← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 115

Sashe 68

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sam Huzaifa ya ƙi gayawa Umma dalilin da ya sa aka fasa auren Farhan, gaba ɗaya hankalinta ya tashi, ga gida a cike da mutane.

Ana haka se ga su Abba sun dawo, Abba ji yake tamkar ƙasa ta tsage ya shige saboda kunya, ya rasa da wani ido ze dubi wannan al'ummar da su ka tara, ga mutane har an fara ƙananun surutai, saboda yadda Sunusi ya dinga miyagun maganganu akan Farhan, wajen ɗaurin Aure.

Wasu daga mutane suka goyi bayansa, cewar suma sun sha gani ana sauketa a mota, kuma falla fallan motoci na alfarma.
Ya yin da wasu suke ƙaryata abun da Sunusin ya faɗa, suna yabon halayen Farhan, ɗin na tarbiyya da girmama mutane.

Su Abba na dawowa, Abba ya wuce É—akinsa, dan baze iya haÉ—a ido da mutane ba.
Ba kunya Malam Zakari yai musu bayanin cewar an samu mishkila, da haka an fasa wannan biki, abinci da aka dafa, kowa yaci sadaka, Allah ya zaɓawa yarinya Mafi Alkhairi.

Nan aka shiga salati da salallami, gashi Malam Zakari mutum ne me kwarjini, dan haka aka rasa wanda ze tunkare shi ya tambaye shi dalilin hakan.

Dangin Umman Farhan, sukai kanta da tambayoyi "Maryamu dan me za'a fasa Auren nan? A tara wannan jama'a haka kuma ace an fasa, lallai ku mutan birni ba kwa gudun abun Kunya, mu dai kin san da a garinmu ne, ba za'ai haka ba, mu zuriyar mu ba a taɓa wannan abun kunya ba , se akanki da 'yar ki. Yo koma mene ya faru ai ba a fasa biki ba, a rufa a ɗaura Aure haka nan, amma kawai ace an fasa"

Sosai Umma take kuka, dan ba ta da amsar da zata kare kanta da shi a gurin 'yan uwanta.

Malam Zakari ya shigo yana ƙwalawa Umma kira, Umma ta fito ido duk hawaye.

Yace "ai ba kuka yakamata ki ba, ki gode Allah da Allah be sa an bawa wannan shashashan auren 'ya ba, ina ita Farhan É—in take? Ta zo muna son ganinta ni da babanta"

Umma ta goge hawaye tace "ta na can a É—aki, ni ban san abinda ya sameta ba, amma malam meyasa aka fasa auren nan mun tara mutane?"

"Kinga kar ki damu, da wata wahalar gara wata, yaron nan mutumin banza ne mara É—a'a, muje ina yarinyar take"

Umma na sheshsheƙar kuka, ta wuce gaba ta buɗe masa in da Farhan take.

Ana buɗe ɗakin, ta zabura ta shige cancikin saƙo, ta takure kanta sosai.

Malam Zakari ya ƙarasa shiga ɗakin yana faɗin "Subhanallah, Farhan lafiya kuwa?" Farhan ta ɗago jajayen idanunta, ta sauke akan Malam Zakari, wanda tuni idanun na ta suka juye, kamar harare garke.

"Meke damunki?"

"Ni..Ni ku ƙyaleni dan Allah, du...duuuk ku fita ku barni, ba na son ginin nan ya faɗo mana a ka..... Allah ya sa ma dai, ya faɗo mana a ka, kowa ya huta"

Malam Zakari yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, me Yarinyar nan take haka kamar maye?"

Umma cikin kuka tace "Nima ban sani ba, na kasa gane kan wannan lamari"

Gida kam tuni labari ya ba zu, ya cika unguwa cewar an fasa wannan biki.

Sunusi kuwa se da ya ga da gaske, an fasa wannan Aure sannan ya shiga hankalinsa.

Yace wa malaminsu "Malam dan Allah aje a basu haƙuri, ina son Yarinyar nan Sosai wallahi"

Malam Labaran yace "wallahi ba zani ba , lokacin da nake kwaɓarka akan maganganun da kake ai ba ka saurareni ba, kai ga ka kuturu Sarkin zuciya, ba irin halaccin da iyayen yarinya nan ba su maka ba, amma ka rufe ido ka dinga rashin mutunci kana ciwa 'yar su mutunci, ba dani ba ba in da zanje"

Haladu yace "Sunusi ba tun tau ba, na sha ba ka shawarar ka rage wannan saurin fushin, amma ka ƙi gashi nan a banza ka janyo kan ka,da tuni Allah ya rufa maka asiri,kai wuf da zuƙieƙiyar Yarinyar nan, amma baƙar zuciya da taurin kai ya janyo maka.meye a ciki dan ace ka je kai gwaji, in da kasan ka na da gaskiya ai ba abun damuwa ba ne, kuma kamar yadda suka faɗa, 'yar su ba kalar ƙauye bace, ba zata iya wannan wahalar ta ƙauye ba, ka na da kuɗi ka kama mata gida ka ƙi, gashi nan kaiwa kan ka, sedai nan gaba ka ga wani yana morarta, dan kai dai ta maka nisa wallahi"

Sunusi yace "inji uban wa, wallahi yadda ban Aura na mora ba, ba bu me mora, sedai kowa ya rasa, za su gani ai"

"Za su ga me? Ka ga Sunusi ka ƙyale mu su 'ya ta huta"

"Wallahi Haladu ba me hutawa, yadda aka hana ni Aurenta haka za su zauna da ita, dan ba zan bari kowa ya aureta ba, na dinga ɓata lamura kenan, har se sun gaji sun bani mata ta"

"Amma kuwa ba ka da imani, ba ka da mutunci duk halaccin da su kai maka?"

Tsaki Sunusi yai yace zuba ido ka ga.

Nana ta dawo daga makaranta, ta tarar da Sadik a gida, sedai a fuskar sa kawai ta lura kamar wani abu na damunsa, ko dai duk saboda laifin da nai masa ne? Ta tambayi kanta.

Sallama tai, ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

Tace "Friend na dawo" ba kulata ba balle yai mata sannu da zuwa,haka ta wuce É—akinta.

A É—akin ta tarar da kayan siyayyar da sukai jiya a kanti, ba ta bi ta kan kayan ba, ta cire kayan jikin ta tai wanka tai sallar azahar, Sannan ta fito falo.

Sadik yana nan a in da ta bar shi, take Kitchen ta É—akko bredi, ta dafo tea ta dawo ta zauna.

"Friend ka ci Abinci kuwa?" A wannan karon ma be tanka mata ba.

A karo na biyu cikin damuwa tace "Dan Allah kayi haƙuri, na ga fushi kake da ni, dan Allah kayi haƙuri ba zan kuma ba"
Miƙewa yai ya nufi ɗakinsa, ya bar mata falon, dan ya gaji da jin surutun  ta.

Nana ta shiga damuwa sosai, saboda yadda ta ga gaba É—aya ya canza, duk saboda abun da tai masa, ba ta zaci abunda tai É—in ze sa Shi fushi haka ba.

Har dare ba ya shiga harkarta, a É—aki ya gama wuninsa ko fita be ba, kuma ba ta ga alamar ya ci Abinci ba, shi ko Sadii Bayan haushin Nana da yake ji, harda matsananciyar damuwa da be san dalilin ta ba.

Nana harta fara shirin kwanciya, tai tunani a ranta tace "Ni, Nana idan ya kwana da yunwa duk laifi na ne, saboda ni na ɓata masa rai, amma ai nace yai haƙuri" sakkowa tai daga kan gadonta, ta saka hijjabi ta tafi ɗakin Sadik.
Yana zaune akan gadonsa, yai tagumi da hannu ɗaya ya zubawa guri ɗaya ido ko ƙiftawa ba ya yi.

Tai Sallama amma be amsa ba, kai tsaye ta tafi gabansa, ta durƙusa akan gwiwowinta tace "dan Allah dan Annabi Yaya Sadik kayi haƙuri, ba zan kuma ba, dan Allah ka dena jin haushi na"
Shi mamaki ma ta ba shi, bil haƙƙi har ranta haƙuri take ba shi.

Ya fuske yace "karki sake zuwa in da nake, ki rayuwar ki inyi tawa, haka kurum kika ɗagamin hankali na dinga nemanki, kuma dan baki da Kunya, kika dinga gayan magana, wai kin barni da mata inje in ta taɓa su ko?"

Ta ɗan tura baki tace "kayi haƙuri, amma ai gaskiya na faɗa maka, se ka je kai ta taɓa mata, alhalin kuma ka san ba kyau, kuma ni haushi nake ji"

Be san lokacin da yai murmushi ba yace "to meyasa kike jin haushin?"

"Bana son a rubuta maka zunubi, Allah ya kamaka"

"Hakane, kina sona kenan?"

Da Sauri ta ɗago kai tace "taɓ a'a wlh"

"To ai kishi na kike"

"Meye kishin?" Ta tambaye shi ta na tsare shi da ido"

Sadik yace "shikenan, tun da ba ki san meye ba, yanzu ke dai burinki in dena taɓa mata ko?" Ta jinjina masa kai da confidence ɗin ta.

Yace "shikenan, É—akkon wayata akan mirror"

Ba tunanin komai, ta ɗakko ta kawo masa, tana miƙo masa ya sa hannu ya riƙota, ya Ajiye wayar a gefe, cikin zafin nama ya cire hijjabin jikinta,ya kwantar da ita akan pillow, ya ɗora kansa akan ƙirjinta.

Tsoro ya baibaye Nana, tace "Sadik meye haka? Dan Allah ka bari"

Hankali kwance Sadik yace "ai kince in dena taɓa mata ba kya so, ni kuma ba zan iya rayuwa ba tare da nayi hakan ba, kinga se ki maye min gurbinsu"

Cikin rawar murya, da janyo numfashi Nana tace "Wallahi babu kyau, Inna ta hana ni, wallahi tace idan na bari namiji yana taɓani zan lalace, dan Allah ka ɗagani, naji ka cigaba da taɓa matan"

Yai murmushi, tare da saka hannunsa akan cikinta yace "so kike a rubutan zunubin taɓa mata?"

Tana kuka tace "Au so kake a rubuta mana tare ni da kai shiyasa kake taɓa ni, wallahi idan Inna ta san abunda nake kenan, za tai fushi da ni Sosai"
Hawaye take Sosai, Kamar wadda za'a yanka, Sadik yai banza da ita, ya sake kwanciya sosai a jikinta, a hankali yaji yana samun sauƙin wannan damuwar da ke ta ɗawainiya da shi tun safe.
Se da jikin Nana yai laƙwas, bakinta ya mutu, ajiyar zuciya take tana jujjuya ido.
A hankali ya ɗaga ta, ya nufi banɗaki, tana ganin ya shige toilet, ta miƙe ta sakko daga kan gadon tai waje, sedai taji gaba ɗaya jikinta ya mutu, se mita take da ƙananan maganganu ƙasa ƙasa.

A can gidan su Farhan kuwa, Farhan ce zaune tai shiruu, duk da haryanzu a cikin maye take, amma ta na iya fuskantar abubuwan da ke faruwa, sedai ta kasa gane hakane a zahiri, an fasa Aurenta da Sunusi ko kuma mafarki take.
Gefe ga Umma na ta uban kuka, kamar ance mata Farhan ce ta mutu, a ganinta dalilin da ya sa aka fasa Auren, ba wani dalili ne da ya taka kara ya karya ba.
Abba kam ya rasa abunda yake masa daÉ—i, dan tabbas Farhan maye take a wannan lokacin.
Chapter 68 · 0% Book details