Sashe 14
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya dafa Sadik yace "Sadik, RUƊIN ƘURUCIYA ne ke damunka, kana tafiya karatu ya ɗauke naka hankali zaka manta da ita, sannan ina kai ina wata Soyayya? Shirmen ƙuruciya ne kawai, ka cire ta daga ranka ka fuskanci rayuwar ka kaji ko?"
Sadik ya jinjina kai jikinsa a Sanyaye.
Abba yace "yawwa my son, Allah ya baka ilimi me amfani, matso kusa dani muyi breakfast tare"
Sadik ya girgizawa Abba kai yace "na karya"
Ya miƙe jiki a Sanyaye, ya bar part ɗin, ɗakinsa na BQ ya tafi, jikinsa har rawa yake saboda tsabar damuwa.
A falo ya wuce Faruk, yana shirin fita.
"Sadik lafiya kuwa?"
Sadik be amsa masa ba ya wuce É—akinaa, yana zuwa ya faÉ—a kan gadonsa, ya É—ora pillow a kansa kawai yaji hawaye ya fara bin fuskarsa.
"Sadik tashi muyi magana, meye haka kake ne?" Yaji muryar Faruk a kansa.
Sadik ya tashi zaune, sedai abunda ya bashi mamaki be wuce yadda yaga hawaye a fuskar Sadik ba.
Take hankalin Faruk yai mummunan tashi, saboda mutum ne me matuƙar son 'yan uwansa.
"Sadik meke damunka ne, ka É—agan hankali fa"
"Faruk dan Allah ka gayamin meyasa kuke cewa soyayata RUƊIN ƘURUCIYA ce? Na gayawa Abba abunda yake damuna, amma shima yace min RUƊIN ƘURUCIYA ce, meyasa kuke cewa hakane?"
Faruk yace "Sadik, ba ka ajiye batun nan ba ko? Ni da kai na gaya maka komai, kuma nace maka lokaci ne, zaka dena jin duk abunda yake damunka"
Shiru kawai Sadik yai, Faruk ya cigaba da ƙoƙarin kwantar masa da hankali, amma sam baya jin abunda Faruk ɗin yake faɗa, har yai ya gama ya bar ɗakin.
Yana cikin tunanin ne, Wayar Sadik ta far ringing, be ko duba waye ba ya É—aga ya kai kunnensa.
"Wato kai dan ka riga mu graduating har ka fara ja mana aji ko? Ji muka fito muka nemeka muka rasa, ana can ana ta celebrating muna nemanka muyi maka spraying kuÉ—i, amma muka neme ka muka rasa gaba É—aya"
Nasir ne yake ta wannan cakwaikwaiwar da ba Komai Sadik É—in yake fahimta a cikin maganganun nasa ba.
"Sadik kana jina kuwa?"
Sadik yai ajiyar zuciya yace "ina jinka mana"
"Amma shine kai mana banza? Wallahi har mun fara missing É—in ka"
Sadik yai murmushi yace "kune za kuyi missing É—ina?"
"Wallahi Sadik dagaske nake, gaba É—aya yau ajin ba daÉ—i baka nan, ko salama ba ka tsaya munyi ba jiyaka tafi"
Sadik yace "na tafi kai mata ta gida ne shiyasa"
"Lallai Sadik, yanzu yarinyar da ka haÉ—u da ita a 'yan watannin nan har ta fiye maka mu da mu kai shekara da shekaru tare?"
"Kowa matsayin sa daban a gurina"
"Bakomai, yaushe zaka shigo ne?"
"Daga gama makarantar se in fara zuwa, se an kwan biyu tukuna, bana son in zo ta shiga damuwa"
Nasir yace "Lallai, abun anku babba ne Sadik"
Sadik yace "ƙwarai kuwa, zamu bawa wanda suka ɗau lamarin namu wasa Mamaki"
Nas yai dariya yace "ai shikenan"
Su kai sallama Sadik ya kashe wayar ya cigaba da tunanin sa.
Ya barwa zuciyarsa ze jarraba cire Farhan daga rayuwarsa ko da gaske ne da ake cewa ba sonta yake ba, RUƊIN ƘURUCIYA ne kawai?
Sir Nazir kuwa tun da abun nan ya faru, kusan kwanaki uku amma damuwa da masa yawa, hakan ya bawa ciwon zama sosai a jikinsa, ga ciwo ga damuwa, hawaye sosai yake idan ya tuna aika aikar da ya tafka, be san wani irin hukunci ze fuskanta ba, ko zata je ta faÉ—a azo a kama shi, ko ba zata faÉ—a ba be sani ba.
Kasa jurewa yai, ya É—au wayarsa ya kira layinta, beyi tsammani ba yaji ta É—aga wayar.
Da sauri ya tashi zaune yana faÉ—in "Fatima ya jikin ki?"
Maimakon tayi Magana se sheshsheƙar kuka da take.
"Lilly dan Allah ki saurareni, kuskure ne mun riga munyi amma dan Allah....
Be ƙarasa maganar ba ta sake rushewa da kuka, wanda yake bayyanar da tsantsar damuwa da take ciki.
Kasa magana yayi daga ƙarshe ya katse kiran, wasu hawayen dana sani suka shiga zubo masa, shima yana da ƙanne mata, ƙannensa tara mata wasu an musu Aure wasu ba suyi ba, amma yau ace shine yai zina da 'yar da da yayi Aure da wuri, da ya kusa haifarta.
Wani irin dana sanin zuwa makarantar nan ya sake baibaye shi, tun yana jami'a mata suke bin sa, tun yana da ƙananan shekaru ma kan ya shiga jami'a, Amma babu wadda ta taɓa cin galaba a kansa se Wannan tatsitsiyar yarinyar ɗalibarsa.
Sosai ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro, damuwa da dana sani suka haɗu suka sake baibaye shi.
Kewa ta fara damun Farhan, na rashin abun ƙaunarta a kusa da ita, shikenan yanzu idan aka fita break bata da gurin wanda za taje suyi hira, sedai kullum ta na aji, wataran sedai ta kwanta tayi kuka, dan ba ƙaramin kewar Sadik ɗin take ba, gashi yai mata alƙawarin ze dinga zuwa yana ganinta, amma yau sati guda da barinsa makarantar bata ƙara jin ɗuriyarsa ba.
Har abunda ya faru ya faru, Lilly ta warware Mummynta ba ta dawo daga garinsu ba, ta koma Makaranta dan zaman Gidan damuwa yake ƙara mata.
Sedai tun da ta koma kallo É—aya za kai mata ka san ta canza sosai da sosai, dan duk ta wani koma so silent.
Yasmin ce ta fara lura da hakan tace "wai Lilly meke damunki ne? Kince mana baki da lafiya, amma na ga duk kin koma wata iri, baki da kuzari, ko dai duk dan Nazir ba lafiya ne?"
Lilly ta girgiza kai tace "A'a, ni ba abunda yake damuna"
Haseena tace "kinga yadda ki ka rame Kuwa? Kin rame sosai gashi kin koma wata saliha, waima meya sameki ne?"
Kallonsu tai suna daga cikin wanda suka dinga ingiza ta duk me afkuwa ta afku, gashi ta rasa mutuncinta amma su suna tare da nasu.
Tace "Ciwona ne ya tashi kawai, ga Mummy ba ta nan, shiyasa duk abun yai min yawa haka"
"Eyya sannu Allah ya baki lafiya"
Ta amsa musu da 'Ameen"
Class rep ne ya shigo yace "Lilly, yau kamar haÉ—in baki, mutumin naki ma se yau ya dawo aiki, yana kiran ki a Office É—in sa"
Gabanta ne ya faɗi, dan ko haɗa ido ba ta sake son yi da Nazir, Haseena tace "Yawwa muje ma, ni ina da Matsala a test ɗinsa yai min ƙwauron maki"
Lilly ba ta son su fahimci wani abu, dan haka ta tashi jiki babu ƙwari suka fita ita da Haseena.
Tun da suka shiga Office É—in idonsa na kan Lilly, wadda kallo É—aya za kai mata ka ga duk a hargitse take.
"Sir ya jiki?" Haseena ta faÉ—a tana kallonsa.
"Alhamdilillah" ya faɗa a taƙaice.
Haseena ta fara masa magana akan test É—in ta, amma ya kalleta yace "can You please excuse us?"
Haseena ta kalli Lilly, ta kalli sir Nazir taga yadda fuskokin su ke É—auke da damuwa.
A hankali ta janye jikinta ta fita daga Office É—in.
Nazir ya kalli Lilly, cikin sanyin jiki yace "Fatima zauna muyi magana"
Girgiza masa kai tayi alamar ba zata zauna ba.
Miƙewa yai a hankali yaje ya kulle Office ɗin, ya dawo ya tsaya a gabanta, ya zubawa kyakyawar fuskarta ido, wadda take ta koma jawur saboda kuka.
Cikin rauni da karaya yace "Am sorry please, ban San meyakamata in ce miki ba, but..
Kasa ƙarasa maganar yai, ganin yadda jikinta yake kyarma saboda kuka.
Riƙo hannayenta yayi a cikin nasa "dan Allah Lilly ki yafemin, ki rufamin Asiri"
"You ruin my Life, ka cuci Rayuwata"
"Na sani, kuma ba kowa nai ba kaina nayi wa, amma ki bani damar wanke laifin da na aikata, ina da ƙanne Mata idan a kai musu nima ba zan ji daɗi ba, idan na nemi Aurenki a gidanku za'a bani?"
Turus tai tana kallon Nazir, dan ta san abune me wuya, dan iyayenta basa ƙaunar talaka mussaman mamanta, amma ita harga Allah tana ƙaunar Nazie duk da wannan abun da ya gifta a tsakaninsu.
"You mean zaka Aureni?"
"I mean it Lilly, na ɗauki abunda ya faru tsakanin mu a ƙaddara, amma in zaki iya Auren talaka kamata, ina sonki a hakan tunda dama aini nayi kuskuren"
"Na yadda, na amince in dai zaka Aure ni"
"Shikenan, tunda mun tsaya akan wannan yarjejeniyar, mu zama masu riƙe sirrin junan mu, kuma muyi ƙoƙarin kaucewa faruwar hakan a gaba"
Ta jinjina masa kai tace "insha Allah, ba zan gayawa kowa ba"
"Yawwa my love" suka rungume juna, yana ɗan shashafa bayanta alamar rarrashi (🙄🙄 anyi ba ai ba kenan).
Farhan kam shirun da taji babu É—uriyar Sadik yasa ta fara karaya, da fari ji tai kamar taje ajinsu ta tambayesu shi, amma ta fasa, dan 'yan ajin nan nasu se a hankali, yanzu za su iya kawo mata maganar banza.
Sadik ji yake kamar bashi da lafiya, zuciyarsa se azalzalarsa kawai take akan son ganin Abincin ruhinsa wato Farhan, amma yana son tabattar da gaskiyar batun da ake masa akan Farhan É—in.
Farhan kam ta fara sarewa, dan in dai ta tuna da shi se tayi kuka, tana Addu'a Allah yasa yazo ta ganshi.
Tana cikin tunanin sa Umma ta ɗaga labulen ɗakinta tace "kije kinyi baƙo"
Farhan tace "to"
Umma na juyawa Farhan ta ɓata fuska, dan ta san ba ze wuce wannan mannannen bawan ba, wato Sunusi duk abunda take masa na ƙin yi masa Magana idan ya zo, be sa ya fahimci in da ta dosa ba.
Ta saka hijjabinta ta fito, aikuwa shiɗin ne ba wani ba, tana ganinsa taji kamar ta koma gida da gudu, dan ko ƙaunar ganinsa ba tayi.
"Barkanki da wannan lokaci ya furen zuciyata"
Idan akwai abunda Farhan ta tsana be wuce wannan banzayen kalaman ba da yake faɗa, dan sam basa burgta sema ƙara ɓata mata rai da suke.
Ya sake cewa "ina fatan kin wuni lafiya cikin aminci kamar ni"
Farhan a ranta taji kamar tace "A'a cikin tashin hankali na wuni" amma ta dake, da yake wulaƙanci ba ya cikin ɗabi'arta.
Tace "dan Allah ko zamuyi sallama, zan tafi makarantar dare kar in makara"
Sunusi ya gyara tsaiwa yace "Amma ai kya bari mu gaisa ko?"