← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 115

Sashe 104

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Burinki ya cika, a karo na barkatai kin kuma maida ni mutumin banza, shine kika zagaya ki ka samu ɗan uwa kika ce masa wannan yaron kike so, kwana biyar ashe iyayensa sun kai kuɗi, ina nan na saki baki likitan nan iyayensa su kai kuɗi, ashe ni kika mayar mutumin banza, Yaron da yai silar ɓata rayuwar ki, nai miki iyaka da shi amma kika zaɓe shi a kaina, to kije gaki gashi nan, tunda kin fifita shi a kaina kije ki ƙarata, ba dai ke kwaɗayi ba zai Auri yaro ƙarami kamar wannan kije, gaki nan gashi ina ga yaron nan shine ajalinki" ƙura masa ido Farhan tai, ba tare da ta iya firta wani abu ba, saboda tsananin mamaki ta ma rasa wane irin tunani za tai, waye ya kai Sadik gurin Malam Zakari? Ya akai ba wanda ya gayamata an kai kuɗin? Kuma shi kansa Sadik ɗin ba ta sake ganinsa ba? Tambayoyi barkatai suka cika mata kai, ta ina zata fara yiwa Abba bayanin bata san maganar da yake ba se yanzu? Lokacin da take yawonta ma be mata Wannan alkaba'in ba se yanzu akan Sadik, aiko me za'ai ba ita ba Auren Sadik musamman da Abba yai mata wannan maganganun, kuma ba zata zama me cin Amana ba, idan akai haka ba'aiwa Abbas adalci ba"

Tun da Nana ta samu labarin kai kuɗin nan, ta ƙara takure kanta, ta shiga wata damuwar saboda ba abunda take hangowa se bankwana da ɗan ragowar farinciki da ya rage mata.

Abba ya tura Sadik ya duba gidan da yake so, a gidajen Abban, wanda Hakimi kan ya rasu, seda ya bada kuÉ—in da za'a saiwa Sadik gida a matsayin gudunmawarsa.

Sadik ya dawo daga sallar isha'i, ya shiga suyi magana da Abba, ya tarar da Usman, da Abba a zaune da alama Magana suke me mahimmanci.

Abba yace "madalla dama kai muke jira"

Sadik ya ƙarasa ya zauna yana jiran yaji jiran me ake masa?

Abba ya miƙa masa wata takarda yace "duba Wannan"

Sadik ya karɓa ya buɗe ya fara karantar, sedai tun ba aje ko ina ba, jikinsa ya hau rawa, gumi ya wanke masa goshi ya shiga tashin hankali.

Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680

AFUWAN BA EDITING.

Bakomai ne a cikin takardar ba face, bayani ne akayi shi dogo akan Farhan, na miyagun halayenta na shaye shaye, da bin maza da takeyi, da gantalin kwana a hotel.
Sadik yayi mamakin wani ƙasaitaccen munafukin ne ya zauna ya shirya wannan kitumurmurar.

Abba yace "ina fatan ka karanta abunda ke ciki?".

Sadik ya jinjina kai jiki a sanyaye, yace "Abba sharri....

"Dakata Sadik, kan in kiraka in nuna maka takardar nan, yau kwananta uku a gidan nan, na saka Usman yaje ya bincika min gaskiyar maganar ne, amma maganganun da ke fitowa, akan yarinyar suna cin karo da juna.

Wasu na sheda mutuniyar kirki ce, wasu na sheda akasin haka, amma batu mafi rinjaye, banji daÉ—in bayanan da aka samo min akan yarinyar ba, kai ka san a haka take amma kaje zaka jajubo ta ka sakamana ita a cikin zuriyar mu? To da sake ba zan lamunci hakan ba, kaje zan cigaba da bincike hukunci kuma zaga abunda ya dace".

"Abba, dan Allah idan ka tashi yanke hukuncin, ka yanke wanda zan iya É—auka dan Allah kar ka yanke wanda ze rabani da Farhan"

Usman yace "wai anya Sadik ba ka fara shaye shaye ba kuwa? Ko ba da hausa aka rubuta takardar da ka karanta ba"

Sadik yace "Na sani, na karanta amma dan Allah ku fahimce ni, ni dai dan Allah karku rabani da Farhan"

Usman yace "Anya Abba ba asiri a kaiwa Yaron nan ba?"

Abba yace "ba wani Asiri da akai masa, shashanci ne kawai, tashi ka bawa mutane guri"

Sadik a ransa yace 'Abba ba zaku gane dalilin da ya sa na dage ba, duk da kun nuna ba kwa so' haka nan jiki a sanyaye ya bar sashin, yana tunanin waye da wannan kuturun baƙin munafunci da ya kawo Wannan takardar?.

Jiki ba daÉ—i ya isa nasu part É—in, Nana tana nan zaune tana aikin nata na tunani, duk ta rame tai wani iri, Sahal na bacci ita kuma ta zubawa guri É—aya ido, da alama tai zurfin gaske a tunanin.
A hankali Sadik ya É—anyi gyaran murya, ta É—ago ta kalleshi, amma ta kasa dena kallonsa kuma ta gaza furta komai.
Ya kalli in da aka kawo kwanukan Abinci da alama ba taci ba, ya ƙarasa ya buɗe babban food flask ɗin, tuwon shinkafa ne da miyar taushe ta sha nama, ya zubo kaɗan ya zo gaban Nana ya zauna ya ajiye mata, yana tausayinta sosai ba ya son ya shiga hakkinta da yawa, gaba ɗaya ta dena walwala ta takure kanta fiye da kima, ba'a ta ɓa yiwa Nana rasuwa ba, dan haka dole wannan ta shigeta sosai.

"Bismillah, ci Abinci" ya faÉ—a cikin bada umarni.

"Na ƙoshi" ta bashi amsa.

"Kika ƙoshi da kika ci me?"

"Na sha shayi" ta bashi amsa.

"Abinci zaki ci, Nana meyasa kike son sekin illata kanki ne? Kin saka damuwa a ranki, ga yaron nam shi ba saurarar miki yake ba idan ya na jin yunwa, haba ki zama me karɓar ƙaddara mana, kiyi haƙuri ki ci-gaba da yiwa Hakimi addu'a, in kuma kema so kike ki rasa ranki kuma se inji"

"Saboda iyayenka suna raye, uwa da uba, kuma yanzu Magana ake ta zaka Auri wadda kake so, ni ban san uwar ba ban san uban ba, babban bango a rayuwata ya faɗi, ban taɓa ɗanɗanan ɗacin rashi ba se a wannan karon. Nima fa ba jin daɗin yanayin da nake ciki na nake, nayi iya ƙoƙarina amma na kasa daurewa, komai ya fita daga raina, dan Allah ka ƙyaleni idan da rabon in koma yadda nake shikenan, in kuma nima a zan mutu shikenan Ka bawa Mother Sahal, ko Su Anty Jidda"

"Meyasa zan ƙyaleki? Yadda kike cewa farincikin Sahal da naki ya na tattarr da farincikina, haka nima farimcikina da na Sahal suna tattare da naki ne, insha Allah da kanmu zamu raini Sahal muyi tarbiyyar sa, ki dena irin wannan tunanin, komai ze wuce Insha Allah, kan ki rasa Hakimi mahaifinki suka rasa, kuma suka cigaba da rayuwa, har kika girma, kowa yana jin haka idan yai rashin wani abu da yake so, dan Allah ki kwantar da hankalinki ki dena koke koken nan".

"He is very kind and generous, wannan halin nasa na tausayi da kulawa ne yasa na fara son shi, ashe shi da wadda yake so, kar ya cigaba da yaudarata da wannan halin nasa, yasa in cigaba da son sa, amma hanklinsa ya koma kan wata gaba É—aya" a zuciyarta tai ta wannan tunanin, a zahiri kuma take kallonsa yadda yake ta rarashinta cikin kulawa da tausayawa.

"Doctor magana nake amma kai banza dani, meyasa zaka min haka? Akan me meyasa? Ka dena ɗaga wayata ka dena zuwa gidanmu, kuma kana jina ina ta magana kai banza da ni" Farhan tai Maganar cikin ɓacin rai.
Abbas ya tashi yaje ya kulle ƙofar Office ɗinsa, Sannan ya jingina da ƙofar ya kalli Farhan yace 'gayamin, me kike so ayi, ko kuma meye baki gane ba?"

"Au kana nufin duk wannan ɓaɓatun da nake yi ba ka ma san me nake cewa ba? Ina can ina jiran ka ka kai kuɗin Aurena, kawai se inji Sadik ya kaimin kuɗin Aure how? Meyasa haka zata faru? Meyasa za kai min haka?"

"Au haba, dagaske Sadik ne ya kai kuÉ—in Auren, Masha Allah, Allah ya Sanya alkhairi yasa ayi damu"

Kawai Farhan ta fashe da kuka, kuka sosai har da sheshsheƙa.

Ɗan murmushin ƙarfin hali yai yace "Am sorry, ba ina nufin in saki kuka bane my dear, Farhan ni babba ne bana son in zama babban banza, ina tausaya muku da ke da Yaron ne, shiyasa na sadaukar masa da ke, a dalilinsa kika faɗa wannan mummunan halin, kuma a hakan ya dawo yace yaji ya gani, dagske yake sonki, mahaifin Huzaifa ne ya nemeni, kuma naje muka tattauna a matsayina na likita, dan shawo kan matsalar ki, muka tsaya a wannan matsaya, ina tayaki murna tare da yi miki fatan Alkhairi"

Cikin kuka tace "dama na sona kake ba? Na ɓata lokacina gurin sonka da tunanin Allah ya musanya min Sadik da kai, ashe kaima yaudarata za kai, yanzu duk azabar da naci saboda Sadik ruhina be cancanci ya huta ba zan koma gareshi, me soyayya RUƊIN ƘURUCIYA ta amfana min? Nagode da wannan sakamako da kai min, na soyayyarka da tunanin zaka tsamo ni daga tsaka me wuyar da nake ciki, Nagode da abinda kai min, kuma ka sani zanje in warware wannan maganar dan ba zan taɓa Auren Sadik ba, gara in cigaba da yawo".

Abbas yace "Subhanallah, haba Farhan ki fuskanci dalilina manax

"Ba wani dalilinka da zan fuskanta, duk mazs kun taru kun maida ni karkatacciyar bishiyarku me daɗin hawa, tamkar wata ƙwallo wannan ya jefawa wannan, in kuka haukatani kun huta ai" ta ƙarasa maganar tare da murza key ɗin ƙofar tai waje.

Abbas ya dafe kai, tare da neman guri ya zauna, ya zaci Farhan za tai murna da wannan abu da yayi, be taɓa tunanin za tai bore ba, shi kansa ba ƙaramin jihadi yai ba gurin haƙura da Aurenta, sedai ko ne haƙura da Auren nata ba, dangin mahaifinsa sunce ba shi ba Auren Farhan, saboda mugun fentin da suka ci karo da shi wajen bincike akan Farhan ɗin.

"Malam, dan Allah ka bi koma a hankali, kar a kuma haihuwa a ragaya a game da yarinyar nan, kaje ka samu Malam Zakarin ku tattauna, kaji ya akai ya karɓi kuɗin wancan yaron maimakon kuɗin gurin likitan".

Abba yace "ba in da zani, ba zasu maida ni mutumin banza ba daga shi har ita, suje suyi yadda suke so, na gaji da halin yarinyar nan da maganar da take janyo mana".

Umma tace "dan Allah kayi haƙuri, in dai wannan ɗin shi tak so, zata zauna da shi ze Aureta a haka ai shikenan, ni babban fatana shine tai Auren nan mu huta gaba ɗaya".
Chapter 104 · 0% Book details