedai damuwar da yake ji ko lokacin da aka ɗaura Auren be ji ta ba, ji yake kamar zuciyarsa za ta tsaga ƙirjinsa ta fito, amma ya kasa tuna me ya jefa shi cikin wannan mawuyacin halin haka.

Ya tashi zaune ya dafe kansa, yana jujjuya kan ya na son ya tuna menene wannan abu a zuciyar sa da ƙwaƙwalwarsa ta kasa tuna masa? Amma kansa ya shiga sara masa, the more yake pressing ƙwaƙwalwarsa the more yake jin wani irin ciwon kai.

Ya runtse idanunsa, yana sauraron yadda zuciyarsa ke wani bugu kamar zata fasa ƙirjinsa.

Haka ya lumshe idanunsa, da ƙyar bacci ya ɗauke shi.

Farhan kuwa, jiki a sanyaye taje ta É—auro Alwala ta tada salla, sedai ta kasa sallar da ta fara karatun sallar se ta rikice, zubewa tai akan daddumar tana kuka, tana faÉ—in "Ya rabbi, Ya rabbi" a hankali bacci kuwa dama ba ta yi shi ba sam.

Washegari tun da sassafe, Jidda ta sa Nana tai wanka, ta shiryata amma Nana taƙi karyawa se kuka da take.

Se da Usman ya zazzare mata ido, ya sata a gaba sannan ta ci Abincin.

Bayan ta karya suka É—au hanya zuwa gidan Abba.

Suna zuwa gaban Nana ya shiga faÉ—uwa, dan a falo suka tarar da Mother ta hakimce tana kallon TV.

Tana ganinsu tai murmushi tana musu sannu da zuwa, amma ta na ganin Nana ta haɗe rai, Nana har ƙasa ta durƙusa ta gaida Mother, amma Mother tai mata banza ta na yiwa Jidda Magana.

Usman kansa be ji daÉ—in yadda Mother taiwa Nana ba sam, Jidda tace "Mother ashe abun Alkhairin da ya faru kenan, Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya, Amma Mother ai ko walima Yakamata a shirya mana kafin su tafi"

Tsaki Mother tai tace "ke rabani da wannan shiriritar, dan ban É—au wannan auren wani Auren kirki ba, ya jikin naki ance min baki da lafiya, hankalina ne ba a kwance ba shiyasa ban zo dubaki ba"

Jiki a sanyaye Jidda tace "Jiki da sauƙi Alhamdilillah"

Suna cikin hirar sega Faruk ya shigo shi da Sadik, Nana ta na ganin Sadik gabanta yai mummunar faÉ—uwa sakamakon kallon da yai mata.

Faruk yace "our runaway bride, shine kuka haÉ—a baki da Abba ki ka koma gidan Dr. Ko ai shikenan ya kike?"

"Lafiya ƙalau" Nana ta faɗa a Sanyaye.

Faruk yace "Sadik ga amaryar fa, ai kwa gaisa ko"

Wani uban tsaki Sadik yai, ze wuce É—akinsa.

Dr. Ne ya daka masa wata irin tsawa yace "zo nan, ana maka Magana waka kewa tsaki?"

Mother tace "ya za kai masa tsawa haka, ba dole yai tsaki ba, an samun yaro a damuwa, dole yai tsaki"

Dr. Yace "Mother please, abu Kafin ya faru ake nuna masa ƙiyayya, ko ɗaukar matakin hana faruwarsa, amma wannan ya riga ya faru, karki tsananta ƙiyayya akan lamarin nan daga baya ki zo kiji kunya, ki fita sabgar yaran nan please"

"Ni kake gayawa haka Usman?"

"Mother, I don't mean to say anything bad to you, but Maganar gaskiya ce tunda lamarin nan ya faru kiyi haƙuri dan Allah, ki musu Addu'a"

"Rufemin baki!" Mother taiwa dr. Tsawa.

"Dan ba kai a kaiwa haka ba shine kake wannan maganar ko? Dan kai ka kammala karatu ka samu aiki ka zaɓo matar da kake so ka samu ka Aura, shine shi zaka dinga zare masa ido, dan ba kai aka aurawa 'yar ƙauye ba ko? Aka ɓata career ɗinka da burin ka na karatu ba?".

Jidda ba ta ga abun tada jijiyar wuya da Mother ke yi ba, sema tausayin da Nana ta bata, dan se kuka take, abun da tausayi a dinga nuna maka ƙiyayya a gabanka, ana goyon bayan a wulaƙanta ka.

Jidda tace "Nana, ta shi ki shiga ɗaki kafin Abba ya dawo" sannan ta maida hankalinta kan Mother tace "Dan Allah Mother kiyi haƙuri, gaskiya ba a kyauta muku ba, amma dan Allah kiyi haƙuri"

"Ƙyaleni Jidda, wannan mijin naki be san yakamata ba, ban san me Sadik yai masa ba da yake takura masa haka"

Dr. Ze magana, Jidda ta girgiza masa kai alamar yayi shiru, yayin da Sadik se cin magani yake yana hura hanci.

Shi Faruk dama takaici ne ya hana shi Magana gaba É—aya.

Nana kam a É—akin ma takurewa tai, ta dinga kuka tana tunanin tun a nan kenan, ina ga in sunje can in da ba kowa, Allah kaÉ—ai ya san irin zaman da za suyi.

Khairat ce ta leƙo ɗakin da Nana take, ta kalleta tace "kwaɗayayyiya kawai 'yar ƙauye, hadda kukan munafunci nan kuwa ƙasan zuciyarki murna kike"

Nana ba tace mata komai ba, se kuk kawai da take, dan ba ta da lokacin Khairat a yanzu.

Kusan awa É—aya da zaman Nana a É—aki, Jidda ta shigo tace "Nana ta so mu raka ku airport Abban ya dawo"

Jiki ba ƙwari Nana ta taso, tana ta goge hawaye, Jidda ta rungumota Zuwa falo, Sadik ya rungume Mother yana kuka tana kuka, Allah sarki Nana ita babu me rarrashin ta, Jidda ce take ta bata haƙuri ta na mata Nasiha.

"Zaka zo ka wuce ne, ko kuwa in ƙyaleka ka fasa karatun, in ya so uwarka tai romonka ta cinye?" Abba yai maganar a fusace

Mother tace "Amma dai ai ka bari in sallama da É—a na"

"Ba abunda ya dameni bane, ya zo ya wuce in ba haka na tafi, wallahi se dai ki nemi kuÉ—inki ki biya masa"

Mother har mamakin yadda Abba ya koyi masifa take, Sadik suka fito harabar gidan, suka shiga mota É—aya shi da dr. Da Faruk, Abba kuma suka shiga É—aya shi da Jidda da Nana da Khairat.

Suna tafe Dr. Yace "kai Sadik, dan kut..... Bar ganin a gaban Mother muke ɗazu na ƙyaleka, wallahi ka kula da kanka, idan ka sake ka cuci Yarinyar nan Magana ta dawo kunnen Abba ka san matakin da ze ɗauka ba ze maka daɗi ba, kuma in da zakaje ba idon kowa a kanka, dan haka kaji tsoron Allah ka kula da addinin ka"

Shiru Sadik yai Kamar ruwa ya cinye shi, yana ta kallon gari, yau kusan wata biyar kenan rabon da yabi wasu guraren, kuma gashi daga yau ze tafi wata Duniyar se dai in ya zo hutu kuma.

Khairat da ma gulmace ta sa ta biyo su Nana rakiya, Jidda ta rungume Nana a jikinta, kamar ƙanwarta tana mata faɗa ƙasa ƙasa yadda ba me ji se Nanan.

"Yanzu idan Sadik ya dawo yana sonki, ai kema zaki so shi ko?" Jidda tai maganar a kunnen Nana.

Nana ta girgiza kai alamar a'a.

"Yarinya zaman Aure ya wuce tunaninki, amma idan kina son ya dena miki masifa ku zauna lafiya, kinga yadda nake wa dr. A gida? Kema haka zaki dinga yi masa"

Nana a ranta tace "taɓɗijan, wallahi ba zan zama 'yar iska ba, bayan Inna ta hana maza su taɓa ko hannu na, in na dawo taga na zama 'yar iska ai seta koreni'

"Ya naji kinyi shiru, ko ba zaki iya ba?"

Nan ma shirun Nana tayi, Jidda tai dariya kawai tana É—an dukan bayan Nana alamar rarrashi.
Chapter 46 · 0% Book details