← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 115

Sashe 33

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankaɗe Nana yayi, ta zauna a ƙasa daɓas, tare da dafe kuncinta da ke mata wani irin Azabar zafi, zanin nata ma ya gagare ta riƙewa, yana neman ya kwance gaba ɗaya.

Inna ta kalli Sadik tace "me kai mata haka?"

"Na sha gayamata ta kiyayeni, amma taƙi gani take ƙarya nake, shiyasa na dake ta"

"Kuma shine dukan saboda tsabar rashin ta ido ka biyo ta har É—akina daga ita se zani ka daketa saboda kain' dai fitsararrene ba ka da kunya, daga ita se zani fa, da zanin ya faÉ—i fa, ka ganga tsirara?"

Sadik ya waigo ya kalli Inna yace "to meye a ciki? Wannan har mace ce? Aba kamar an daki gwangwanin madara, wannan ai bata wuce 'yar yaye ba, ƙwaila ce kuma ni ba abunda ya dameni kenan ba, zuwa nai dan in koya mata hankali"

Baki Inna ta buɗe kamar wata shashasha ta bi Sadik da kallo, wato har ya san wata ƙwaila da wadda ba ƙwaila ba.

"Allah ya sakamin, azzalumi mara imani, wallahi ban yafe maka ba, Allah yasa ai maka abunda ze baƙanta maka rai kamar yadda kai min"

Ko a jikinsa, yana jin ta ya bar É—akin,ko waigowa be ba, saboda atleast ya rage haushin da ke cunkushe a ransa.
Nana kam sosai ta cigaba kuka, har fuskarta ta jawur saboda ta maru, ga shedar yatsunsa kwance akan kyakyawar fuskarta.

Inna ta kalleta tace "ince ko dai be miki komai ba?"

Cikin kuka tace "Inna fa marina yai har sau biyu"

Inna tace "to ina ruwana da marinki yayi? Ban sha gayamiki ki kiyayi yaron nan ba? Sam ba shi da ta ido, da ya miki tsirara ai da ya gama cutarki"

"Inna wallahi na tsane shi, dan Manzon Allah a maida shi gidansu kan ya kashe ni, ba wanda ya taɓa marina seshi wallahi Allah ya isa"

"Ba zaki dena wannan surutan da kike ba, in kuma jin bakinki, ke ganinki ma da yai daga ke se ɗaurin ƙirji be dame ki ba"

"Wallahi marin da yai min yafi zafi, ni Wallahi na zata ma zanin ya faÉ—i"

Duk da yadda Inna take a ƙule, seda taji tausayin Nana, Saboda yadda fuskarta ta koma jawur kamar ɗanyen Nama.

Riga Nana ta zura, ta fice daga É—akin zuwa turakar Hakimi.

Tana zuwa ta tarar da Sadik a turakar Hakimi a zaune, da alama Magana suke.

Yana daga abunda Hakimi ba ya son gani, ganin damuwa a fuskar marainiyar jikar sa, saboda yana matuƙar tausayinta.

"Ya akayi ne? Kukan me kike na zaki Makaranta bane?" Ya jero mata tambayoyin.

Jikin Hakimi taje ta zube tana kuka. Sadik kuwa ya basar kamar ma be santa ba.

Hakimi yace "Ke da kakar taki ne?" Nana ta girgiza kai alamar a'a.

'to meya faru?"

"Dan Allah Alhaji ka maida Yaron nan gidansu"

Wani shu'umin kallo Sadik yai mata, tare da maimaita kalmar yaro a hankali.

Hakimi yace "wane yaron tukuna?"

Ba Kunya ta nuna Sadik tace "gashi nan, wallahi na tsane shi, ko ganinsa ba na son yi"

Take Hakimi ya haÉ—e rai yace "É—an uwanki ne fa, meyasa kuke furtawa juna miyagun maganganu haka ne?"

Cikin kuka Nana ta É—ago, ta nunawa Hakimi Fuskarta tace "kalli Fuskata, dukana fa yayi, da ni 'yar uwarsa ce ai baze dakeni haka ba kome nai masa"

Hakimi yace "Ke me ki kai masa ya dake kin?"

"Ko laifi nai masa seya dakeni haka?" Nana tai maganar wasu hawayen na zubowa daga idonta.

Hakimi ya maida idonsa kan Sadik yace "me tai maka kai mata wannan dukan haka? Kalli shedar yatsunka a fuskar ta?"

Kallo ɗaya Sadik yai mata, ya ɗauke kai yaƙi sake kallonta, kuma yaƙi Magana kamar gunki.

"Magana fa nake maka"

Sadik yai shiru ya sunkuyar da kai.

Hakimi yai murmushi yace "Yanzu nan, ka zo ka sani a gaba, kana min magiyar in bari ka koma gida, amma na fuskanci haryanzu ba kai laushi ba da sauranka, tashi ka bani guri"

Seda Sadik yai jimm kamar ba ze tashi ba, se kuma ya tashi yana kumbura baki ya bar É—akin.

Nana kuwa ta cigaba da kuka Hakimi na rarrashin ta, Inna ce da ta shigo ta koretaz tace maza taje ta saka Uniform ta tafi Makaranta a haka, gobe ta kiyayi shiga sabgar Sadik.

Bayan fitar Nana Inna ta kalli Hakimi tace "Allah ya baka Nasara, nifa lamarin Yaron nan ya fara bani tsoro"

Hakimi ya numfasa yace "ba ke kaÉ—ai ba, ni kaina haka, amma hakan ya samo asali ne daga rashin kyakyawar tarbiyya da be samu ba a gidan su"

"Tabbas ni zan faɗi wannan ma, kasan zuwa nai na tarar ya ritsata a ɗaki daga ita se ɗaurin ƙirji ya mareta, nai masa magana nace masa duk hukuncin da ze mata kamata yai ya bari se tana cikin sutura, a haka zata iyayin tsirara, Yaron nan ba kunya ba tsoron Allah yace min wai ai wannan ba mace nace ƙwaila ce, Yaron nan fa idan ba ai dagaske ba se abunda Allah yai, wai harya san ƙwaila ya san mace, ko da yake ba abun mamaki bane, tunda a kunne na naji yana gayawa uwarsa wai Aure yake so"

Hakimi yai murmushi yace "Manya gatan wasa, to be isa Auren bane?"

Inna tace "ya isa mana, da a zamanin mu ne ai tuni an masa mata, kuma jiya da Asubar fari ya shiga ya hau wanka, kaga kuwa ya tabatta ya isa Aure"

"Amma shine mahaifinsa yake son turashi ƙasar waje karatu? Shi duk baya ganin abubuwan mu da muka gani?"

Inna tace "wayasan masa? Yasa Aƙidar boko da yahudawa a zuciyar sa, gashi Allah ya haɗashi da matar da ita ma ba ta san abunda ya dace ba"

"Lallai kam, shikenan zanyi abunda ya dace a kai, na san abunyi, ai da zuwa yai ya sani a gaba yana so in bari ya koma gidansu, da har zan amince wannan yarinyar ta zo tana kuka, tunda abun masa hakane nasan maganinsa"

Inna tace "meye maganin nasa?"

"Ki zuba ido zaki gani".

Abu kamar wasa Lilly suka koma yadda suke ita da Sir Nazir, sedai haryanzu sheÉ—an na cigaba da hura musu wuta, tun da suka aikata son zuciya sheÉ—an ke ta sake ruru musu wutar fitina a tsakanin su.

Gashi Nazir ya tuba, yace baze sake aikata makamancin abunda yai ba dama be taɓa ba se a kanta, kuma baya sha'awar sake aikata abunda yai ɗin.

Sedai a duk lokacin da suke tare, se yai ta maza yake iya daure kansa, dan wasu lokutan idan a wayane ma ya dinga sakin layi kenan.

Yanzu ma ta gama zana jarabawar da zata zana, kasancewar makarantar ba kowa ya basu damar sakewa sosai da juna.

"Fatima" ya kira sunan ta.

"Na'am" ta amsa tana kallonsa.

"Babanki ze bani Aurenki kuwa?"

"Wallahi sir ban sani ba, amma meyasa ka tambaya?"

"Bana son mu sake aikata ɓarna ne, wallahi ina sonki da gaske, idan zaki iya Auren talaka kamata"

"Nima ina sonka sosai sir, sedai ban sani ba ko Daddy ze yadda ba, kuma ai kaga baze yuwu yai min Aure yanzu ba, a Jss3 fa nake"

Ya lumshe idonsa yana fesar da iska daga bakinsa yace "in my opinion, ina ga zan bar aikin nan in koma Jigawa kawai, ai dama na gama service É—in naji daÉ—in zaman garin nan ne"

ÆŠan zare ido tai tace "meyasa zaka koma?"

"Saboda in dena ganinki ko na samu nutsuwa, a baya ni babu wata mace da nake shiga wani yanayi saboda ita, amma idan har zan ganki da ƙyar nake samun saita kaina"

"To seka tafi ka barni?" Tai maganar a shagwaɓe.

"To ya zanyi Lilly, haka shine samun nutsuwa ta"

"But i love You, Please kar ka koma dan Allah" tai maganar kamar za tai masa kuka.

A hankali ya janyo ta jikinsa, ya ɗora hannunta a saitin ƙirjinsa, tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri sauri, yace "kinji fa halin da nake shiga a duk lokacin da muke tare ko na ganki, ƙaddara ta kawoki cikin rayuwata, idan ban same ki ba, i better go back to my village"

Gyara kwanciyarta tai a jikin Nazir tace "no ba za ai haka ba, zan san abunyi nima gaba É—aya karatun nan ya fita daga raina, dama ba wani ja nake ba, gara aimin Auren in huta"

"Karatun yana da kyau, amma idan munyi Aure zan bari ki cigaba, but Please help me"

Ta É—ago tana wasa da sajensa tace "don't worry Baby" a nan ma dai Allah ne ya rufa Asiri basu watse ba ni dai nai gaba.

Faruk na kwance a falo daga shi se boxers, yana kallon TV, yana missing É—in Sadik sosai, se yaita kallon É—akin Sadik É—in yaga kamar ze ga Sadik É—in ya fito daga É—akin.

Knocking ɗin ƙofar yaji yana ayi, ya miƙe ya nufi ƙofar dan ya buɗe, yana mamakin waye da tsakar ranar nan haka.

Yana buÉ—ewa ya ga Khairat a tsaye da tray a hannunta, seda gabanta ya faÉ—i ganin Faruk, jikinta ya É—au rawa kamar mazari, ta shiga bin sa da ido, yadda gashi ya kwanta a jikinsa.

Yatsunsa biyu ya haÉ—a ya murza suka bada sauti, a saitin fuskarta Yace "ya dai? Ya akayi ne?"

Da ƙyar ta haɗiye yawu jikinta na rawa ta miƙa masa trayn da ke hannunta.

"Meye wannan?"

"Amm..dama nayi juice ne na cucumber na san kana so shine na kawo maka"

Yace "Wow, aikuwa kin kyauta, shiga ki ajiye"

Ta shiga cikin falon ta ajiye, tana cigaba da kallonsa, ba ta taɓa sanin kyan Faruk ya kai haka ba, gashi da ƙira me kyau, ga wani six packs a cikinsa.

Bedroom ya shiga ya sako jallabiya fara ya dawo falon ya zauna.

Se taji dama be saka ba ta cigaba da kallonsa a haka.

Yace "yau me kuka dafa ne a gidan?"

"Ai ba a gama girkin ba" ta bashi amsa.

"Ai ba cewa nai ko an gama ko ba a gama ba, cewa nai me kuka dafa, ko ince me kuke dafawa?"

"Ina ga shinkafa da miyar zogale"

Yace "what? Shinkafa da miyar zogale kuma?"

Tai saurin dawowa hayyacinta tace "shinkafa da miya ne"

"It seems something is wrong with you, tashi ki tafi"
Chapter 33 · 0% Book details