← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 115

Sashe 31

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taslim tace "ni zan gaya maka 'yar talakawa ce, wallahi se an sa gidansu uku zuwa huÉ—u a gidan mu, ai ni naje na taho da ita ranar birthday É—in ta"

Nas yace "dama ai batun wani aure tsakanin sa da Yarinyar nan ba abune me yuwuwa ba, shiyasa ake bashi shawara kawai ya huta da ita a wuce gurin, amma ya tsaya yana shirme wai shi Aurenta zeyi kamar ba namiji ba, kalli da yadda aka sa yai kissing É—in ta, daga baya kuma wai yazo abun ya dame shi, wasu lokutan yai ta abu kamar ba wayayye ba"

Amin yace "ba haka bane, daga Yarinyar ne, da ya samu tantiriya, da zata gogar da shi sosai, da irin su Taslim ya samu, amma ita she's so innocent, shi yasa na koma jin tausayin ta dan da farko haushi take bani, amma daga baya naga idan Sadik ya lalata rayuwarta abun ze mata yawa, ga Talauci ga kuma lalacewa"

Nas yace "kai tafi can, ka bibiya ba abunda ba ta sani ba, yaran nan na yanzu, kai yanzu in aka cewa iyayen mu muna zagawa square mu huta, zasu yadda ne? Kai dai kawai ai sha'ni duk rufa rufa ce abun"

Taslim tace "kuma wallahi Yarinyar nan da zata shigo layi, zata É—au haske zata gara manyan mutane, dan tana da kyau ga uban diri kamar babbar mace"

Meena tace "ai abunda yake sake ruÉ—ar Sadik kenan, wannan dirin nata"

Nan suka cigba da gulmace gulmacen su.

Seda aka idar da sallar azahar, sannan aka tashi daga fadar nan, Sadik yaga shirme a gurin 'yan ƙauye kala kala.

Yadda suke kawo ƙara, wasu akan filaye wasu dabbobi, ba wanda yafi bashi takaici irin cases ɗin Aure.

Wata mijinta na satar mata awaki ya siyar, wata yana cin mutuncin ta, hadda me kawo ƙara akan tana ciyar da dabbobin mijinta dusa yace ze biyata amma baya bayarwa.
Shari'a kala kala, wasu abun haushi da takaici haka Sadik ya dinga jin su.

Ƙarewa gidan kallo Sadik yake, yana tunanin ta ina ze fara haurawa ya gudu daga gidan? Sedai katangar gidan doguwa ce sosai.

Sadik yana sha'awar kallon dawakan da suke burga, dan haka ya tsaya a gurin yana kallon yadda suke cin abinci suna huci.

Kamar an mintsine shi, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko ƙaramar wayarsa ya kira layin Farhan, by luck yaji ta fara ringing.

Murmushi yai ya gyara tsaiwar sa, yana jiran ta É—aga.

Sedai bata samu ta ɗaga ɗin ba, a ƙalla ya kirata kusan sau uku amma bata ɗaga ba, haka ya haƙura ya koma neman layin Mother, sedai shi kuma yaƙi shiga.

Gajeren tsaki yai, ya waiga bayansa yaga wannan dogaran tsaye da bulalai kamar masu gadin bawa, haka ya juya ya shiga cikin gidan yana kumbura baki.

Yana shiga ya cire wannan uban kayan da aka sa shi ya saka, ya zauna daga shi se vest da dogon wando.

Ya zauna akan katifar nan yai shiru, gaba ɗaya jin sa hake kama a prison, ba wani abun ɗebe kewa, ba abokai ba kallo, ba yawo, ga wayarsa Babbar caji ya kusa ƙarewa, ga kewar Mother da yake yi, gaba ɗaya abun duniya ya dame shi.

Farhan se da taje gida, Sannan taga missed call É—in Sadik, gashi ta riga ta dawo gida, dama wayar kullum a silent take, shiyasa ba ta ji ringing ba.

A gaggauce take komai, dan ta samu ta fita Islamiyya da wuri, ta kira Sadik, dan ba halin ta kira shi yanzu a gida, za'a iya jinta.

Sadik ya zauna ba daÉ—ewa yana jiran ya samu yai bacci, aka zo aka kirashi seda yai tsaki sannan ya fito.

A turakar Hakimi aka sashi a gaba, da bulala aka kuma narka masa irin tuwon da yaci da safe.

Sadik yana ci yana goge gumi, haka ya dinga cin tuwon nan, ji yake dama ya mutu ya huta da wannan jarabar.

Seda yaci sannan ya koma É—aki ya kwanta, zuciyarsa a cunkushe.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya tashi zaune da sauri ya duba yaga Farhan ce.

Cikin hanzari ya katse kiran, ya kirata sedai ba ya jinta sosai, a haka yace "Baby ina kika je ne na kira baki É—aga ba?"

"Ina school ne, ka san wayar tana silent tun jiya nake trying lambarka taƙi shiga, se da na dawo gida naga missed call ɗinka, na bari seda na fito Islamiyya sannan na kira ka"

Cikin damuwa Sadik yace "Baby ina cikin damuwa da tashin hankali wallahi"

"Subhanallah, meyafaru ne?"

"Kin ganni haryanzu ina ƙauye, ba kiji ba kya jina sosai ba?"

"Eh naji abun ya bani mamaki"

"Daga zuwa dubiyar nan aka hanani komawa gida, an barni a nan ina ta shan wahala"

Cikin damuwa Farhan tace "meyasa to aka barka a ƙauyen?"

"Kakana ne yace se an barni, baki ga yadda na koma ba, ba zan iya zaman garin nan ba, ina nan ina tunanin yadda zan gudu"

Farhan tace "ya salam, ka dena batun guduwa karka ɗaga musu hankali, kayi haƙuri ka zauna zuwa lokacin da zasu bari ka tafi"

"Farhan ba zasu bari in koma gida ta daɗin rai ba, se gana min wahala suke, ba ruwa ba wuta, ba irin Abincin da nake so tuwo fa ake bani, ga ina missing ɗin Mother, ga kema ba kya kusa dani, cajin wayata ma ya kusa ƙarewa, tunda na zo banga an kawo wuta ba, ba wanda na kira ba wanda ya kirani wace irin rayuwa ce wannan kamat wani bawa dan Allah"

Tausayin Sadik ya mamayeta gaba ɗaya, cikin damuwa tace "ka kwantar da hankalin ka Dear, dan Allah kar kayi wani abun da ze ja maka ɓacin rai kayi haƙuri, kasan su iyaye ba'a jayayya da su"

"Kakan ni na ne fa ba iyaye na ba, shima Abba ya tafi ya barni a nan, ban zaci Mother zata bari in kwana a garin nan ba ma"

"Kakanni suma iyaye ne, kayi haƙuri zuwa lokacin da zasu bari ka dawo kaji my"

"Hmm ba Zaki gane halin da nake ciki ba, duk yadda zan misalta miki ba zaki gane ba"

"Zan gane mana, na sani zaman ƙauye babu daɗi amma kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka kaji my love"

"Lovely ya zanyi, but definitely se na bar garin nan ba zan iya zama ba, and am missing you sosai wallahi"

"Am missing You too sweetheart"

"Are you sure?" Yai maganar yana shafa sumar kansa.

"Au ƙarya nake kenan?" Tai maganar a shagwaɓe.

"Wane ni in ƙaryata Baby na, sonake in ƙara tabattar da abunda kike faɗa ne"

"Hmm to ai shikenan, bari in ƙarasa Islamiyya"

A ɗan shagwaɓe yace "ban gaji da jin muryarki ba Farhan"

"Nima haka, amma kasan komai a ɓoye nake yi"

"Hakane, kiyi fatan zamana a garin nan yai silar warwarewar matsalata"

"Insha Allah, zanyi mana Addu'a sosai, Allah yasa su barka ka dawo"

"Ameen, in ma basu barni ba zasu wayi gari suga na gudu, nace ya batun yaron nan ya kuma miki wani abu ne?"

"A'a tun ranar nan ba ƙara ganinsa ba"

"To shikenan, ki kula sosai duk abunda kika gani wanda baki yadda da shi ba ki sanar min, bana son ɓoyemin abubuwa da kike"

"Shikenan insha Allah, amma baka gayamin meya haÉ—aku da shi ba"

"Karki damu, idan na dawo zan baki labari, duk da ban taɓa gayawa wani ba, ni dai ki kulamin da kanki Farhan, kinji my wife".

"Karka damu, Farhan taka ce kai kaÉ—ai, as Sadik is for only me"

Murmushi yai yace "hakane, naji daÉ—in wayar nan in kin rage min damuwa sosai, sekin dawo Allah ya kiyaye hanya"

"Ameen ya Allah, have a nice day"

Ta katse kiran.

A hankali bacci yai awon gaba da shi, duk da ba wani jin daÉ—in baccin yake ba.

Nazir ya kasa zaune ya kasa tsaye, tuna sakamako ya nuna Lilly na É—auke da juna biyu, yanzu tsoron sa Allah tsoronsa Asirinsa ya tonu, ya san ya shiga uku idan Asirinsa ya tonu, dan kuwa ya kaÉ—e har ganyensa, gata 'yar gidan soja ga cin mutunci da zubewar mutunci da ze fuskanta.

Ganin zaman tunani ba ze fishshe shi ba, yasa ya tashi yai wanka ya shirya, ya fita neman mafita.

Abu kamar wasa, ko Abinci ya gagari Mother ci, saboda tunanin ɗan Autan ta, abun ya dameta ƙwarai amma Abba yaƙi bata fuskar da za tai masa ƙorafi.
Duk da shima dannewa yake kawai, dan ya san Sadik ba ze taɓa jin daɗin zaman ƙauyen nan ba, amma ba ya son ya nuna dan kar Mother ta samu damar yin ƙorafi.

Yauma Sunusi ya zo gurin Farhan taɗi, sedai ba ta sauya zani ba, taƙi kula shi balle ta tofa komai, shikaɗai yake ta zubarsa kamar an kunna tanki.

Can ya nisa yace "Farhanatu, dan Allah wai meyasa idan nazo ba kya son sakin jiki dani ne? Da har gaisheni kina yi amma banda yanzu na rasa me nai miki"

Haɗe rai tayi ta sake ɗauke kanta, daga barin kallon in da yake ma saboda baƙin ciki da take ji ba duk lokacin da ta kalleshi.

"Ki kalleni mana ki min magana ko naji daÉ—i"

"Aikuwa ka daÉ—e ba ka ji ba, ni dan Allah in baka da abun cewa ka bari in shiga gida bacci nake ji"

"Haba Farhan yanzu maganar da nake miki bata da mahimmanci a gurinki? Ina son mu tattauna akan yadda zata kasance da bikinmu"

Farhan ta É—an murguÉ—a baki tace "Allah ya kiyaye"

"Me kika ce?"

"Ni bance komai ba, dan Allah kaga seda safe"

"Saboda Sadik ne yasa kike min wulaƙanci?"

Waiwayowa tai da sauri ta kalle shi, amma ta basar tace "waye kuma Hakan?"

"Kin fi ni sanin waye hakan, sedai abunda nake son ki sani shine, ke tawa ce an riga an bani ke, ni iyayen ki suka sani dan haka ki fita sabgar wannan É—an Yaron"

"Kai ka san shi ni ban san shi ba"

Sunusi yace "kin fi ni saninsa, tunda yake kawoki a mota, wato ni talaka ne shine kika ɗaura ɗambar wulaƙanta ni, to na dena lallaɓa ki in kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba"
Chapter 31 · 0% Book details