← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 115

Sashe 72

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana na tsakar ɗakinta tana karatun exams, ta jiyo muryar Sadik a falo yana ƙwala mata kira "Friendy where are you?"

Daga É—aki ta amsa masa "gani a nan, Lafiya Kuwa?"

Buɗe ƙofar ɗakin yai yace "Ashe kin dawo?"

"Na dawo tun É—azu, naga ka ware harka fita"

SADIK yace "Yeah, come and see something"

Tace "something like what?"

"Zo ki gani mana"

Ta ɗan lanƙwasa wuya tace "karatun exams fa nake"

Yace "dan Allah ta so ki gani"

Ta miƙe ta biyo bayan Sadik, ƙofar gida ya jata ya nuna mata sabon babur dal.

Ta kalleshi tace "Friend wannan kuma na waye?"

Yace "Namu ne? Har lasisin tuƙi na yi"

Tace "wai siya kayi?"

"Eh mana, be kyau bane?"

Ta naɗe hannayenta a ƙirjinta tace "yayi kyau sosai, amma ba ka ganin muna yiwa Abba ɓarnar kuɗi da yawa"

"Ke wai fina son Abban nan ki kai ne? Allowance ɗina ne, na ƙwallo da shi na siyo mana"

Tace "Au har biyanka suke?"

Yai murmushi yace "au ke da duk wannan facakar da muke da kuÉ—i kin zata duk kuÉ—in Abba ne? Ina samun kuÉ—i da ball É—in nan, ba dan karatu ba ma da babban club ne za su siyeni, business zan fara fa"

"A siyeka kuma, se kace Zamanin bayi?"

"Ke fa Matsala ta da ke kenan, wauta ke ba ki taɓa jin ance an sai ɗan ball ba?"

Nana tace "yo ina gida, a ƙuryar turakar Inna ta ina zan sani.
yanzu masha Allah, Congratulations to us, ubangiji Allah ya tsare mana, saura kuma ka dinga tafiya kana barina"

"ÆŠakko É—an kwalinki, ki zo muje É—ani"

Nana ta ɗan ɓata fuska tace "karatun exams fa?"

"Ke dalla, shikenan rayuwa bawa ba ze huta ba, ki dinga hutawa kan ki da bokon nan, maza jeki shirya mu ware kawai, yau ba zama munyi ƙafa"

Nana tai murmushi ta koma gida, ta É—akko mayafi, tai rolling akan abayarta, ta hau sabon babur É—in Sadik suka shiga zaga gari.

Sun sha yawo sosai, sun zaga gari Sosai, sannan Sadik ya maida Nana gida ya sake fita gararambarsa.

Se taran dare ya dawo, ya wuce É—akin Nana, ze sa ta girki, dan yawon da yai, yunwa yake ji sosai.

Yana shiga ya tarar tana banɗaki tana wanka, ya kalli yadda ta ɗame gadonta, ɗakin se ƙamshi yake, aikuwa dan ya tsokane ta yaje ya haye gadon, ya kwanta.

Ya kai mintuna goma a kwance akan gadon, yana game a wayarsa, Nana ta buÉ—e toilet daga ita se towel ta fito.

Se da ta razana ganin Sadik a kwance a kan gadonta tace "meya haka dan Allah zaka shigo min É—aki ba sallama?"

Ya É—an kalleta yace "yunwa nake ji wallahi, sonake ki É—an dafamin wani abun"

Ta riƙe ƙugu tace "taɓ, ni baiwarka ce? Ina shirin kwanciyar zan maka girki, ai yaseen ba zan ba" tana cikin yi masa tsiwa, ta ga ashe har da takalmi ya hau mata kan gado.

A fusace ta nufo kan gadon tace "dan Allah meye haka, na gyara gadon ka hau min kan gado da takalmi, wannan ai wulaƙanci ne, dan Allah ka saukar min daga kan gado"

Shareta yai ya ci-gaba da game ɗin sa, a fusace taje ta sa hannu ta cire takalaman da ke ƙafar Sadik, ta ajiye su a ƙasa tana cigaba da masifa.

Ganin ba shi da niyyar kulata ne, ya sa ta É—au kayan baccinta, ta shiga banÉ—aki ta saka, ta fito ta shafe jikinta da mai, ta shafa turaruka, ta É—ako turare ta É—au lallausan duvet daga wardrobe, ta feffesa masa turare, ta zo kan gadon ta É—au fululluka ma, ta shafa musu turare.
Sadik yana kallonta ta wutsiyar idonsa, a ransa yace 'wannan Yarinyar akwai ɓarna'

Sedai ƙamshin da ya gauraye ɗakin, ya saukar masa da kasala, se wani lumshe ido yake yana shaƙar ƙamshin turarukan da suka gauraye ɗakin.

Kan sa ta zo ta tsaya, hannunta rungume da bargonta, ta kalli Sadik tace "Ni ka tashi, zan kwanta"

"Ai ban hanaki ba" yai maganar ba tare da ya kalleta ba.

"To ka saukar min daga kan gado, kasan dai na zan kwanta tare da kai akan gado ba"

"Ashe kuwa zaki kwana a ƙasa, dan ba zan tashi ba"

Haushi ne ya kama Nana, ta san Sadik da taurin kai, ta ɗakko pillow, za ta kwanta a ƙasa ta tsaya tace "kaiii, ni da ɗakina kuma gadona in kwana a ƙasa, rannan da nake jin tsoro naje ɗakinka ai a ƙasa na kwana, yau kuma se ka kwana a gadona ni kuma ina ƙasa, to wallahi ba ze yuwu ba" ta ƙarasa maganar tana hayewa kan gadon.

Fulo ta sa a tsakanin su, ta nemi guri ta kwanta.

Take Sadik ya ji shi a wata duniya ta daban, kasancewar Nana a kusa da shi, tana wannan ƙamshi me daɗi.

Lumshe ido tai tana Addu'oin ta na kwanciya bacci.

ÆŠiff taga Sadik ya kashe lantarkin É—akin.

Tace "A'a ya naga haka, ya zaka kashe fitila, ga ka É—are É—are akan gado, wannan ai ba É—abi'ar arziki bace"
Ji yai kamar ya kwashe da dariya, yace "ni ba na iya bacci fitila a kunne.

"Gaskiya idan muka kwana gado É—aya baka kyauta min ba wallahi, gaskiya ka shiga hakkina"

Shareta yai, yana cigaba da tattaɓa wayarsa.

Har bacci na ƙoƙarin kwashe Nana, ta ji Sadik a jikinta, muryarsa ƙasa ƙasa yace "Husna, haka zaki barni in kwana, yunwa nake ji wallahi"

"Ni na aike ka yawo? Wai ma wa ya gaya maka sunana na gaskiya? Ba wanda ya san sunan nan se wanda suka raÉ—amin"

Kamar ze mata kuka ya zagayeta da hannayensa yana sa hancimsa a wuyanta yace "So kike Ulcer ta kamani ko? Husna" ya kuma faÉ—a a hankali.

"A gaskiya bana son irin wannan abun da kake min, ni wallahi jikina wani iri nake ji in ka taɓa ni, gaskiya ka dena, kaga ni cikani in koma falo, naji zan bar maka ɗakin"

Cikata yai yace "Sorry, na ƙyaleki ba se kin fita falo ba, yanzu zan tafi, have a nice dreams"

Murguɗa baki tai kamar yana kallonta a ranta tace "Mutum shi dai in be naniƙi mace ba ba yajin daɗi, shiyasa rayuwa cikin turawa be ba, mutum yai ta kwafar banzayen ɗabi'u'

Ta koma can ƙarshen gado, ta takure, a haka har bacci ya kuma kwasheta.

Sadik kam ya rasa meye ma abun yi, yayi dana sanin zuwa É—akin Nana, ya rintse idanunsa, yana ajiyar zuciya.

So yake ya tashi ya bar É—akin, amma ya kasa motsawa, yana nan a kwance, dare ya cigaba da tsalawa ba tare da ya samo mafita ba.

Nana akwai make-make in ta na bacci, yo ta saba da kwana ita kaɗai, ta buga masa hannu a ƙirji, in aka jima ta maka masa ƙafa, ƙarshe gaba ɗaya ta dawo kansa tana baccinta.

A gigice Nana ta farka daga baccin da take, jin wani baƙon al'amari da ba ta taɓa zata ba.
Sedai Sadik ba wani tausayi ko makamancin haka, yai abunda zuciyar sa ke raya masa, se dai bayan ya nutsu ya dinga jin kamar ya aikata ba daidai ba, tamkar ya aikata wani gagarumin laifi, duk da yasan Nana matarsa ce, amma ya kasa gane dalilin da yasa yake jin hakan
Se dai ya bar abun a Nana tai ƙanƙanta da abunda yai mata, shi kansa be san yadda akai al'amuran suka kasance ba, jinsa yake kamar ba shi ba, kamar wani sabon mutum daban haka yake jin kansa.

Nana kam baki ya mutu ƙus, se kuka da take ko Magana ta kasa, se Allah ya isa da take masa a zuciyar ta.

A hankali ya janyo Nana jikinsa yace "Am sorry Husna Please..... Ai be ƙarasa ba, ta ƙwace daga jikinsa tana kuka, sedai ta kasa Magana sam.

Ya lumshe ido, yana son rarrabe wane irin yanayi yake ciki a halin yanzu.

Ya ɗau dogon lokaci a haka, Sannan ya miƙe ya shiga toilet ɗin dake ɗakin Nana.

Ya É—an jima Sannan ya fito daga toilet É—in, ya samu guri ya zauna a gefen gado, ya zubawa Nana ido, dan be san meya kamata yai mata ba.

Wayarsa ya É—akko, yana É—an daddanawa, daga ba ya koma banÉ—akin, sannan ya dawo a hankali yace "ki tashi ki shiga toilet ki gyara jikinki"

Banza tai masa ta sake shigewa cikin bargo.

Cikin tsawa yace "ba kiji me mace bane?" Ai a razane ta diro daga kan gadon, ta Sanya doguwar Rigar baccin ta, ta nufi banÉ—aki tana kuka me sauti.

Yace "kuma ba wankan soso da sabulu za ki ba"

"To wann zan yi?" Ta faÉ—a tana share hawaye.

"Ba'a koya miki wankan tsarki a Islamiyya ba, shi za kiyi"

Wani kukan kura ne ya ƙara ƙwacewa Nana, Sadik ya gama raina mata hankali.

Ƙasan zuciyarsa kuwa, wani irin tausayin Nana ne ya mamaye shi, amma ya san halinta, yana lallaɓata zata lanƙwashe tai ta Iskanci.

Bayan tai wankan ta fito, ta ga Sadik ya kuma kwanciya akan gadon nata, har da lulluɓa da bargo.

Ta canza kayan baccin ta, ta ɗau pillow ta koma ƙasa ta kwanta, tana ta sheshsheƙar kuka.

Sadik yana jinta, yai mata shiru. Se da yaji alamun tai bacci, sannan ya sakko daga kan gadon, kansa yana wata irin sarawa, ya ƙaraso in da Nana ke kwance, ya kwanta a kusa da ita, ya lulluɓe su da bargo, ya rungumeta tsam a jikinsa, yana faɗin "Am sorry Friend, na miki laifi but am so sorry" yai maganar yana sake ƙanƙameta, yana jin yadda jikinta yai zafi, se ajiyar zuciya take a bacci.

Ras!Ras!!Ras!!! Gaban Farhan yai wata irin mummunar faɗuwa, ƙirjinta ya buga da ƙarfi a jere, wanda se da numfashinta yai barazanar ɗaukewa.

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Miƙewa tsaye Farhan tai, taje gaban Window ta tsaya, ba tare da ta san dalilin hakan da tai ba.
Chapter 72 · 0% Book details