← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 115

Sashe 55

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sameshi a É—aki yana danna waya, ta zauna kusa da shi ta kalleshi tace "Abba nifa haryanzu baka gayamin wani mataki zaka É—auka akan Auta ba"

"Ai na gama magana, me kike so ince miki kuma? Gida ze dawo ya haƙura da karatun kawai, da ya lalace gara ya dawo ya zauna, in ya ga dama yayi karatun a nan"

Mother tace "dan Allah kar kayi haka, ka dai ja masa kunne, kuma nima na kirashi, nai masa faɗa dan Allah ka ƙyaleshi"

Abba ya girgiza kai yace "is too late"

"Is not late, kaga yaro ne shirirtar Ƙuruciya ce ke damunsa, amma baze ƙara ba"

"Ya a kai kika san ba ze ƙara ba?"

Mother ta gyara zama tace "Munyi waya da shi ai, yace baze sake ba"

Abba ya sake girgiza kai yace "na gama yanke hukunci kuma ba zan canza ba"

"Dan Allah kar kayi haka,kas...

"Kinga, ya isa haka na gama magana"

Abba ya fututtuke yaƙi saurarar Mother, haka ta tashi jiki ba ƙwari ta bar ɗakin ta koma sashinta.

Dr. ta kira a waya, ta sanar masa abunda Sadik yai, da hukuncin da Abba ya yanke.

Usman yace "Wallahi Mother Sadik is  so much spoiled, mu meyasa ba muyi haka ba da mukai karatun a waje, se shi?"

A fusace Mother tace "ba kiranka nai kai min faɗa ba, na ga mahaifinka yana shawara da kai, shiyasa na kiraka ka taushe shi kaima, dan ni yaƙi saurarata sam"

Usman yace "to Allah yasa ni É—in ya saurare ni, dan abunda kika kasa yi ba lallai mu mu iya ba".

"Ai kwanan nan duk ya canza wallahi, ka dai tuntuɓe shin, ko Allah ze sa ya yadda"

Usman yace "shikenan, zan shigo gidan zuwa gobe insha Allah"

Mother tace "Allah ya kaimu, ka gaida Jiddan"

Ya amsa da "za taji insha Allah".

Lokacin Auren Farhan na ta ƙaratowa, ba tare da samun wata fahimtar juna tsakanin ta da Sunusi ba, kullum cikin faɗa suke da tashin hankali, Gashi ta kasa fidda ran Sadik ze dawo rayuwarta, wasu lokutan ta kan tuna da Doctor Abbas, dan ba zata taɓa manta Alkhairinsa ba, dan set ɗin tukwane non stick ya sai mata, da gas cooker, da kuɗi har dubu hamsin, haka Hajiya ta kai gidansu Farhan tace inji Abbas.

Idan Farhan ta ga kayan da ake siya da sunan Aurenta, se taji ina ma gidan Sadik za'a kaita da kayan nan ba gidan Sunusi ba.

Tayi duk yadda za tai ta cire Sadik daga ranta, amma abu ya gagara, gashi kamar wadda akaiwa Asirin farinjini, duk da ƙanƙantar shekarunta, kusan kullum idan ta fita se tai saurayi, suyi ta binta, abunda yake ƙara caza mata kai kenan, shikuma Sunusi da ya ganta da wani se ya hau bala'i yana surfa mata jaraba.

Gashi ya ɓata mata suna a unguwa, tun lokacin da ya tara mata Mutane a ƙofar Gidan su Abbas.

Abubuwa suka sake damalmalewa Farhan, ta rasa in da zata saka ranta taji sanyi.

Lilly kuwa abu kamar wasa, suka koma ruwa ita da Nazir, dan tamkar matar da ya sa sadaki ya auro haka ya maida ita, duk lokacin da ya buƙace ta, za taje ba musu ba komai.

Mussaman yake mata allurar family planing, saboda gudun sake samun matsala, makarantar kanta wasu lokutan ba ta zuwa, se tai tafiyar ta gidan sa, fafur taƙi yadda direba ya cigaba da kaita yana ɗakkota, a cewar ta ai yanzu tai girman da ta wuce wannan level ɗin.

Abba yai banza da batun Sadik, be kuma yin Maganar ba, har Mother tai zaton ya haƙura da batun ne, ta cigaba da sabgogin ta.

Rana tsaka yace mata zeje London. Ta tashi hankalinta "dan Allah idan akan maganar yaron nan zakaje kayi haƙuri, na gaya naka baze sake ba"

Abba yace "Ai ba Sadik kawai na ajiye a London ba, ina da 'yar da zanje in ga halin da take ciki, dan haka ni yanzu babu ruwana da lamarin É—anki, 'ya ta zanje in gano"

Maganar Abba taiwa Mother ciwo nesa ba kusa ba, ta so ta mayar masa, amma ta ƙyaleshi, dan yanzu se su kuma haurawa da shi, dan haka ta ƙyaleshi.

Nana farinciki take yau kamar me, tana murna yau za'ai musu hutun session, watanninta huÉ—u kenan tunda aka kawota ba ta sake ganin wani yazo mata daga Nigeria ba, kuma ba ta fita daga makarantar ba.

Ta sa ran ganin Abba, Amma ga mamakinta se taga Steve, duk da ba haka ta so ba, amma hakan be hanata nuna farinciki da ganin sa ba.

Shine ya ɗauke ta, ya tafi da ita gidansa in da suka taɓa zuwa farkon zuwan su garin.

Matarsa da yaransa na da kirki matuƙa, suka karɓeta cikin mutunci.

Tana son ta tambayi ina Abba, amma se taga zasuga kamar abunda suke mata suna ta tarairayarta, kamar ba tai appreciating ba, dan haka tai shiru.

Se yamma liƙis, ba tsammani taji muryar Abba, kamar an mata kyakyawan Albishir haka ta tashi cikin murna da fara'a.

Abba yaga Nana tai fresh da ita kamar ba ita ba, yai murna ƙwarai da gaske da ganin Nana.

Yaci Abinci yai salla, ta dinga ba shi labarin Makaranta da kuma ƙawayen da tayi a makaranta.

Wannan karon a gidan Steve Abba ya kwana shima, da safe taga an fito da Akwatin ta, da kuma Akwatin kayanta na farko da ta zo da su, duk an saka a Mota.

Tai ta murna tana tunanin Nigeria za su dawo, sedai ta ga sunyi doguwar tafiya, sannan suka shiga wata unguwa, me ƙarancin gidaje, kusan gidajen da suke unguwar iya wani ɗan rukuni ne kawai.

Wani matsakaicin gida akai parking, taga su Abba sun buɗe motar sun fita, Abba ya leƙa yace "Nana fito"

Ba musu ta fito, taga Steve ya sauke Akwati nan ta daga Motar.
Kai tsaye Abba ya nufi Gidan, yasa hannu ya buɗe ƙofar Gidan, suka bi bayan Abba.

A falo Nana tai tozali da Sadik, ba ƙarya yayi kyau fatarsa tai fresh, sumarsa se ƙyalli take ya ƙara wani kyau na musamman.

Seda gabanta ya faÉ—i, dan rabon da ta ganshi tun Ranar da suka bar gidan Steve aka kaita Makaranta.

Kallo É—aya yai mata ya É—auke kansa, suka nemi guri suka zauna, Steve ya fita waje ya basu guri.

Abba ya nemi guri ya zauna, sannan yai wa Nana umarnin ta zauna, ba musu ta nemi guri ta zauna tana rarraba ido, tare da satar kallon Sadik da yake ta haÉ—e rai.

Abba ya kalli Sadik yace "Wannan shine hukuncin da na yanke a kanka, wallahi da niyyata hatta makarantar, se ka barta ka koma Nigeria, amma 'yan uwanka su kai ta bani haƙuri, da ne nake maka kallon yaro ƙarami, amma tunda abunda ka zaɓawa kan ka kenan, ga matarka na kawo maka, idan ka ga dama ka kwaɗata ka cinye, sedai ba zan cigaba da maimaita maka ba, duk abunda ka ga dama kai mata, daidai nake da kai, dan ba zan sa ido ka lalace a banza ba, ka ɓatamin suna".

Ya maida idonsa kan Nana yace "Nana, Steve ya karɓo miki takardar transfer, in aka koma Makaranta ze kaiki sabuwar makarantar da zaki koma, daga nan gidan zuwa makarantar ba nisa, day ce Makarantar, Steve ze dinga zuwa yana duba ku, duk lokacin da yai miki wani abu, na rashin jin daɗi, ki karɓi wayar Steve ki kirani ki gayamin.
ki kwantar da hankalinki, ki masa biyayya tunda Allah ya ƙaddara mijinki ne, kai kuma in kaga dama, kai mata riƙon da ka ga dama, zaka ga yadda zan da kai, miƙomin wayarka"

Sadik ya ciro wayar ya miƙawa Abba, Abba ya zare layukan wayar, da wayar ya sa a aljihunsa, ya miƙe ya nufi hanyar fita.

Nana tabi Abba da kallo, kamar ta tashi ta bi Abban da gudu, dan ta san kashinta ya bushe tun da aka ce ta zauna  ita da shi a gida ɗaya, ba ta san laifin da yayi Abba yake masa faɗa haka ba, amma da alama laifin da yayi babba ne.
Ba ta ƙara tsurewa ba, se da taga irin ɗan banzan kallon da yake binta da shi, nan da nan ta sake jin jikinta yai sanyi.

Daga Nana har Sadik aka rasa wanda ze raka Abba, saboda kowa da abunda yake saƙawa a zuciyar sa.

Suna jiyo ƙarar motar Steve, Sun tafi.

Nana ta É—aga kai ta kalli Sadik, suna haÉ—a ido ya ja wani uban tsaki ya tashi ya fice ya bar gidan gaba É—aya.

Nana ta zauna tsuruu ita kaɗai a zaune, ba tai zaton za'a mata transfer ba, se yanzu take jin ta shaƙu da su Linda Sosai.

Farhan dai gata nan gata nan, wasu lokutan kamar mara hankali, gaba ɗaya gudun mutane take yanzu sosai da sosai, kullum se dai ta ƙule a ɗaki, tai kuka tai tunani rashin son maganarta ya ƙaru fiye da da, babban abunda yake damunta shine rashin bacci da matsanancin feelings da take fama da shi, wanda Duk silar Sadik ne ta shiga wannan halin da take ciki.

Ta dawo daga makarantar dare, ta biya ta gurin me chemist É—in nan da ya zo ya dubata.

Suka gaisa Sannan tace masa "dan Allah maganin bacci nake so ka bani, da rage damuwa"

Ya kalleta yace "wane irin maganin bacci kuma da rage damuwa?"

Tace "wallahi nafi wata uku bana bacci duka dare, se ciwon kai bana iya bacci"

"To ai kinga jininki ne yake hawa yana sauka, haƙuri zaki ki cire duk wata damuwa da take ranki"

Farhan tace "dan Allah ka temaka min, ko baccin ne in samu in dinga yi, kaga allurar da kai min kwanaki naji daÉ—in ta, ka temaka min kar kaina ya tarwatse"

Ya É—anyi shiru Sannan yace "shikenan ba damuwa, bari in baki amma kaÉ—an kije ki gwada, duk in da kika sha na kwana uku zuwa huÉ—u, se ki dena sha"

Farhan tace "to, nawa ne?"

Yace "karki damu, ki bar kuÉ—in kawai, kije ki jarraba Allah yasa a dace"

Ta karɓa tai masa godiya ta tafi gida.
Chapter 55 · 0% Book details