← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 115

Sashe 20

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To jikin nasa dai da sauƙi, but he is seriously sick, Abbanka yace jibi in Allah ya kaimu ze koma, kuma tare zaku tafi, kaje ka duba shi, dan wannan tsohuwar ta fara mita"

Sadik yace "nifa bana san zuwa garin nan, wannan tsohuwar ta sa mutum a gaba da masifa, tun da na masa Addu'a ba shikenan ba?"

Mother tace "Ni dai ba ruwana balle ace ni nake ziga ka"

Suna cikin maganar Abba ya shigo, tare da Faruk, Sadik ya kallesu yace "Abba sannu da zuwa"

"Yawwa sannu, wato kai muka shirya mukaje dubiya babu kai, wai ina ma ka shiga ne?"

Sadik ya É—an sosa kai yace "bacci nake, ban san ma zaku ba"

"Jibi in Allah ya kaimu zan koma, in gani in ba dama zan taho da shi nan cikin gari a duba shi, in ta kama a fita da shi ne a duba yadda za'ai, tare da kai zamu tafi kaima ka duba shi, dan haka ka shirya"

Abba na gama Maganar yai gaba, dan be jira me Sadik É—in ze ce ba.

Shi ba zuwa ƙauyen ne ma yafi damunsa ba, illa halin Inna na shegen sa ido da masifa.

Yauma haka ya kwana cike da tunanin Farhan, lallai da alama ita ma fushin take da shi, dan duk ta tosje duk wata hanya da zasu haÉ—u.

Farhan kam ta ajiye wayar da ya bata, ta kashe ta ta ɓoye, ta cewa direban Sadik ya dena zuwa ɗaukan ta, gashi tana tsoron Babba ya cigaba da bibiyar ta.
Dama an kusa fara exams, ba wani lesson ake musu ba, dan haka ta dena zuwa makarantar Gaba É—aya, tace se an fara exams ta koma.
Ga damuwa ta sa ko Abinci ba ta iya sakin jiki taci, kullum ta na É—aki, Umma kuma ba ta damu da taji meke damunta ba.

Yau gaba É—aya zaman Gidan ya isheta, dan haka ta yanke shawarar zuwa Makarantar dare yau, ko ta É—an samu releif.

Tana fitowa daga gida, ta kusa barin layinsu, sega Sunusi, duk da babu wuta amma yana ganinta ya ganeta.

"Hajiya Farhanatu, ance min baki da lafiya ya jikin?"

"Na ji sauƙi" ta bashi amsa tana ƙoƙarin raɓa shi ta wuce.

Sake tare ta yayi yace "haba to ki É—an tsaya mu gaisa mana, kwana biyu fa bamu haÉ—u ba, haba tauraruwar zuciyata"

Cikin rawar murya kamar tai kuka tace "dan Allah ka ƙyaleni Makaranta fa zan tafi"

Ze kuma yi mata magana, ta raɓa shi tai tafiyarta.
A duk lokacin da ta ga Sunusi ji take ta ƙara shiga matsananciyar damuwa, saboda shike barazanar rabata da farincikinta.

Jefa ƙafarta kawai take yi, taji tai karo da mutum a gabanta, ta ɗago ido ta kalleshi, duk da lungun ba wuta amma hakan be hanata gane shi ba.

Kewaye shi tai zata wuce ya kuma shan gaban ta.

"Ni zakiwa wulaƙanci, kina ganina zaki tafi, waye wancan ya tsaida ke yana miki Magana?" Yai maganar a matuƙar kausashe.

Haushi ne Yakamata, duk da a ƙasan zuciyarta taji daɗin ganinsa, cikin ƙwarin gwiwa da tsiwa tace "ban sani ba"

"Ni kike cewa baki sani ba?"

Shiru tai masa zata raɓa shi ta wuce, amma ya riƙeta gam yace "muje mota"

"Ba zani ba, ka cika ni"

"Ai ba abune ne wahala ba in É—agaki in kai ki motar ba, sedai kome za'ace a ce ba ruwana"

Ta san halin Sadik sarai, ze aikata abunda ya faɗa, dan haka ta haƙura ta bishi tana kuka, zuwa in da ya saba parking.

Sun kwashi mintuna a motar, kuka kawai take kamar ranta ze fita, a hankali yace "kukan ya isa haka, ke kullum cikin kuka ko gajiya ba kya yi?"

Shiru tai masa, tai me isarta sannan tai shiru.

"Yanzu gayamin, ma tukuna kukan me kike?"

Ko kallonsa ba tai ba, ta É—auke kanta.

Sadik yace "Hmm, dole inyi fushi a duk lokacin da naci karo da abunda yake barazana ga soyayya ta, banji daɗin ɓoyemin batun Babba na bibiyar ki da ki kai ba, baki san hatsarin yaron nan ba"

"To shine zaka dena É—aga wayata, ka dena kulani, shikenan tunda ka dena sona"

Sadik yai murmushi yace "Taɓ, bana tunanin akwai wannan ranar, da zan dena sonki Farhan, yanzun dai ga Abinci na taho miki da shi naji kince ko Abinci ba kya iya ci"

"Ni ba zanci ba" tai maganar tare da murguÉ—a baki.

Yai murmushi yace "lallai nayi sake wannan bafullatanar ta raina ni, har nake Magana kina mayarmin, shikenan let me feed you"

Ya takura mata harta haƙura ya dinga bata Abincin a baki da kansa.

Aikuwa ta sake taci sosai, suka fara hira, yake gayamata washegari zeje ƙauye duba kakansa.

"Amma ba zaka daÉ—e ba ko?"

"Taɓ, ya za'ai naje wannan ƙauyen na zauna, a goben insha Allah zan dawo"

"To shikenan, Allah ya bashi lafiya, amma dan Allah meya haÉ—aka da wannan Mubarak É—in da yake nema ya shafe ni?"

Sadik ya É—anyi Jimm sannan yace "abun babba ne, amma karki damu idan na dawo zan baki labari"

Tace "shikenan" ta kashingiÉ—a a jikin seat É—in motar kamar yadda yayi.

Ta ƙura masa ido, tana jin wata irin soyayyarsa na ratsa jikinta, ba ta san wani hali za ta shiga ba idan ta Auri wani ba Sadik ba.

A hankali ya juyo da fuskar sa ya kalleta yace "Ya dai?"

"Gabana ne yake faÉ—uwa ban san dalili ba" tai maganar wasu hawayen na bin fuskarta.

"Please calm down, muna tare Princess, mucigaba da Addu'a duk yadda za'ai, idan naje ƙauye ina ga zan gayawa Kakana buƙatata ina ga su su fahimce ni"

A hankali ta furta "Allah yasa"

Fuskar sa ya matso daidai ta ta yace "wane irin so kike min Farhan?"

"I don't know" ta faÉ—a tana lumshe ido, lokacin da taji bakinsa a nata.

They really enjoys the moment, jinsu a wata duniyar ta daban, me cike da rikitattun al'amura.

(Yau Sadik watsewa yake ji🙄, ga bani da lafiya, dan haka zan fice in bar ɗakko rahoton ban son harkar watsewa 😂😂)

Sosai Sadik ɗin yake ƙoƙarin zarce tunani, duk da yadda jikinsa ke rawa idanunsa suka rufe.

Rirriƙe hannunsa Farhan tai tana kuka, tare da girgiza masa kai.

A hankali ya bar abunda yake, ya cikata ya jingina yana sauke numfashi.

Yau har ƙofar gida ya rakata, ya kalleta yace "sena dawo, kimin fatan nasara, Allah ya cika mana burinmu, sannan shi wannan me gangancin zuwa in da kike, ya kiyayi abunda yake nawa, in ba haka ba ze mamakin abunda zan masa, ko ya rabuda ke ta daɗin rai, ko kuma in masa amfani da yaren da ze fi ganewa"

Farhan bata iya cewa komai ba, se bin Sadik da kallo.

Ya juya ya fara tafiya dan barin layin.

"I love You, Please don't stay long, without hearing from you"

Ya waiwayo yai murmushi yace "I love You too"

Sunusi kuwa yana bakin layi, yaga wucewar Sadik da Farhan.

Ya jinjina kai yace "dama wani ne yake hure miki kunne yasa kike wulaƙanta ni? Zaku gane baku da wayo daga ke har shi, zan hau buzu akan ku, sena rufe zuciyarki ruf, shi kuma in kife tasa zuciyar, ze gane ba'a takara da ƙolo"

Kai tsaye ya nufi in da Sadik ke tafiya a cikin duhu!.

Sunusi yace "Aminu, jirani mana"

Sadik ya waiwayo yace "ba Aminu bane"

Sunusi yace "dan Allah Aminu meye haka? Daga ina kake haka?"

Sadik yace 'ba Aminu bane, Sadik ne"

Sunusi ya jinjina kai ya maimaita "Sadik"

INA ME BAKU HAƘURI NA JINA SHIRU DA KUKAYI, NAYI RASHIN LAFIYA NE, NAGODE SOSAI DA ADDU'AR DA KUKAMIN, I MANAGE TO TYPE FOR TWO PAGES FOR YOU, BUT I STILL NEED YOUR PRAYERS PLEASE 🙏🙏🙏)

Ayshercool
07063065680

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Jin Sunusi ya maimaita sunan Sadik yasa Sadik É—in binsa da kallo, duk da cikin duhu ne, Sadik be damu ba ya cigaba da tafiyar sa.

Har ya ƙule da lungun Sunusi yana tsaye yana kallonsa, seda ya ga Sadik ya bar layin sannan yai ajiyar zuciya ya jinjina kai yace "daga yau idan aka kuma cewa ka kalli in da take ba zaka ƙara ba, dani kake zancen sena muku farraƙu"

Sadik kam a matuƙar kasalance ya nufi in da motarsa take ya ɗauka ya tafi gida, da ƙyar ya kai kansa gida, saboda yadda yake jinsa a gajimare.

Farhan kuwa tana shiga gida ta tarar da Ummanta a tsaye a tsakar gida, seda gabanta ya faÉ—i.

"Daga ina kike?" Umma ta tambayeta tana kallonta.

"Umma daga Makaranta nake"

"Ƙarfe nawa yanzu? Ƙarfe goma da rabi fa, ku da ake tashi tun goma, duk ƙannen ki sun dawo amma banda ke, har Amir na kuma aikawa Makaranta ya dubamin amma yace ba kya nan"

Gaba ɗaya Farhan ta rikice, dan harga Allah bata san lokaci ya ƙure haka ba, uwa uba ma ko makarantar ba taje ba.

"Ina tambayarki amma kin min shiru" Umma tai maganar a kausashe.

"Umma nifa ba in da naje, mun biya duba babar su Naja ne, an mata aiki yaron ba rai, amma ba in da na tsaya.

Umma tabi Farhan ba dan ta yadda da abunda ta faɗa ba, sema mamakin yadda yanayin maganar Farhan ɗin ke nuna ƙarya kawai take zabgawa.

Umma ba ta kuma ce mata komai ba, ta wuce É—aki ta barta.

Farhan ta nufi É—akinta jikinta na rawa.

Sadik kam da ya koma gida se da yai wanka, sannan yai shirin kwanciya, sedai abunda ya gudana tsakanin sa da Farhan ya sa shi a wani mawuyacin hali, me wuyar fassara.

Tashi yai daga kwanciyar da yai, ya fara zagaya ɗakinsa yana tunanin nemawa kansa mafita, tabbas yana ƙaunar Farhan, kuma a yadda yake jin kansa baze iya zama tsawon shekaru bakwai yana wata boko ba tare da yayi Aure ba.

Wata irin iska ya dinga fesarwa daga bakinsa, ya shiga safa da marwa a bedroom É—in sa.
Chapter 20 · 0% Book details