← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 115

Sashe 26

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan daban na san Allah ne ya karɓe shi, amma yana raye ina raye a nesanta ni da shi, ba zanji daɗi ba, dan Allah a dawomin da shi"

Abba gyara kwanciyarsa yai, ya juya mata baya, dan ya gaji tun yana lallaɓata za ta sa su fara faɗa.

Lilly da safe miƙewa ta gagareta se da ƙyar, da ta tashi se jiri ya dinga kwasarta, duk yadda taso ta fita falo ta kasa, se kwanciya tayi.

Ganin har wajen sha É—aya ba ta fito ba, yasa mamanta biyo ta taga ko lafiya, ta na zuwa ta tarar da ita a cikin bargo ta rufe kanta.

A hankali ta kai hannu ta yaye bargon tace "Lilly, lafiya kuwa? Meya sameki haka?"

"Mummy bani da lafiya" Lilly ta faÉ—a cikin karkarwa.

"Yasalam, amma baki gayamin ba, meyasameki haka?"

Seda gabn Lilly ya faɗi jin tambayar da Mum tai mata, amma ta basar tace "zazzaɓi nake da gudawa"

"Amma baki zo kin gayamin ba, taso maza muje ki karya mu tafi Asibiti"

Ta kamata da nufin ta miƙe, sedai tana miƙewa tai baya saboda jiri.

Hankali a tashe Mummy ta riƙota tana salati, ta duba jikin Lilly taga jini tace "jinin meye wannan kuma a jikin ki?"

"Mummy period nake, yana min rushing Sosai, tun jiya haka yake zuwa"

Gaba É—aya Mummy ta rikice, ta kama Lilly Zuwa banÉ—aki, ta taimaka mata ta gyara mata jikinta, ta sa kaya ta É—auketa zuwa Asibiti.

Idon Lilly harya nuna alamun ƙarancin jini, a yadda Lilly tai musu bayani, tace zazzaɓi tayi na kusan sati biyu se gudawar kwana uku, dan haka ba wanda ya kawo waccan ta'asar da tayi.

Nan likita ya hauta da faɗa "ke dan shirme kina zaune ba lafiya kina nema ki kashe kanki, meyasa zaki zauna tsawon lokaci da larura ki ƙi faɗa"

Mummy tace "nima abun ya bani mamaki, ya za'ai ace tsawon wannan lokacin, baki da lafiya ki kasa faÉ—amin, salon babanki ya dawo yace ina sane na barki ba lafiya"

Lilly dai tai shiru, tana jin yadda kanta ke cigaba da juyawa.

Nan da nan aka bata gado aka kwantar da ita, aka É—ebi jinita dan yin gwaje gwaje.

Nan aka gano yadda jininta yai ƙasa, dan har tana buƙatar a ƙara mata jini, saboda yadda jininta yai ƙasa.

Gashi duk gwaje gwajen da a kai mata sun nuna lafiyarta ƙalau, se 'yar malaria kaɗan a cikin jininta.

Mummy ta fita waje dan kiran Mahaifin Lilly ta sanar masa halin da ake ciki.

Likitan da ya duba Lilly ya shigo, ya kalli yadda ruwan da aka samata yake shiga jikinta a hankali.

Ya ƙarasa gaban gadonta ya kalleta yace "Fatima, duk teses ɗin da akai miki sun nuna ba wani abu da yake damunki, malaria da ke jininki ma ba ta kai ace tayi tasirin da zaki rasa jini haka ba, ki gayamin tsakani da Allah, meke damunki?"

Shiru tai tana binsa da kallo taƙi magana.

"Magana fa nake miki"

"Ni ba abunda yake damuna, kawai zazzaɓi nai da gudawa" tai maganar cike da ƙosawa.

"Amma jinin da kika zubar yayi yawa, se fa an ƙara miki jini"

"Nima ban san meya sameni ba" ta faÉ—a idonta na cikowa da hawaye.

Yace "ok shikenan, Allah ya baki lafiya"

Ta amsa da Ameen.

Bayan fitar doctor, ta lumshe idanunta, ta tuna Nazir na can na hutawarsa, ita kuwa gata tana faman wahala tsakanin rayuwa da mutuwa.

Me aikin su Lilly kuwa, ta shiga ɗakin Lillyn dan gyara mata, ta tarar da duƙunƙunen nan bedsheet da kayan Lillyn kaca kaca da jini, abun ban tsoro.

Tai shiru tana tunani, ta san Lilly ta fara period, amma wannan Jinin yayi yawa ace na al'ada ne ya ɓata guri haka.

Haka ta je ta zuba kayan a washing machine ta Wanke, tana cigaba da mamakin wannan jini haka.

Nazir Kuwa tun daren jiya ya kuma kiran Lilly yaji bata É—auka hankalinsa ya tashi, ya rasa in da ze sa kansa, bacci ma ya gagare shi yi, se kaiwa da komowa yana tunani, ya kira harya gaji amma wayar bata shiga.

Da safe kasa zuwa makaranta yayi, dan yana cike da zullumin ko wani abune ya faru da ita, kar Asirin sa ya tonu.

Allah ya temaki Sadik an ɗan rage wannan takurar da ake masa, mussaman akan cin Abinci, sedai fa babu hanyar fita, dan duk wani yunƙuri da ze ido na kansa ana kallonsa.

Se dai ya auri zaman É—aki, kullum yana É—aki a zaune, idan ya fito to salla za'a je.

Yau da daddare yana kwance yana kallon ƙaramar wayarsa, wadda gidan cajin yai ja alamar kowane lokaci zata iya ɗaukewa.

Yau kusan kwanki huɗu beji muryar Farhan ko Mother ba, dan ma ƙaramar wayarsa akwai riƙe caji sosai.

Gaba É—aya ba bu lambar wanda take shiga.

Ya duba agogo kusan ƙarfe goma da rabi na dare, amma zuciyarsa ta dinga azalzalarsa ya kira Farhan, ya Danna lambarta ya fara kira, yai ƙuri ya zubawa screen ɗin wayar ido.

Be san wayar ta shiga ba, se jin muryarta yai yai can ƙasa ƙasa ta daki dodon kunnuwansa "Assalam Alaikum"

Se da yai nannauyar ajiyar zuciya sannan ya ce "wa'alaikum salam" daga nan kuma yai shiru.

Cikin sassanyar muryarta tace "kana lafiya?"

"Kin manta dani ko?"

"Ya za'ai in manta da kai, kasan wayarka ba ta shiga"

"Hakane, ya Makaranta"

"Lafiya ƙalau ya gidan, ya kowa da kowa"

"Ƙyaleni da wannan gidan, meyasa baki bacci ba?"

"Karatu nayi, kuma na zauna tunaninka"

"Allah sarki matar Sadik, wallahi nima duk kewarki ta isheni, ina son in ganki"

Murya a Sanyaye Farhan tace "nima ina son in ganka am missing you so much"

"Kinga wayata ma ta kusa É—aukewa saboda rashin caji, ban zaci wayarki zata shiga ba, but Alhamdilillah tunda na samu wayar ta shigo, ina fatan dai ba wata matsala ko?"

Se da Farhan ta É—anyi jimm, dan ta so tai masa maganar Sunusi, amma ta basar tace "ba wata matsala se guda É—aya"

"Matsalar menene?"

"Ina so in ganka"

Sadik yai murmushi yace "Nafi ki son mu haɗu, se in dinga jin kamar kafin in dawo wani ze ƙwacemin ke"

"Ba wanda ze ƙwaceni, sedai ina fatan ka dawo da wuri, saboda idan kana nan zan fi samun ƙwarin gwiwa, rashin ka a kusa nima yana sani karaya"

Haka kurum Sadik yaji wasu hawaye masu É—umi, suna zirarowa gefen idonsa.

"Farhan, ina sonki sosai, ni na san son da mukewa juna ba RUƊIN ƘURUCIYA bane, Allah ya cika mana burinmu"

"Nima ina wannan fatan, bana son wata Magana ta kuma tasowa tsakani na da Sunusi, shiyasa na damu ka dawo"

"Insha Allah ba wani abu da ze faru, ke tawace, wayata zata É—auke Farhan se kuma in Allah yayi na samu caji, kimin Addu'a Allah yasa in dawo gida nan kusa"

"Insha Allah zaka dawo nan kusa, I love You"

Sadik yai murmushi yace "sake faÉ—a inji, in kika fadi kalmar nan ji nake kin tafiyar da mafi yawan damuwata, ina ma kina kusa dani kika faÉ—a, in kalli É—an bakin nan son raina"

Murmushi Farhan tai tace "good night"

"Good night ko, am missing Your body warm and sweet fumes, just want kiss you again"

Duk da matsananciyar kunyar da Sadik ya bata, amma hakan be hana ta jin wata kasala, da kuma jin yadda take missing É—in sa ba.

Farhan tace "Seda safe, kaga mun fara exams, gobe in Allah ya kaimu da wuri zan tafi makaranta"

Sadik yace "Na sani, bari in zo mu kwanta tare"

Seda Farhan ta buÉ—e baki jin abunda Sadik ya faÉ—a, bata san meke damun Sadik yau ba.

"Ya ki kai shiru?"

"To me zance?" Ta faɗa cikin shagwaɓa.

"Ba kya son in tayaki kwanan? Aikuwa tare zamu kwana yau, hug your pillow, you will feel me with you"

Murmushi kawai Farhan take, tana jin sabon salon soyaya a gurin Sadik, duk da yadda yake magana a hankali zaka san a cikin damuwa yake dan a muryarsa kawai taji yadda take É—auke da damuwa.

"Ba kice komai ba"

"Naji, ka kwanta kai bacci"

'kona kwanta ba na iyawa seda kyar, kinga in da nake kwana kuwa? Haryanzu ban saba ba"

"Zaka saba ne, lumshe idonka in maka addu'a kayi baccin"

Be kai ga lumshe idon ba wayarsa ta É—auke.

A hankali ya lumshe idanun nasa, hawaye na cigaba da zirarowa daga idonsa, wanda shi kansa be san takaimaimai na menene ba.

Ya ajiye wayar, ba tare da ya buɗe idon ba, yana jin yadda zuciyar sa ta cunkushe, ga matsanancin shauƙin son kasamcewa da Farhan da yake bijiro masa.

A hankali ya janyo pillown da ke gefensa, ya rungume shi gam a ƙirjinsa, yana sauke ajiyar zuciya.

Sunusi ke zaune akan wani buzu, se rubutu yake a jikin wani allo, gabansa wuta naci a jikin wasu ƙananun itace.

"Sunsi wai akanwa kake wannan aikin ne haka?"

Sunusi ya ɗago kansa yai murmushi yace "Haladu kenan, ai tunda ka ga nayi wannan zaman, aikin nayi ne, zazzafan aiki zanyi farraƙu zanyi"

Haladu yace "wa za kaiwa Farraƙun?"

"Wannan yarinyar mana da malam ya tambayar min aurenta, se nema take ta wahalar da ni, ashe wani ɗan tayin yaro take so, yake hure mata kunne, shine nake son in nuna musu ba a ja da ƙolo"

Haladu yace "haba mutumina, a sassauta musu mana, kasan wannan aikin yayi zafi da yawa kai musu wani dai daban ba wannan ba"

Sunusi yace "inaa, ai Wannan ɗin dai zan musu, naga kanta yana rawa ne, gara in saita ta tun da wuri, se tayi dana sanin wulaƙanta ni, kuma aikin da zanyi akan Yaron nan na gaske zanyi, yadda gobe in ance ya ƙara baze ƙara ba, zan kwashi kwanaki ina yi"

Haladu yace "to ai shikenan, Allah ya dafa"

Sunusi yace "Ameen"

Lilly kam likita yace se ta kwana a Asibiti, saboda a cigaba da ƙara mata ruwa.

Da yamma Mummy ta koma gida dan harhaÉ—o kayan da zasu zauna a Asibiti kafin a sallame su.

Lilly tace a taho mata da wayarta, zata gayawa ƙawayenta dan su sanar ba ta da lafiya a makaranta.
Chapter 26 · 0% Book details