← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 115

Sashe 70

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki ya cika Farhan, meye laifinta a cikin fasa Aurenta da a kai, ita wace gudunmuwar ta bayar na fasa Auren.

"Umma dan Allah ki barni in cigaba da zuwa makaranta"

"Ba in da zaki, wuce ɗaki ki zauna, ke da ba ki ɗau abun kunya wani abu ba, ke da boko har gaban abada, wuce ɗaki, yadda kika samu a wannan halin na damuwa ke ma ba zaki ga da kyau ba, tun da kangarewa ki ka zaɓa ga ki ga duniyar nan"

Da ƙyar Farhan ta cira ƙafa ta koma ɗaki, zuciyarta kamar tai bindiga, ita ka a rayuwar ta wane irin laifi taiwa Umma da ta tsane ta haka? Take jifanta da mummunar kalmar kangarewa.

Nan zuciyarta ta shiga kai komo, da tsananin buƙatar nemawa kanta mafita.

Nana kam bayan sun dawo ma faÉ—a suka cigaba ita da Sadik, ya dinga mata masifa akan cewar dan me za ta gaisa da maza.

Tace "Ashe kai ma ka fara kishin nawa?"

"Ubanwaye ze yi kishin na ki?"

Tace "to in ba kishin ka ke ba, ina ruwanka da ni?"

"Ni kike wa haka?" Yai maganar yana nuna kansa.

Ta tura baki tace "to yadda ka ji ɗin nan, haka na ke ji idan na ga kana taɓa mata"

Ƙwafa yai ya raɓata ze wuce, se kuma ta bishi da Sauri tana faɗin "Abokina dan Allah kayi haƙuri, wallahi nima ban ji daɗi abinda nai ba, se Astagfirullah nake, wallahi nayi ne dan ka ji abunda nake ji, amma ka yai haƙuri ba zan sake ba"

"Kije ki cigaba, tunda abunda kike yi kenan a makaranta"

Ta ƙwalalo ido tace "wallahi bana taɓa maza, ka ji na rantse maka, dan Allah kayi haƙuri" tai maganar a marairaice.

Yace "Naji, jeki ki bani guri" ta ɗan zumɓura baki ta fita.

Amma a ƙasan zuciyar sa sosai, yaji pain na gaisawar da Nana tai da abokinsa, amma ya danne dan ya san shima ba shi da gaskiya.

Farhan ta na son Zuwa Makaranta sosai, dan zaman Gidan ba abunda yake sa mata se tsananin damuwa, da tsangwama da ga mahaifiyarta.

Abba ta je ta kuma samu, akan Umma ta hanata zuwa Makaranta, yace bakomai ta shirya ta koma makaranta, Umma taji hasuhin hakan, amma ba yadda ta iya da su.

Se dai yau ma da kanta taje neman maganin da Mubarak ya bata, Tasleem ta ce mata ita ma babu maganin agunta, kuma Mubarak yau be shigo makarantar ba, amma idan za ta iya, yau za'ai birthday ɗin Meena, a wani Hotel ta san babba ze je, taje se ta karɓa.

Farhan kam, ba taji za ta iya zuwa Hotel ba, dan ba ta taɓa zuwa ba, sedai da aka tashi daga Makaranta, tana dosar gidansu, ta fara jin fargaba, saboda ta san ta dawo kurkuku, yanzu za ta cigaba da jin baƙaƙen maganganun Umma, damuwa kuma za ta sake baibaye ta!

Gashi abun takaici, Ranar da ta fara fita, aka fara zunÉ—emta ana nuna ta da baki, akan abunda ya faru da ita.

Nan fa ta shiga tunanin meyakamata tayi ne, shan maganin nan kawai shine mafita ga damuwar ta.

Ta faki idon Umma tana banÉ—aki, ta É—au hijjabin ta ta fice daga gidan.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

But Farhan ta fice daga gidan, se sauri take ta bar layinsu.

"Hajiya Farhan ina za ki ne kike sauri?"

Muryar da tafi tsana a rayuwarta taji ta daki dodon kunnenta, ta waiga ta kalli in da Sunusi ke tsaye yana ƙare mata kallo.

Ƙwafa tai kawai tai gaba, dan ko ganinsa ba ta son yi, balle tuna wani abu ya taɓa haɗa ta da shi.

Ta tari abun hawa, ta gaya masa in da ze kai ta.
Suna tafe ta zubawa sabuwar dubu ɗayan da ke hannunta ido, Sadik ne ya bata ita, a ƙalla akwai kuɗi sun kai 20k a hannunta, wanda Sadik ya kan bata, kuma ya fututtuke yace se ta karɓa.

A hankali ta ji hawaye masu É—umi na bin idonta, har yanzu zuciyarta na begen Sadik, sedai ta dage da Addu'a Allah ya sa ta manta da shi a rayuwarta.

Har gaban Hotel É—in me abun hawan ya kai Farhan, ta sakko ta ba shi kuÉ—in sa, nan ta shiga rarraba ido, dan sam ba ta san in da za ta dosa ba.

Tana nan tsaye jikin wata mota, tana waige waige "What are you looking for?" Taji wata murya ta daki dodon kunnenta, a hankali ta É—aga idanunta ta ga me maganar.
Matashi ne a ƙalla ze shekaru talatin da takwas, ya kuma cewa "wa kike nema ne?"
Janye idonta tai da ga kansa, ta cigaba da jujjuya ƙwayar idonta, ko za ta hango su Tasleem.

Yace "Ikon Allah, shikenan tun da ba za'a kulani ba, nace zan iya É—aukar mota ta?"

Yai maganar da sigar ladabi, É—an kallon motar Farhan tai, Sannan ta É—an yi jimmm, a hankali kuma ta janye jikinta daga jikin Motar, ta koma gefe.

Matashin yai murmushi yace "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, dan Allah ki min magana mana" yai maganar yana kallon Farhan da ga sama zuwa ƙasa.

Ba tare da ta san in da zata nufa ba, tai gaba abunta ta bar shi a gurin, babban burinta be wuce ta ga su Babba, ta karɓi maganin nan ta koma gida ba, in ya so se taiwa Umma ƙaryar siyan magani ta fita.

Wata zuƙeƙiyar mota ce ta shigo cikin hotel ɗin, Farhan ta ɗan tsaya motar ta wuce, amma taga Motar ta tsaya a Gabanta, sauke glass ɗin motar akai, ta hango Tasleem a ciki.

"Laa Farhan, da ma zaki zo? Ya na ganki a nan?"

Farhan tace "ban san in da ake taron bane, ban ga Mubarak É—in ba"

Tasleem tace "bari in sakko mu shiga tare.

Farhan ta kalli mutumin da suke tare da Tasleem, har ga Allah Farhan ta ɗauka baban Tasleem ne, ta durƙusa tana gaishe shi.

Amsa mata yai yana murmushi, yana binta da kallo kamar maye, ya gyara parking ya kalli Tasleem yace "Wannan sweet sixteen É—in fa? Ya za'ayi?"

Tasleem tace "Ai fa, ido a mata, to wannan dai ba ta san wannan harkar ba, kuma ta na da taurin kai, a hankali nake son na hilato ta"

Yace "Subhanallah, Tasleem dan Allah ina son a riƙe mata wuta, ko nawa kike buƙata zan ba ki, wallahi tayi min ɗari bi sa ɗari gata 'yar Yarinya amma ƙirarta ta min wallahi"

Tasleem tace "kaga, sallameni zan tafi kuma ka dawo ka É—auke ni"

Yace "ko nawa kike so zan baki, amma ina buƙatar Yarinyar nan, ke daga Naira ɗaya zuwa millions, zan bayar in sameta, in ajiyeta mussaman in dinga hutawa"

Tasleem tace "ba ka da case, but for now, sallameni"

"Karki ji komai, zaki ga alert irin wanda ba'a taɓa miki ba"

Tace "kaji ka, kasan nawane a account ɗina kake cewa ba a taɓai min irin alert ɗin ba? Kawai dai ina jira" daga haka ta fito daga motar.

Farhan tai mamakin shigar da ke jikin Tasleem, wando ne jeans ya matse ta sosai kamar tai juyi ya tsage, ga wata matatsiyar riga a jikinta, attachment ɗin ta har ɗuwawu, kuma kanta ba ko ɗan kwali se uban glass baƙi ƙirin a Fuskarta.

Tace "Farhan muje ko" ba musu Farhan ta bi Tasleem, Kamar raƙumi da akala, se kallon Tasleem take sake yi.

Wani ƙaramin hall ne a wani ɓangare na Hotel ɗin, kallo ɗaya za kaiwa wanda suke gurin, kasan ba Mutanen kirki bane, gaba ɗaya Farhan ta sha jinin jikinta, take ta tuna lokacin da a kai na ta birthday ɗin, abunda ya gudana a gurin tsakanin ta da Sadik.

Take ta ji hawaye ya ƙwace mata, Babba ne ya hango su ya ƙaraso in da suke ya kalli Tasleem yace "ya kuma take kuka?"

Tasleem tace "Nima ban sani ba"

Yace "Common beb, whats wrong?" Yai Maganar yana ƙoƙarin janyota jikinsa.

HaÉ—e rai tai ta matsa tace "don't try it, ka bani zan tafi"

Yai murmushi yace "shikenan, zan baki, bari Nas ya ƙaraso suna hannunsa"

Suka bawa Farhan guri ta zauna, sam ta dena fargabar za'ai mata faɗa a gida, babban burinta be wuce ta ga maganin nan ya zo hannunta ba, dan tai imanin idan ba shi ta sha ba, shikenan sun ƙulla da damuwa kenan.

Tana nan zaune Tasleem ta kawo mata ruwa tace "Farhan ga ruwa, kan su kawo miki"

"Ni ba na sha, so nake a bani in tafi, kar a neme ni a gida"

Tasleem tace "ba komai, karki damu, yanzu za su kawo dan Allah ki sha ruwa mana"

Ba tai tunanin komai ba, ta karɓi ruwan nan ta sha sosai, ta ajiye sauran.

Ko mintuna goma ba'ai ba, Farhan ta ɓingire a gurin ta na bacci.

Sadik ji yake kamar an kunna wuta a cikin zuciyarsa, ya miƙe ya kai ya kawo a ɗakinsa, ya kaiwa iska naushi yana wani irin huci, ba tare da ya san meya haddasa masa hakan ba.
Ya zauna a gefen gado, ya dafe kansa yana jujjuya kai, yana son gano matsalar sa amma ya kasa.
Kawai ya fashe da kuka, hawaye wani na bin wani.
Nana ce tai sallama É—akin na sa ta na faÉ—in "Aboki, dan Allah ka koyamin wannan Assignment É—in, koyamin za kai, ba yi min za kai ba, sabo.......

Se kuma tai turus, ganin Sadik na kuka, a kiɗime ta ƙarasa in da yake, ta jefar da littafin hannunta ta zaune, tana janye hannunsa daga dafe kan da yai "Sadik meye ya faru? Me a kai maka?" Ta jero masa tambayoyin.
Maimakon ya amsa mata se ma cigaba da kukan da yai.

Itama ta fashe da kuka tana faÉ—in "Dan Allah Sadik menene? Ka gayamin"

"I don't know, something is killing me inside, and i dont know what is it, ina cikin damuwa amma ban san menene ke damuna ba, zuciya ta kamar za tai bindiga"
Chapter 70 · 0% Book details