← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 115

Sashe 43

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "Yawwa, ai dama na gaya miki ba zafi, saura ta baya se kuma in sa miki drip zan tafi gida".

A ɗan shagwaɓe tace "wayyo Allah"

Abbas yace "to yi kuka kawai mana, kin samu lafiya ne shiyasa kike kuka"

Sunusi ji yake, kamar ya dunƙule hannu yai ta kirɓar Abbas.

Abbas ya kalli in da Sunusi yake, wanda se da ga baya ya lura da shi a É—akin yace "É—an bamu guri zamuyi allura ko?"

"Ba inda zani, nace ba in da zani, tunda nine mijinta ayi a gabana mana in ba munafunci ba se lailaye mata jiki kake, Wato in baku guri kaji daÉ—in yi, to ba zan fita ba"

Abbas ya zare gilashin idonsa yace "Kaine mijin nata ko wa?"

"Eh nine nan, kallon ku ai kawai nake"

"I don't fucking care who so ever you are, kaje waje zan mata Allura, kuma ni babu wanda yacemin matar wani ce, tunda aka kawota mahaifinta nake gani a kanta, dan haka ka bamu guri"

Abbas ya kalli Farhan yace "wai ma waye wannan?" Kuka Farhan ta saka ta kasa magana.

Be kuma cewa komai ba, yai waya gate sega security da bindiga yazo ya fitar da Sunusi.

Har gari ya waye tsakanin Mother da Abba, ba wanda ya kula wani kowa sabgar gabansa yake da saƙa abunda yake ganin shine daidai a gareshi.

Da safen Abba harya shirya ze fita, yaje ɗakin da Nana take dan ganin halin da take ciki, ya tarar da ita a kwance a ƙasa.

Abba ya ƙarasa da sauri, yace "Nana, kwanciyar me kike a ƙasa haka?"

Nana ta tashi zaune tace "Abba ina kwana"

"Lafiya ƙalau, meyasa kika kwanta a ƙasa?"

"Zazzaɓi nake ji shiyasa"

"Meysa baki faɗa ba to, ai da ko maman naki kin gayawa, wannan kukan da ki kai ai dole kiyi zazzaɓi"

Tace "Ai ban ganta bane, shiyasa ban gayamata ba"

Ya kalli idon Nana, ya ga yadda tai wuri wuri kusan kamar ma a galabaice take, yace "kinci Abinci kuwa?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Jiya fa an baki Abinci?"
Tace "eh"

"Gayamin gaskiya, an baki ko ba a baki ba?" Yai maganar cikin razanarwa.

Tai sauri tace "A'a"

Abba ya jinjina kai yace "dole in nunawa yaron nan da uwarsa a ƙarƙashina suke, zasuga matakin da zan ɗauka.

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Abba ya tashi Fuuuu ya fice daga É—akin da Nana take, an É—an jima kaÉ—an sega Talatu É—aya daga cikin masu aikin gidan ta kawo wa Nana Abinci.

Tace "Nana, ya akai ki ka zo ban sani ba, baki nemi kowa a gidan nan ba?"

Murmushin ƙarfin hali kawai Nanan tayi, idanunta sunyi jawurr sun kumbura.

Tace "Yallaɓai ne yace a kawo miki Abinci, Ya kike ya Hajiyar?"

Nana tace "tana nan lafiya"

"Madalla, ashe ba da ita kuka zo ba"

Nana ta fara ƙosawa da hirar Talatun, dan haka tai shiru, ta haɗa tea ta fara sha saboda yadda cikinta yake a ƙulle.

Sosai take cin Abincin ba dan tana so ba, sedan azabar ƙullewar da cikinta yai.

Daga Inna har Hakimi babu wanda yai baccin kirki, mussaman Inna da ta dinga kuka cikin dare, akwai shaƙuwa me ƙarfin gaske tsakanin ta da Nana, lokaci ɗaya ba tare da ta shirya ba, an raba su.

Abba kuwa yana zuwa gate, ya kira security.
Cikin hanzari yazo cikin girmamawa yace "gani ranka ya daÉ—e"

Abna yace "Dan Allah, daga yanzu zuwa lokacin da Sadik ze bar Gidan nan karka kuskura ka barshi ya fita, idan kuwa har yai maka gardama ka harbe shi a ƙafa"

BuÉ—e baki security yai da mamaki, É—an Auta kuma shalelen ake cewa a harbe, Abba yace "Umarni nake ba, idan ba kai abunda nace ba ka bari ya fita, to kai zan harbeka"

Jiki na tsuma yace "shikenan, insha Allah baza'a bari ya fita ba"

Daga haka Abba ya fice daga gidan.

Sadik kuwa tun daga ƙwarin gwiwar da ya samu daga gurin Mother yaji zuciyarsa ta ɗanyi masa sanyi.

Wayoyinsa ya ɗakko ze saka a caji, dan yau da Yamma yana son fita ya sha iska, sedai ya tuna ya baro simcards ɗin sa duka a can ƙauye, a ƙulle a ƙasan kilisai.

Wani dogon tsaki ya ja, ya jona wayoyin, sannan ya fita BQ.

Yana zuwa ya tarar da Faruk yana karyawa, Faruk yai masa murmushi yace "Ango Ango, Ango ka sha ƙamshi Allah ya karɓi Addu'ar ka kayi Aure ka barni"

Tsaki Sadik yai yace "Wannan har wani Aure ne? Da shi da babu duk É—aya dan babu abinda na tsana sama da Yarinyar nan"

Faruk ya Ajiye kofin hannunsa yace "A'a Sadik, koma menene babu laifinta a ciki, ba ita tace tana sinkaiba, yadda a kai maka ba zata ita ma haka a kaimata, dan haka karka cutar da Ita Sadik"

"Ba abunda yai min zafi, yadda kakaninta suka dinga azabtar dani akanta zan rama, kuma da ƙafafuwanta zata koma in da ta fito, zata gane kurenta"

A É—an hasale Faruk yace "Sadik, ka manta abunda Hakimi yace maka, amana ce a gurinka"

"Mother tace ai ba Ubana bane, dan haka ba abinda ze faru dan ban bi son zuciyarsu ba"

"Sadik! Are You mad? Babu biyayya ga abokin halitta gurin saɓawa mahalicci, a nan gurin be kamata kaiwa Mother biyayya ba, kakanmu mahaifinmu ne tunda yai silar kawo mahaifinmu duniya, a tunaninka da baffansu Mother yana raye shi ya ɗau wannan hukuncin zata gaya maka haka ne? Mahaifiyarmu ce amma Yakamata mu dimga tunani akan wasu abubuwan"

Sadik yace "Stop it please, babu wani abu da zaka gayamin da ze sa in sauka daga kan bakana, bana ƙaunarta kuma ba zan zauna da ita ba, se ta koma ƙauyensu, dan yadda suka azabtar dani sena rama a kanta"

Be kuma sauraron Faruk ba yai waje, ya bar shi da buÉ—aÉ—É—en baki.

A harabar sukai karo da Khairat, cikin fara'a da murna Khairat ta nufi in da Sadik yake, sedai ko kallo ba ta isheshi ba, saboda yadda ransa yake a ɓace.

In da masu aikin Gidan ke hutawa ya nufa, yana zuwa ya kallesu yace "Ina Bala?"

Security yace "ya fita da Alhaji"

Sadik ya kalli security yace "buɗemin ƙofa zan fita"

"Zuwa inam" ya tambayi Sadik.

"Ban gane zuwa ina ba, ka aikeni ne?" Ya faÉ—a a hasale.

"Am sorry, megida yace kar in yadda in bari ka fita, in kai gaddama a harbeka a ƙafa"

Saroro Sadik yai yana kallon security, tabbas baya wasa da su, balle ace tsokanar sa suke, wannan maganar Abba ya faÉ—e ta.

Da sauri ya koma cikin gida, ya iske Mother a kitchen cikin ɓacin rai.

"Lafiya kuwa?" Mother tai Maganar tana ƙare masa kallo.

"Mother, wai Abba yace kar a kusakura a bari na fita, wai idan nace sena fita a harbeni, abun har ya kai haka?"

Mother tace "Ai babu uwar da ta tsuguna ta haifi baturen da ya sarrafa bindigar harbinka, duk wanda ya harbeka sena sa an ɓatarmin da shi, rabu da shi duk dan ya muzguna mana ne ni da kai, kuma ba gudu ba ja da baya sena kashe Auren nan murus, ƙyaleshi kar ka sake attempting zaka fita ma, ka nuna masa baka damu da hakan ba"

Sadik ya sauke ajiyar zuciya, cike da takaici ya juya ya bar Kitchen É—in.

Abba da kansa ya kawowa Nana magani, ya bata ta sha, sannan ya fita.

Gaba É—aya ya tattara Mother da Sadik yai watsi da su, ya dena shiga sabgar kowa a cikin su, ya cigaba da harkokin sa.

A masallaci ya sanar da ɗaurin Auren Sadik, kuma ya shirya ƙwarya ƙwaryar walima shi da abokansa, suka taya shi murnar Auren Sadik.

Yayin da a ɓangaren Mother abun kunya ne a ce anyi auren ɗanta a haka, Auren mara galihu.

Sunusi kuwa tunda ya bar Asibitin ya dinga mita yana masifa akan abunda Abbas yayi masa, tare da cin alwashin akan Farhan ze rama abunda a kai masa.

Tun da Sadik ya dawo, Khairat take son yi masa Magana, amma babu fuska dan ko falo baya fitowa a É—aki yake wuni, ko BQ baya zuwa saboda yadda Faruk yake sa shi gaba yana masa Nasiha.
Ɓangaren Nana ma ko da wasa bata fitowa ko falo, saboda tasan aranagamarta da Mother abun baze mata kyau ba, kullum tana ɗaki Talatu ke kawo mata Abinci, kasancewar akwai banɗaki a ɗakin, a ciki take wanka ta wanke kayan da ta cire, ta shanya a ciki.

Talatu na ta son dukan cikin Nana, dan ta fuskanci abunda yake faruwa, amma Nana taƙi Magana.

Wata irin kewar gida take sosai da sosai, tana kewar Inna da makarantar ta da ƙawayenta.

Kullum se Abba ya zo ya dubata, sun gaisa da kansa yake tambayar ta idan tana buƙatar wani abu, se tace masa ba ta buƙatar komai.

Ƙarfe takwas na dare Dr. Ya zo gidan, ɓangaren Mother ya nufa kai tsaye, tana ganinsa tace "kai kaɗai, ina Jiddan?"

Yace "Ba ta jin daÉ—i ne, shiyasa na taho kawai"

Mother tace "too, ko ciki ne?"

Dr. Ya É—an É—age kafaÉ—a yace "i dont know"

"Kamar ya You don't know? Baku je Asibiti an dubata bane?"

"Bata son Zuwa Asibiti, wai tana tsoron Allura, she prepare to take drugs, ni ba zan takurata ba"

"But atleast, yakamata kuje Asibiti a tabattar da me ke damunta, zuwa yanzu ai ba abun mamaki bane ta samu ciki, ai kun huta dan nasan wataƙila wani abun ku kayi, shiyasa ba ta haihu ba"

Murmushi kawai Dr. Yai, bece Komai ba.

Mother ta sa aka kawo masa fruit, dan be fiye cin Abincin dare ba.

Yana cikin ci Mother ta kalleshi tace "hmmm ka san abinda Babanku kuwa yayi?"

Dr. Cikin ko in kula Yace "me yayi?"

"Sadik ya dawo ai shekaranjiya"

Yace "Wow, that's good se hankalinki ya kwanta ai"

"Hmmm, ka san wai Anyiwa Sadik Aure?"

"Aure Kamar yaya?"
Chapter 43 · 0% Book details