← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 115

Sashe 29

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya tace "Ni kam ko baki da lafiya ne naga duk kin rame"

Farhan take taji kamar ta fashe da kuka, dan marabarta da mara lafiya kaɗan ne, amma tace "A'a Hajiya lafiyata ƙalau" Farhan ta ƙarasa maganar muryarta na rawa.

Hajiya tace "tashi kije, naga ke ba son Magana kike ba, ni wallahi Umman Farhan da ina sauran É—a da be Aure ba da nace muna kamun Farhan, ni ko a masu Auren ma in yi wani amarya da ita, ina son Farhan wallahi"

Umma tace "Allah sarki, ai an mata miji, É—an lokaci kawai ake jira a fara Maganar Aure"

Hajiya tace "Allah sarki, ashe an rigamu to Allah ya tabattar da Alkhairi, na so ace cikin iyalina ta shigo, Farhan akwai nutsuwa"

Suka cigaba da hirarsu da Umma, yayin da Farhan ta koma ɗaki ta zubawa kayan karin kumallo ido, ta kasa ci se zafi da ƙirjinta ke mata.

"Yaya wai kije inji Abba" maganar ƙninta ce Amira ta dawo da ita hankalinta, haka nan taji gabanta ya faɗi, saboda wasu lokutan kiran Abban ba ya wuce zancen Sunusi.

Kamar kasar da ta haɗiyi ƙwai, haka Farhan ta tashi ta tafi ɗakin Abba.

Umma ma na zaune a É—akin Farhan ta shiga ta zauna tace "Abba gani"

Ya kalli Farhan yace "Farhan magana nake so muyi da ke, kuma ina son ki gayamin tsakani Allah"

Gaban Farhan ya faÉ—i, tace "to Abba"

"Farhan kwanaki an cemin ana kawoki a mota, amma kince min 'yar Makarantar ku ce, na ce miki bana son biyewa yaran masu kuÉ—i, Amma an kuma tarata ance min wani ne yake kawoki a motarsa.

Gaban Farhan ya faÉ—i, wane munafukin ne wannan? Rabon da Sadik ya zo an do shi wata na biyu kenan bama yanan, amma an samu wanda ya samu Abba ya gaya masa.

"Farhan waye yake kawo ki a mota?"

"Abba Sadik ne" ta faÉ—a kai tsaye.

"Waye Sadik" Abba ya tambaye ta.

"Wanda suka zo suka kawomin invitation ɗin bikin yayan su, shi da ƙanwarsa, motar gidan su ce, idan anzo ɗaukar su ne muke tahowa tare, kuma na dena biyosu tunda kace min baka so, nika ɗai nake tahowa gida"

Abba yace "to, ba a shedar ɗan yau, ba zan gazgata abunda kika faɗa ba, kuma ba zan ƙaryata ba, sedai ina sake jaddada miki Farhan kiji tsoron Allah, ki tsare mutuncinki, ki kula da kanki Farhan 'ya mace ce ke, kije shikenan"

Farhan ta tashi jiki a sanyaye, ta bar É—akin.

"Nifa na fara tsorata da wannan lamuran, abu tun ana waiwai to maganin kar ayi kar a fara, kawai kacewa yaron nan ya fito, ni in babu hali ma kawai a haƙura da karatun nan, ka aurar da ita"

Abba yace "Nima ina wannan tunanin, zanwa Malamin nasu Magana kawai su turo a kawo kuÉ—in, muga abunda yakamata ayi"

Farhan kuwa tana tsaye a ƙofar ɗakin, a kunnenta taji Abba yana faɗin ze karɓi kuɗin Auren ta a hannun Sunusi.

Jikinta na rawa ta ƙarasa ɗakinta, ta na zuwa ta durƙushe, ta nannaɗe a cikin hijjabi tana faman kuka.

Kamar yadda Abba ya yanke shawara shi da Maman Farhan, washegari yaje ya samu malamin su Sunusi.

Ya tarar da shi da Almajirai, Yana ganin Abba ya taso yana murmushi, suka koma gefe suka gaisa, Malam yace "Malam Mahmud, ina fatan dai lafiya?"

Abba yace "lafiya ƙalau, dama ba wani abu bane, magana ce akan Farhan da Sunusi".

"Eh to ya ake ciki?"

Abba yace "ka san yanayin zamanin nan da muke ciki, da kuma halin É—an yau, shine nace idan ba damuwa Sunusi ya fito kawai ya kawo kuÉ—in Aure"

Malam yace "Alhamdilillah, amma gaskiya naji daɗin wannan magana ta ka sosai da sosai, ubangiji Allah ya ƙara girma, zanyi Magana da shi Sunusin, muje can garin nasu a tattauna da magabantasa se ya fito, Nagode ƙwarai da karamcin ka, Allah ya nuna mana lokacin Auren"

Abba ya amsa da Ameen, daga nan su kai sallama.

Fafur Abba ya fututtuke ya hana Mother Zuwa in da Sadik yake, tun tana damuwa tana kuka harta dangana ta saba, dan Sadik ya kusa watanni biyu a garin nan, ba tare da ta sake sa Sadik É—in a idonta ba.

Takanas su Nas sukaje har gida, dan kaiwa Sadik ziyara amma aka sanar da su baya gari, Faruk ne ya gaya musu, Amma be gaya musu in da Sadik É—in yake ba.

Allah ya temaki Farhan Tunda Mubarak Babba su kai arangama da Sadik ba ta sake ganinsa ba, dan haka ta manta da batun Mubarak Babba.

Lilly kuwa ga warke sumul kamar ba tai rashin lafiya ba, dan har zata fara zuwa Makaranta cikin hutu ai mata jarrabawar da ba ta samu tayi ba.

Ranar farko da t fara zuwa ta haÉ—u da Sir Nazir a makarantar, yana fama da marking É—in takaddun

Se da gabansa ya faɗi da ya ganta, duk ta rame sosai da sosai, sedai ta ɗanyi ƙalau da ita, ko in da yake ba ta kalla ba ta shiga sabgogin ta.

A wani aji aka ware su, ita da wasu É—alibai, wanda ba su samu damar yin jarrabawar ba.

Se shiga yake yana fita yana son samun hanyar da ze mata Magana, amma abu ya gagara.

Seda ta gama exams É—in ta fito sannan ya samu ya biyo bayanta yana mata Magana.

"Wai dan Allah Nazir me kake so ne? Me zan maka?" (Ashsha, ya rasa wannan darajar da girmamawa ta malami da É—alibi saboda abunda ya aikata"

"Haba Lilly, kin dena ɗaga wayata gaba ɗaya na biyoki kuma kin ƙi saurarata"

Cikin tsiwa tace "in É—aga wayarka in ce maka me? Bayan ka cuceni ka zalunce ni Allah ne yai da sauran kwanana na gaba da yanzu wani zancen ake ba wannan bax

"Lilly ki dena É—aga murya dan Allah kar wani yaji"

"To wanin ma yaji mana ina ruwana?"

"Lilly ni ki ke wa haka?" Yai maganar yana nuna kansa da yatsansa.

Kawai kuma se taji tausayinsa ya kamata.

"Koma me nai ai kai ka janyo min, se da aka samun leda biyu na jini, dole raina ya ɓaci"

"Amma bisa amincewar ki koma mene ya faru, kuma ke kika bani damar nema mana mafita, se kuma ki dinga wulaƙanta ni dan ina binki?"

"Ni ba wulaƙanta nai ba"

"To girmamani ki kai?"

Tai shiru tare da sunkuyar da kai.

Cikin sanyin jiki yace "Tun da abun nan ya gifta a tsakanin mu nake jina cikin damuwa, amma kin kasa fahimtar hakan, nasan mun aikata Babban laifi, Amma dan Allah ki dena min haka"

"Shikenan naji"

"Shikenan kim ji kuma? Ba zaki ce Komai ba?"

"To me zance?" Ta faɗa a ɗan shagwaɓe.

"Nayi kewarki sosai Lilly"

"I miss you too"

"Ba wani ba ki missing É—i na ba"

"Wallahi nayi missing É—in ka, wahalar da na shiga ce yasa naji haushin ka"

Yace "to Yanzu fa?"

"Ya wuce" tai maganar tana murmushi.

"Yawwa Love, Allah ya ƙara lafiya muje restaurant mu ci Abinci tare mana"

"Daga yin salaryn in cinye maka kuÉ—i, karka damu"

"A'a kinga ban samu na zo duba ki ba, saboda ina tsoron ko kin faÉ—a a gida, muje mu ci Abincin kan azo É—aukar ki"

"Shikenan muje" suka jera suka fita daga cikin Makarantar.

Khairat na zaune a falo, ta harɗe ƙafa tana kallon Bollywood, se ga wata 'yar makarantar Islamiyyar  su ta kawo mata ziyara.

Khairat ta dinga murmushi, ta kalli ƙawarta tace "Yasmeen, waye ya gaya miki ina nan?"

Yasmeen yace "gidanku naje, aka cemin kina Gidan su Prince, ni wai ina gayen nan, tunda ya bar school É—in nan sau É—aya ya zo, ko gurin budurwar ta sa ba ya zuwa?"

Khairat tace "ke yana ƙauye fa"

"Wane irin ƙauye kuma?" Yasmeen ta tambaya cike da Mamaki.

"Yana ƙauye gidan kakanninsa, sun riƙe shi a can"

Yasmeen tace "taɓ, Wannan gayen a ƙauye abun ba arziki, kin san yarinyar da yake so 'yar ajinmu ce"

"Haba dai, Farhan ne sunan nata ko wa?"

"Eh, haka sunan ta, wata 'yar talakawa sam bata waye ba"

Khairat tace "Na santa, tare muka kai mata invitation É—in bikin dr. Ya nace yace se ita yake so, in ya tafi karatu dai kowa ya huta"

Yasmeen tace "hakane, amma meyasa ba zaki ba shi shawarar ya nemi budurwa wadda take tsarar sa ba, me ze yi da wannan?"

"Ke kin san kuwa waye Sadik? So kike ya min rashin mutunci ko? Ko da wasa mutum ya kushe ta ba ki ga yadda ake kwasheta da shi ba, balle wata Shawara, ke nifa before am the one crushing on him, but now ya min yarinta kuma halinmu ba ze zo É—aya ba, kawai na bar mata shi naga yadda yake hauka a kanta, ni ina jiran in samu wani handsome É—in ne"

Dariya suka yi, Faruk yai Sallama falon, suka amsa gaba É—aya.

Faruk yace "Khairat, Mother ta fitan ne?"

"Eh tun É—azu ma, ta daÉ—e da fita gaskiya"

A hankali Yasmeen ta furta wow, ta kalli Faruk tace "ina wuni?"

"Lafiya ƙalau ya kike?"

Tace "Lafiya ƙalau"

Faruk yace "ke Khairat baƙuwar taki ko ruwa ba zaki bata bane?"

Cikin shagwaɓa Khairat tace "yanzu fa ta zo, zan bata ai"

"Ba wani nan, baki iya saukar baƙo ba" ya ƙarasa Maganar tare da barin falon.

"Wow, Khairat wannan ma É—an uwan Prince ne?"

"Eh É—an uwansa ne ba kiga suna kama ba?"

"Kai amma naga wannan fari, gaskiya yafi Prince kyau"

Khairat tace "haba da faÉ— kike, dan dai wannan fari ne tas, Sadik kuma be kaishi haske ba, amma duk 'yan gidan nan ba me kyan Sadik"

Yasmeen tace "wayyo Allah, ammm da Allah kice ina gaise shi"

Dariya kawai Khairat tai, ta canza hirar.

Bayan tafiyar Yasmeen ne Khairat tai shiru tana tunani, tunda ta san ba zata samu Sadik b, Ai Faruk shi yafi dacewa ta sa a gaba, saboda shine nan da wani É—an lokaci ze iya yin Aure.

Sunusi ne a tsaye a bakin wani ruwa, da yake ta zuba gudu ga iska na kaÉ—a ruwan sosai, ga duhun dare se hasken farin wata da ha gauraye gurin.
Chapter 29 · 0% Book details